Wednesday, April 18, 2007

MAIGANJI; Daga Malam Muhammadu Namaiganji

Ba dai wani takamaimiyar magana, akan kowanene Malam Muhammadu Na Maiganji, ba kuma tabbacin lokacin da ya rubutata. Amma insha Allah, zan kawo cikakken bayani a gameda wakar ta Maiganji. A yanzu dai ga wakar Maiganji

Bi Bismillah ni bawa, na far yabo ga mai baiwa
Arrahmani baiwarsa, gamamma ce ga dan kowa
Rahmani ya kebe baiwarsa, baya yiwa majusawa
Allahu yai dadin tsira, ga Ahmadu shugaban kowa
Baicin ambaton Allah, nufina gargadin kowa

2]Wanda ya yada addini, baya tambayar kowa
Girman kai ya debe shi, ya sashi ya fandare wawa
Yaku yan uwa dangi, Allah ya halicce mu
Domin tsaida addini, Tawhidi kaza Sallah
Musan Azumi da Zakkarmu, kaza Hajji wajibin kowa

3]Mu sansu, mu sanda yayanmu, kaza matanmu bayinmu
Kanko mun ki sanasshe su, ranar lahira ka sani
Acan aka tambayar kowa, akan doran siradinsa
Ga kaifi, ga makonansa, Kama nan za'a tsaishe ka
Idan yazo dasu ya shige, idan bai zo da kome ba
Wa'ila sai su turo shi, cikin zurfin wuta wawa

4]Bayi na ciki su cane, ya kaitonka kai bawa
Ina halinku ma'aikinku, ya kance 'sun isar da sani'
Iyaye sun ka bashe mu, suna aikin majusawa
Kan ance da su su bari, su kance 'mu iyayenmu
Mun same su sun aika, abinda su kanyi shi zamu bi, bama jin fadar kowa

5]Ka duba can ga kakanku, , Adamu, Nuhu, Idrisu
Da Ibrahim uban kowa, Manyan Annabawa ne
Sun bi fada ta Allahu, tazo har kan ma'aikinmu
Kowak ki ta ya ratse, yabi fadar Yahudawa

6]Yahudu, Nasara sun ratse, shaidani ya rude su
Yace ku tsaya a nushe ku, ga aikin iyayenkuAbin bautarsu su gunki, gama shine mashasharku
Kar ku bi annabin kowaYa jama'a ta addini, bin Allah farillansa
Bin manzo cikin sunna, wanda ya yada bin sunna
Kamar bai aika komai ba, kamar dai wanda yai sallah
Bai zakka ba ya tabe, cikin bin Jallah mai baiwa

7]Wanda ya bauta Allahu, yana sabon iyayensa
Bai karba ba sarkinmu, ka tuba ka bisu kai wawa
Ya mai bauta Allahu, nemi halas abar cinka
Kan ko tabe, haramun wanda ya cita
Misalin gwargwadon lauma
Kwana Arba'in za ai, yana bauta ga sarkinmu
Bai karba Allahu, Jallah ubangijin kowa

8]Ina Malam, Ina Malam Malam tsorci Allahu
Kabar tsoron mutanenka, fada musu gaskiya hakkan
Kan sun bita ka huta, kan sun ki ta ka kubuta
Wurin Sarkinmu Allahu, Jallah Karimu mai baiwa

9]Zan muku gargadi dangi
Ku kai yayanku gun malam
Karatu wajibin kowa

10]Wanda ya samu da nasa, Yaki ya kai shi gun malam
Ya dau alhakin dan sa, Yahudu, Nasara sun samu
Kaza suma majusawa, Kowanne da
Ka haifeshi, duk jama'ar Ma'aikine
Sai babansa yaki shi, yakan koma Nasarawa

11]Malam nemi sarkinka, kace masa yai fadan bidi'a
Bidi'a kishiyar Sunna, kowab bita y rates
Yabi fada ta shaidani, yaki fadar ma'aikinmu
Muhammadu Annabin kowa, wanda yabar fadar MammanYana nushe shi kan turba, Yana kimso cikin jeji, yana yawo kamar giwa

12]Mai yawo cikin jeji, kan yaje cikin jama'a
Mazaje masu bin Allah, suna taro gidan malam
Ko jam'a ta yin sallah, baka ga shi baya sheka yana cigiyar, bata wawa
Koda nace, da ko daji, ba daji na kura ba

13]Ko acikin gidnsa yake, yaki yaje gidan malam
Shi san Allah, bazai Sallah, kace masa
Mai shiga jeji, zaya bace cikin njeji, Babu gudunmawar kowa
Maza mata ku nemi, fada tasa shugaban kowa

14]Wanda ya bar fadar Mamman, yaki fada ta Allahu
Ta'ala wanda yai kowa, Wanda yabar fadar Allahu
Ya kafirta ya watse, yabi safun
Abu Jahalin, Abu Lahabin da wansunsu
Yana koyi da su wawa

15] Ya jama'ar musulminmu, mai kaunar yasan Rahma
Yabar aure cikin idda, Allah bai hallata ba
Ma'aiki bai halatta ba, Malam ya cane ka bari
Kana yi kaito kai wawa
Mutum uku munji sun rates, limamin da ya daura

16]Waliyin wanda ya aiko, da mai nema cikin idda
Sun ko sun ki bin turba, Ta annabi shugaban kowa
Su duka mun ji sun ratse, da wadda ta karkace idda
Har jama'ar da tai shaidar, asasu wuta
Cikin karfe, su kuna ba ruwan kowa

17]Inai muku gargadi dani, maso jinkai
Ya same shi, Yai auren halaliya
Ya dauki ruwa da gammonsa, ko ya saya
Da kurdinsa, Ruwan wankanta ko sallah
Hadisin shugaban kowa.

18]Wajibne ga da namiji, yai bauta ga matansa
Kadan yalwa ta same shi, kadda su durkusa
Dutse, Ni fan day a bare mai yawa
Fadar nan duk da nayita, nib a shisshigi
Nai ba, ka bi ta kabar batun kowa


19]Wanda ya kama matansa, da cinsu da shansu ya dauka
Yana yi gwargwadon iko
Tamkar wanda yai sadaka, har ma yafi mai sadaka
Wurin sarkinmu Allahu
Jalla karimu mai baiwa

20]Ka nemi halas ka cishe su, Allah zai biya kowa
Kadda ka nan haraminya, kowac cita ya kuna
Sai ya tuba ya barta, Rahimu ya maida jinkansa
Allah Rahimin kowa
Yaku masu bin bidi'a, da kun tuba kun barta

21]Kun bi fadar ma'aikinmu, bin farali da bin sunna
Kowa mai hana ku barin, Yalwa sai ta same ku
Dabbobi sa wadaceku, Kishirwa babu
Ko yunwa, bare yafi ya daukeka
Bare bautar Nasarawa

22]Ku shirya zasu bashe ku, kui damara ta bin
Mamman, ku tserewa Nasarawa
Ku bar waka ta shaidani, kui zikiri na bin Allah
Halshe an halitta shi, dan zikiri
Da yin kalma, ku bar zagin ubankowa

23]Ku bar zambon iyayenku, Gwarabjawa
Da Maiganji, ku tuba ku bar gamin kowa
Mai zagin iyayensa, mu mun sami labari
Can a wutar Yahudawa

24]Mu mun sami labariAcan a can a wutar Yahudawa
Macizai har kunaminta, suna dako su cije shi
Kan sun sami bakinsa
Sukan kama suna yago,
Su kan taye kamar yawa.

25]Kunaminta na harbi dubu saba'in,
Karin nasu gaba daya zsu soke shi
Su zarta jikin maki Allah, masabin dan Kuraishawa
Muhammadu wanda yaki ka, shi darajarsa ta tauy
Anan duniya gidan Darbashan, inda Dayyanu mai sakawa dan kowa

26]Ina makadi maki Allah, da shi da ubansa shaidani
Da mai murnar abinda su kai, Allah ya la'ance su
Ma'aiki ya la'ance su, Mala'iku na Allah suma
Sun la'ance su, mutane masu bin sunna
Suma sun la'ance su

27]Kifi maigida a ruwa, shima ya la'ance su
Tsuntsu maigida a sama, shima ya la'ance su
Duk bayio na Allahu, basu san su
Domin kinsu bin Allah
Ta'ala wanda yai kowa

28]Mai ganga maki Allah, kan ya dauki Gangarsa,
Ya kanje dandali nasa
Shaidani yakan tashi, yana gayya gidan kowa
Kowa amsa gayyarsa, can zai kaishi gun gayyu
Shiko Gayyu Zaza ne, cikin zurfin wuta wawa

29]Kowa tuba ya huta, Allah rahimin kowa
Ku tuba ku daina yin bidi'a, Allah ya jikan kowa
Ina makadi uban bidi'a, mai sababinka kin Allah
Yai maka hannu da kafa, ya baka idanu da kafa
Da baki duk da kunnenka, wa zai kirga baiwarsa da yai maka ja'iri wawa

30]Kaki ka gode baiwarsa, menene tsakaninku
Kana bijirar da bayinsa, kana ta kidi suna waka
Kana bauta ga shaidani, kun ki ku bauta Allahu
Ta'ala wanda yai kowa, ku bar bauta ga shaidani
Nufinsa yaje ya yashe ku, ya kai ku cikin wuta wawa

31]Ina makadi uban bidi'a, da kun tuba kun bit
Allah sai ya yafe ku, Rahimu Ubangijin kowa
Kan ance su bar Bidi'a, su kan ce tun iyayensu
Da kakanni ake yinta, shi sabonsa
Tun nan, basa jin fadar kowa


32]Ku duba tun iyayenku, da kakannin iyayenku
Sha sabon karatun nan, suka tarda shi wawa
Ina jin tausayin dangi, basa tausayin kansu
Sun ki su kama bin turbar
Muhammdu shugaban kowa

33]Fitar mata zuwa jeji
Suna nema da dan gyaftoSuna cin kasuwar lahadi...........

34]Yaya ne ka auro su, ba bayi ka auro ba
Kabar su suke fita yawo, tsorci
Ubangiji Allah, Ta'ala wanda yai kow
Ko bayi ka same su, kanka bukace su
Auransu kadda ka bar su su yawo, fada ta ubangijin kowa

35]Kuna cewa iyayenku, basu bada su da ka-
Kanninku, Addini na Ibrahim, yai tsari ga matansa
Sahhabai dukka sunyi tsari, dan kakanku yaki tsari
Ba sauki akai masa ba
Shi ne yaki bin turbar Annabin kowa

36]Fadar Allah Ta'ala ce, zaman mata cikin daki
Kun ki fada ta Allahu, kuke fusshesu gun narko
Bar kallon fadar Allah, ko sarkin kasa ya fadi
Kan ka ki ta ka tashi, gidanka
Da shi da gonarka, don ka barshi bayanka

37]Ka sheka kana yawo, cikin ZazzauKaza
Katsina, ko birnin Kazaurawa
Kamarka mutum kakewa gudu
Ka rasa zamna gidanka
In ka ki fadar Allah, ina magudarka kai wawa?

38]Mala'iku su kamo ka su saka
A sasarin karfe, a sundukin bakin karfe
Sai ka tuba ka barsu, kai hakuri
Da noman so, Allah sai ya yafe ka
Domin bin uban Kasim, jikin Hashimiyawa

39]Ina mai annamimanci, da mai hassada
Da mai ruwa, da mai zina ja'iri bawa
Da mai suka ga addini, da mai gaba
Da malumma, da mai karya cikin jama'a
Da mai zuku yana tazidu............

40]Mai zina ya shiga ya shiga uku, radda ka tada yan adam
Da aljannai da wansunsu, du da mala'ikun Allah
Ana kallonsa duk jama'a, yayi baki bakin zunubi
Kai kace bakin wawa
Da shi da abokiyar la'ana, gabanta kamar ruwan miki

41]Tana yoyo cikin jama'a, kamar randa data burme
Ga doyi kamar kuna
Kaman nan zai kusance ta
Yana lasa da bakinsa
Kamar lasar kare wawa

42]Jahannama can tana dako
Akai mata jairin bawa, maki sarkinmu Allahu
Maki jin gargadin kowa
Mai riya zamu zancansa, maki zancen
Ma'aikinmu, maki jin gargadin kowa

43]Manzo ya cane ya bari, Shirka ce wurin Allah
Shiko yaki mai shirka
Wanda ya bada kayansa, don a fada a cane
Wane, jikan wane, dan wane
Shaidani ya rude shi, don ya batar da shi Wawa

44]Shi bai nemi lada ba, wurin sarkinmu Allahu
Shi dai duniya ta fadi, suit a yabonsa yan
Adam, sun ace ba kamar wane, domin
Sunga wawa ne, shi bai san da karya ba
A’a ya sani it ace, yake bautar kwanikawa.

45]Ina wawa maki turba, fahimci abinda za
Ni fadi, Allah ya halitto ka, dan bautarsa
Ka ki sani, kana neman taro da kwabo
Kaki ka nan shinan Sallah, bar kallon taro da Kwabo
Ko kasan Sule da Dala, ko rumbu guda ka cika, sai wata ran mala’ika, ya dauke ran yabar gawa.

46]Su kai ka su sa cikin rami rami, su lullube
Yar kasa su rufe, su juya can wurin karfe
Suna ta raba sub a naka, Anini guda
Basa baka, Kwabo ma yafi karfinka
Kanan shinan Sallah sai itace, wurin bawa cikin kabarinsa kai wawa

47]Ku san neman taro da kwabo, halaline wurin Allah
Kan ka san shinan Sallah, kadan ko ba shinan
Sallah, haramunce gad an kowa
Allah yayi wo bawa, dan bautarsa kai wawa
Kai ko ka ki bautarsa, dan neman taro da kwabo, ka duba arzikin bawa
47]Rababbe ne wurin Allah, abinda ya bashi ya bashi
Da zai hau samaniya yana neman dadi
Babu yace ya gode mai baiwa
Godewa ga sarkinmu, bin sa da
Bin ma’aikinmu, da bin ulama’u kai wawa

48]Lura fadar da nai bawa, kan ka kita ka tabe
Ba azumi bare sallah, duk aikin addininka
Ba lada wurin Allah, sai ka tambayo malam
Allah yaki addinin
Da ba’a tambayar kowa

48]Azaba can tana dako, ga bawa wanda yaki sani
Kamanan wanda yayi sani, baya aiki da shi
Wawa ku bar wasa ku nemi sani
Said a sani ake samun gidan Rahma
Wurin Sarkinmu Allahu, Ta’alas wanda yai kowa

49]Ana wa’azin bakin bawa, dillalin bakin bawa
Wanda yaje cikin kurmi, yana yawo da ka-
Yansa, kan ace da shi ya cira, yakan ce
Yafi karfinka abinda akan tayi goma, yakan ce Sha Biyar ka taya,
Ba tsoro bare kunya, yaki fadar ma’aikinmu, bare maganar ubankowa.

50]Kiyayi riba haramunce, wanda ya cita zai kone
Ka tsoraci ubangiji Allkah, Tabaraka wanda yai kowa
Karya ma haramunce, kabar san yenta kai wawa
Mai karya cikin jama’a, shi kan keta bakinsa
Yakan je har zuwa keya, kadan karyarsa ta shahara

51]Allah ya la’ance shi, a sa la’ana a goshinsa
Kowag ganshi ya san shi
Duk dabbar gida da dawa, kan tag an shi ta san shi
Ta ce Alhamdu lilLahi ni nagode sarkinmu
Tunda yayi ni ni dabba, naïf makaryacin bawa, mugu fajiri wawa

52]Ina bawan dake hassada, ya tuba ya daina yin hassada
Kan ko yaki ya kone, yana haushin
Rabon Allah, zato nasa ja’iri wawa
Zani yabon ma’aikinmu, tsattsarka uban Kasim
Baban Fadima Zahra, mai hakuri uban dayyabu, Sidi Balaraben kowa

53]Mai haske da kyau Mamman, Mai saje da kyawun
Fuska, gashi da kyan bakin gashi, bashi da furfura
Da yawa, cikin sajensa har gemu
Kan ka san guda goma, kana neman biyar ka dada
Baka samu ba sai ka tsaya, kana kallon wushiryarsa

54]Ga haske yana tashi, turare ma yana tashi
Kamshi ya buche kowa
Ana ajabi da sawunsa, Kan ya taka kan dutse
Wurin takun yakan gurbi, kan ya taka
Rairansa, baka gurin ba yai gurbi, hukumcin Jalla mai baiwa

55]Dadai ka gani bawa, yadda ka tsaida yan adam
Wurin ikonsa Sarkinmu, ranar kaga jayayya
Iyayensu da yayansu, mazaje su da matansu
Sarki shi da fadawa, dogarrai da sauransu
Har da yace da babansa, kai ka batar dani Turba

56]Kana ji na ina ihu, nakan zallko ina juya
Kai ko ka ki yin tsawa
Kowa ya kira dansa, yana nusheshi
Bin turba, kai ko ka ki nushe ni
Bare nabi annabin kowa

57]Ina Magana ga dattijo, tunda ya bar fadar Mamman
Ya ki fada ta Allahu, jallah ubangijin kowa
Yara su da manyansu, kan suka dubi kankanci
Su kance Rabbu sarkinmu, mun bi ta
Shugabanninmu, su suka bi damu turba

58]Rabbu ka fara bashes u, sui nisa da jinkanka
Jallah ubangijin kowa
Wadanga da su da manyansu, jayayya takan
Rude, sukan ce mu musulmi ne
Bad an ku ba manyanmu, su suka ce da su a’a, …………

59]Sukan ce ba Kaman nan ba, ko kace mu bar turba
Mui bautar wanin Allah, ace fa su daina jayayya
Akai su wutar Nasarawa, fadar wa’azi da nai dangi
Don mai hankali na fadi, koda nace daku waka
Tunda ya sa dani acikin, musulmi masu san baiwa

60]Acikin mutane masu yin Sallah
Suna karbar fadar Mamman, Sidi balaraben kowa
Salatin Lahi Sarkinmu, ya tabbata
Ya tabbata nan ga manzonmu
Muhammdu mai dubun baiwa

61]Da aloli da as’habu, damu mabiya umarninsa
Ana ranar dab a bawa, mai debe kewa
Kan ance daku waka, wanene matsarinta
Ku ce masu kankanin bawa, malacin gayyi
Aikin karatu ya buwaye shi, na Qur’ani kaza ilimu, sai sururi abin wawa

62]Cikakken hankalin bawa, yai sauki da surutu
Sakankance da wautarsa,
kan ya yawaita surutu
cikin taro, wajen jama’a
Ku taru gidan zaka wawa.





Tuesday, April 17, 2007

TABARKOKO; Daga Sarkin Zazzau Aliyu Dansidi

Wannan dai itace wakar Tabarkoko, wadda sarkin Zazzau Aliyu Dansidi ya wallafa. Wakar dai gugar zana ce, ko kuma ince shagube da bai nuna wanda yake yiwa ba. Amma ana zaton ko yayi tane domin yiwa fadawansa shagube, game da yadda suke tafiyar da rayuwarsu.

Aboka zo nan mu bata
ka dubi dan dai ga wata
wada daban da batta
Haske na rana da wata
Ba zasu zam daidai ba

He dubi dai tsettsewa
Ya samu kifi a wuya
shina zaton babu kaya
Inta kafe mai ga wuya
ba zasu debe mai ba


He dubi dai irame
Can tai gida a rame
Can dauri kau ta rame
kyaushe mijin Irame
gallonsu ba zaki ba

Abin ga dai gama na
kare shi tono magana
zai iske kura a hana
ba dun akwai wata magana
da bai fito rannan ba

Ai ga fage ga doki
Noman fako ba taki
ai maganan ta sake
da dan kare da na doki
ba zasu zam daidai ba

Mu namu ga ta da taki
babu biri ba zaki
barde dubu mai doki
da zamanin kai taki
da bamu samu nai ba

Saura garin ya waye
duk kokuwan tai kaye
Damu ga yan tawaye
da masu da da maye
zamansu bai zam dai ba

Karya take zabira
bata zama gurara
Iska daban da sarara
matar maza da bera
kudinsu bai zam dai ba

Na ganshi duk ya kwabe
Yayi tabo ya tabe
yayi bago ya rabe
Neman jini ga babe
Ba za'a samu nai ba

Zo ka taba dai ka jiya
Yau muke koko jiya?
Haure ka ciwo ijiya
in yayi sai ayi jinya
ba za'a debewa ba

Ko ka iso, ko ka tsaya
Taunan aya ko ka iya?
Amale cimansa kaya
Jaki, da sa, ko akuya
Ba zasu taunawa ba

Kaya ga Rakumi shike
Takarkari sai taiki
Saimo akanwa taki
Tsaiko akanwa daki
bukka ba ta dauka ba.

Makaryata, mahassada
basu iya komi da guda
na yanzu ba ko da na da
tara su dai duk ka gwada
ba su zamo daidai ba

Babba da jaka ya zaka
Yana bidan kifi tsaka
gulbin da dorina tsaka
Gefen kadanni ya saka
kafansa ba zai kai ba

Yada guda ka dau guda
Duk ka fasa su ba guda
hanya mararraba guda
gaba-gaba akan guda
cikinsu bai ba daya ba

Ga kutu ga Tabarkoko
Ga dole-dole tai hako
ni naga tana ga fako
kai mai bago shiga sako
Wurin ba'a zo mai ba

Kwaddo ina kadangare
Naji kafarsa ta kare
ya bar diyanshi gangare
in yayi nan sai a tare
ni ban gano zai kai ba

Ko kaga mai digirgire
wuya awa gadar zare
Takuna zance hantsare
da zamanin bakin zare
da basu sa riga ba

Ga tsada mai dan tashi
kullum ta dau albashi
ba ta ci bata hana bashi
ran da safiya tai fashi
ba za'a koka mai ba

Ga wani tantalwashi
na biyunsu mai kan bashi
na ukkunsu bashi da nashi
Da dai ana tuna bashi
da basu sa riga ba

Nazundu mai zaka fada
kullum ka gana da rada
roko awa dan makada
a baka bashi a dada
ba zashi fasawa ba

Ga wani wai shi ya iya
yaje ya jawo igiya
ta nannade mai a wuya
yana kira da waiwaya
ba za'a debe mai ba

Shin me ya samu shamuwa
na ga tana ta dimuwa
naga ruwan da kainuwa
ba dun kasan da kaguwa
da bata sauka anan ba

Da kunkuru da bushiyta
halinsu dai noke wuya
ga zamani na waiwaya
da zamanin mazan jiya
ni naga da basu kai ba

Debi yawa, sam ma kadan
yanzu yawa ta zam kadan
a hankali kadan-kadan
Gidan yawa kan yi kadan
Abinga ba banza ba

Nai muku waka ta batu
ku zo ku nemi yan batu
awa su lugegen batu
tara fasihai na batu
ba zasu ganewa ba

Mai wagga waka ta batu
Ali Amiru wan Shatu
Shine abokin Warqatu
Dadai da sirri na batu
Da bashi boyewa ba

Allahu shi yai mu duka
Baki fari yai su duka
Shudi da Korensu duka
Da Ja da Rawaya duka
Shi dai kayi ba wani ba

Zama fa shi dai ya iya
Shi yo mutum shi tafiya
Wadansu ko shi yi su tsaya
Shi yai itace da kaya
Nufinsa ne ba wani ba

Shi yai dawa da karkara
Shi yai dawa da karkara
Shi yai kwai, yai zakara
Yai zabuwa, yai fakara
Shi ad damu ba wani ba

Bautanmu dai hasana'u
Zam haufu, duk dada rija'u
Ku lura ko asma'u
Nisa'u masu gina'u
Sha'aninsu ba karko ba

Asma'u an sanki da dai
Halinki ki ne ko can dadai
Shirinki kullum na kwadai
Maso biyu,bashi da dai
Batun ga ba karyaba

Ywaita rokon Jalla
Ka wakkale ga Allah
Ka zam kula da Salla
A baka ni'ima walla
Anan da can ba waiba

Muyi zikiri da salati
Mu karkare afati
Gobe mu san najjati
Ga shugaban hajati
Muhammadu bawani ba










Monday, April 16, 2007

Wasiyya Sipikiyya; Daga Mudi Spikin

Ta'ala ina rokonka ranar da zan cika
Kasa in cika Allah cikin daki na

Gaban duk iyali na da 'ya'ya da 'yan'uwa
Allah ina rokon ka sai a gidana

Idan na cika yan'uwa na gaya muku
Da kun ji cikawata ku taru gidana

Idan har da rana abin yazo ko cikin dare
Batun jinkiri kar dai ya faru wurina

Idan anyi sallah an gama kar a dakata
A dauka kawai hanyar zuwa kabarina

Idan anka je da zuwa a sani ciki kawai
Cikin hankali domin tuno lamarina

Kasar kabarin kuma kar a ware daban-daban
A turo gaba daya duk ta watsu a kaina

Idan aka kare gini da an tashi an gama
Ku koma wajen harkarku ya jama'ata

Batun sadakar Uku, ko Bakwai, ko ta Arba'in
Kaza shekara wallahi babu ruwana

Irin masu kukan nan da ihu da razana
Don Allah na roke ku kar kuyi kaina

Ina tausayin ku kwarai zuwa gun jana'iza
Kaza wahalar tafiya hakan kabarina

Kaza wahalar wanka da dauko ni don zuwa
Cikin makara tafiya zuwa karshe na

Hakika a rannan da da ikon da zan iya
Ya sa tausayin a wajen dukan jama'ana

Anan zan tsaya domin wasiyarmu ta tsaya
Mudi Spikin ne uba ga Amina

Wakar Shehu malam Nasara Kabara; Daga Mudi Spikin

Bagadada suna ajabi nasa
Don sun ga irin himma tasa
Suka ce kai wannan ya isa
Har yanzu suna Allah yasa
Su ga Alhaji malam Nasiru

Qadiriyya yai zurfi ciki
Darajarta kwarai yai arziki
Jama'a da yawa duk sun saki
Hairi a gare shi daki-daki
Kuma ga takawa gun Nasiru

Shi gwarz ne mai kokari
Mai kamala mai kyawon shiri
Ga mutunci gashi da hankuri
Ko ina an san shi gari-gari
Kwarjini sai Malam Nasiru

RASHA Abokan Fita Kunya; Daga Mudi Spikin

Wannan waka ta jawowa Malam Mudi dauri a gidan yari. Domin a fahimtar Turawan Mulki wannan wani sako ne da kan iya tunzura talakawa suyi bore, kuma kan iya jefa kasa cikin juyin-juya hali irin na Kwaminisanci. Mudi Spikin ya rubuta wannan waka a 1948. Ga dai wakar

Ya yan'uwa ku zo don ku ji ni
Zan wo bayani akan Rusiya

Gama Ingilishi fa sun tashi haikan
Suka suke yi akan Rusiya

Da babbata hanyarsu don kar a so su
Don kar su zo nan mutan Rusiya

Shine nake so in wo dan bayani
Domin ku gane kasar Rusiya

Kasa ce ta kirki da himma garesu
Da kaunar mutane kasar Rusiya

Wakilinsu Malik sunansa ke nan
Sunan musulmi da ba fariya

Ni dai ace yau zan samu iko
Ni sai in koma kasar Rusiya

Kamar na iya tsunts inje can in Zauna
Idan na tuno su mutan Rusiya

Girmama kowa dabi'arsu ce
Ibada kamar Hajji sai Rusiya

Da son musulunci da bayar da zakka
Yawan azumi sai kasar Rusiya

Kwalta na banza damu bamu samu
Da kafur akeyi acan Rusiya

Da banki na rance idan har kana so
Ko fam Dubu Goma baki daya

Musaki acan sai ya zauna da Gwamna
Wajen shawara babu kin gaskiya

Sa'annan da sauran abubba na kirki
Suna da yawa a kasar Rusiya

Gidaje dubu Goma ne don Musakai
A yau su kasar wane ba ko daya

Akwai Talakawa akwai Tajirai
Kamar dai kasarmu ta Nijeriya

Anan gaba na tabbata babu shakka
Nijeriya zamu zam Rusiya

Mu zam mun fice daga gun Ingilishi
Mutanen daba sa rikon gaskiya

Sun barmu babu kudi babu gona
Babu abin yi cikin gaskiya

Sun shekaru yanzu Hamsin kasarmu
Ba taimako babu son gaskiya

Ta'ala Rahimu kadai taimakemu
Ka kawo mutan Rasha Nijeriya

Idan aka ce wa ya tsara ta waka
Ya bayyana halin mutan Rusiya

Ba zan boye suna ba ko za'a nema
Mudi spikin maso Rusiya

Gama bani tsoro na dauri hakika
Akan Rasha ma sai in bar duniya

Karara; daga Malam Mudi Spikin

An haifi Alhaji Mudi Spikin a ran 1 ga watan Oktoba 1930, a unguwar Darma da ke birnin Kano. Yayi karatun qur'ani a hannun Malam Umaru Badamagare. Bai taba zuwa makarantar boko ba, amma duk da haka, ya zauna jarrabawa GCE Ordinary level, ta hanyar yin rijista da wata kwaleji a Ingila, acikin 1960. Ya sami illimin zamani ne a hannun abokansa na gwagwarmayar siyasa irinsu; Malam Sa'adu Zungur, Malam Aminu Kano, da kuma Alhaji Yusuf Maitama Sule. Yana cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar kwato yancin talaka wato NEPU a 1950. Ya fara rubuta wakokinsa tun a 1948, ya fara da wakarsa ta "Rasha Abokan Tafiya", da kuma wani raddi da yayiwa malaminsa, wato malam Sa'adu Zungur maitaken "Arewa Jamhuriya Kawai".

A ya jama'a ina tashin
Ku dan ku rage yawan bacci

Ayau na zo gareku da sha
Wara don kara inganci

Mu wo himma mu tashi tsaye
Mu gyara kasa ta san yanci

Mu kawo shawara mai kyau
Mu tashi mu yaki jahilci

Rashin illimi ya sanya yau
Kasar nan ke yawan baci

Fa sai mun tsaya gyara
Na sosai babu jahilci

Sannan zamu san matsayi
Mu tsere wa wulakanci

Idan ba tattali a kasa
Hakika dole ta baci

Idan an zubda hakkin yan
Adam domin wulakanci

Idan masana kwarai an zub
Da su domin rashin yanci

Idan sharia ta zam ciniki
Ana nunnuna bambanci

Idan kuma masu aiki sun
Zamo duk babu inganci

Idan aiki ya zamto ba
Ayi, sai an ciwo hanci

Idan hairi a baki ake
Fada sharri cikin zuci

Idan da akwai yawan hassada
Da bata mutum da iskanci

Idan da akwai yawanta saki
Na aure don wulakanci

Idan ba tanadi wai duk
Wata sai anyi angwanci

Idan aure ya zam a kasa
Ana yi ne da jahilci

Idan kayan biki aka mai
Da su tamkar na dillanci

Idan ga jahilai a kasa
Na kin canji da shashanci

Idan da zama na banza, ba
Sana'a ai ta kakaci

A sa fatala gaban goshi
Da hula wai tsageranci

Ana ta musu ana karta
Ana zance na wawanci

Idan kuma ga yawan zargi
Na banza ga rashin yanci

Idan wani dan'uwa wai yayi
Samu ayi munafunci

Idan sharri ya zo a iza
Nufi dai ayi wulakanci

Idan da akwai yawan camfi
Da bori masu shashanci

Idan da akwai yawan tsegun
Guman banza na jahilci

Idan a kasa ya zam an go
Yi bayan masu lalaci

Idan mai gaskiya ya zamo
A kullum zai ga kaskanci

Idan gata ya sanya wadan
Su yin shirme da shashanci

Idan aka maida wadansu kamar
Ace bayi rashin yanci

Idan yan kasuwa suka zam
Sana'a aita hainici

Idan ga karuwai a kasa
A kullum ai ta fasicci

Idan da giya an ta
Ru kullm nuna iskanci

Idan ba tausayi a kasa
Mutane na ta makirci

Idan kuma har amana tai
Kadan sai nuna ha'inci

Idan har maluma suka bar
Sani i zuwa fagen baci

Idan bidia ta zam an gir
Gina kuma babu sassauci

Idan yaya suna sabon
Mahaifa har da kaskanci

Idan a kasa akwai wannan
Hakika dole ta baci

Fa sai in anyi aiki za
Hiri ba nuna lalaci

Sa'annan zamu san haske
Mu tserewa wulakanci

Abinda na farfadan nanYan
'Uwa da akwai muhimmanci

Fa duk gyaran wadannan na
Garemu cikin batun yanci

Mu daina abinda bashi da kyau
Mu daina biyewa jahilci.






Tuesday, April 10, 2007

Wakar Kidayar Mutanen Nijeriya 1973; Daga Hajiya Yar Shehu

An haifi Hajiya Yar Shehu a shekara 1937, a garin Dambatta. Ta halarci makarantar Yanmata dake lardin Sakkwato, bayan ta kammala karatun addini a gida. Ta fara aiki a ma'aikatar lafiya ta Kano a 1953, bayan ta koyar a makarantun Firamare. Daga bisani ta koma kamfanin jiragen sama na Kano, a matsayin mai bada hanyar Tarho, inda ta zama jami'ar kula da ma'aikata na ma'aikatar. Haka kuma member ce a shahararriyar kungiyar mawakan nan, wato Hikima Kulob. Ta dai wallafi wakoki da dama, domin fadakarwa, zaburarwa, illimantarwa, wa'azantarwa, da sauransu, wakokinta sun hada da "Waka da Bayani", Wakar Kidaya, Wakar Zamani dss. wadanda insha Allahu zamu kawo muku su, da dai-dai. Ta rubuta wannan waka, domin fadakar da mutane akan kidayar jama'a wato Census da akayi a 1973. Ga dai Wakar;

BismilLah na fara da sunan Rabbana
Allah Ta'ala Jallah Sarkin gaskiya

Kai ne Sami'un Basiru, Mai ji, Mai gani
Ka tsare mu sharrin, masu sharrin duniya

Domin Muhammadu shugaban duka duniya
Har lahira ma, in ka bashi gaba daya

Don Annabawa har Sahabbai Mursalai
Har dukka dangogin Rasulu abin biya

Kayi taimako agareni kai min kangiya
Kai ne katanga wadda bata zagaya

To zanyi tsari dan Kidaya ne yankuna
Ta Arewa harma duk kasarmu gaba daya

Allah Hakimu hikimarka da ta isa
Kasa mu gane don mu bayyana gaskiya

Don kada mu fada ayyukan shibcin gizo
Da ya kasa dauka, sai ya karo kungiya

Ga gargadina gun sarakai malamai
Lalle ku dage don ku kange areriya

Komai idanu bakuna har kunnuwa
Komai ya baci wuyanku ne zai rataya

Ko Shehu Fodiye ku yaba tuta tasa
Har ma amanar dogare gaba daya

Domin hakan nan sai ku tashi ku taimaka
Akan kidayar na jihannunmu gaba daya

Don kadda a kwaso kyankyaso da su kwarkwata
a zazzage mana nan Arewa mu sha wuya

Allah jikansu na baya manya sun wuce
Giwa saka kawo ban Arewa gaba daya

Dan kadda mu ji ta kururuwa rashe idon kuma
Har ma da makirci na mai kin gaskiya

Kuma kadda jahilci ya sa sarkacen tasa
Ya ja kafa kuma har wuyanmu gaba daya

In anka zo kirga ya tabbata mun zaka
Mun bayyana musu dangunanmu gaba daya

Maza da mata har da yara kankana
Har jinjirai ma wanda sun kwana daya

Kuma har da tsofaffi da basu fita waje
Don Allah duk a fade su kar a rage daya

Domin barin wani, baya ba wani taimako
An fidda dashi acikin mutan Nijeriya

Shi bai ga tsuntsu bai ga tarko ya bace
Sai yai nadama nan cikin Nijeriya

Allah tsare mu da yin hakan, ya yan'uwa
Kuma maganin wannan a bayyana gaskiya

Kuyi tir da masu batun na banza kun jiyya
Makiya jiharmu, munafukanta Arewaci Nijeriya

Har ma suna cewa haraj za'a sa
Domin su wargazar da shirin ta areriya

Kuma don a danne tattalinmu na arziki
Har ma a danne komi nan arewa mu sha wuya

Ba'a kidaya kan haraji kun sani
Yara da mata ba'a sa musu kun jiya

Haka ma a zozzowa da tsofaffi duka
Suma haraji ba'a sa musu kun jiya

Wannan kidaya dai nufinta daban yake
Nan dai asan jimlar mutan Nijeriya

Kuma don a san adadin mutanen jihhunan
Jihar da tafi yawa cikin Nijeriya

In an rabo ita zata samu mafi yawa
Ninkin ba ninkin za'a bata kunjiya

Kan duk ku da ayyukan gona duka
Kuma asibitoci makarantu kun jiya

To zasu samu rabo mafi girma duka
To kadda mu cuci jiharmu nan ta arewiya

Duk wanda ycce ma haraji za'a sa
Ce mai haraji arziki ne ka jiya

Mara lafiya da mahaukata basa biya
ashe haraji lafiya ne kun jiya

Sauki gareshi gun manomi kun jiya
Zakkar abinda ya aikata shi ke biya

Yan kasuwa ma sau guda ne shekara
Ma'aikata ne ba iyaka kun jiya

Dukkan wata kullum akan diba ake
Sisi ake diba a kowace fam Daya

Kai malami har malama kuyi anniya
Ku bada sunan yan uwanku gaba daya

Yaya da jikoki da dangi ba ragi
Har wanda basu gida suna wata nahiya

Dada wanda yaki shiga cikin kirga kusan
Shi zaya sha kunya cikin Nijeriya

Sannan ya zam mugu sharari jahili
Mai taimakawa don a cuci arewiya

To malaman Sansan inai muku gargadi
Dan Allah don manzo Rasulu abin biya

Kuma banda kosawa ku dau hakuri kwarai
A wajen kidaya kadda ku dinga tsamiya

Ku bi sannu-sannu a hankali ba firgita
Kuma ba tsanantawa a kowace tambaya

In ko akayi muku tambaya ta rashin sani
Ku bada amsa kadda ku kosa kun jiya

Kuyi ayyukanku da gaskiya bisa ka'ida
Acikin birane, kauyuka har tsangaya

Ahaiyye iyyenanaiyaye yurai yurai
Malam abin ga da niyyi kada kai tambaya

Na barwa Jallah wa'azu sarki mai sani
Ubangiji ya sani kafin ya darsu ga zuciya

To shugaban kirga muna ta sa ido
Muga ayyukan komi yana kan gaskiya

Don kadda azo da ka taho ayi ta gunaguni
Harma takai mu fagen a dinga hatsaniya

kuma kar ta kai ga fagen abin da-na-sani
Ita ko alama ce ta bacin zuciya

Da-na-sani keya a baya take tutur
In an fade ta ku tabbata an sha wuya

Gabas da Yamma, Tsakiya da Arewiya
Muga kan shirin komi ya zam mana bai daya

Don kada a sayar da dubu a kasa sayan daya
Har ma akai ga fagen ace ya rasa kiya

Alhamdu LilLahi ina yin godiya
Agurin Ta'ala Jallah Sarki shi daya

Tamat bi HamdilLahi waka ta tsaya
Waka a gargadinku nan mu gaba daya

a wajen bayani kada ku damu da tambaya
Yar shehu tai wanga tsari kun jiya

In an ka ce adires ku duba ba wuya
Don ni a kofar mata sai kui tambaya

Nagode Allah har Rasulu abin biya
Alai Sahabbai Tabi'ina da Auliya

Baitinta Sittin ba Biyar ba kunjiya
Na rufe da sunan wanda baya fariya

Wakar Zuwan An Nasara Kasar Hausa; Daga Sarkin Musulmi Attahiru

Shine dai Sarkin Musulmi na karshe, kafi mulkin Turawa. Ya rasu a Burmi a ran 27 ga watan July 1903, bayan sun kafsa da Turawan mulkin mallaka. Ya ki amincewa da Turawan da kuma tsare-tsaren da suka zo masa da su, a saboda haka nema ya rubuta wannan waka, domin ya fadakar da mutanensa illar zama karkashin mulkin Nasara. Hakan ya jawo bore a kasar Hausa, wanda ya sanya, turawan suka yi fito-na-fito dashi. Ganin hakanne ya sanya ya bar garin Sakkwato, inda yayi niyyar yin Hijira zuwa kasa maitsarki. Ya rasu tare da mutane da dama, kuma an kama jama'u da dama, cikinsu kuwa hadda Sarkin Kano Alu. Ga dai wakar

Gudun mutuwa da son rai aggaremu
Da kau kin kaddara abi Annasara

Ina muka yi da dama da hauni suna
Ku tashi mu sa gabanmu mu tsira tsara

Idan ka ce akwai wahala ga tashi
Lahan duka na ga masu biyan Nasara

Idan iko ka kai kak ko ki tashi
Ina iko shi kai ikon Nasara

Idan sun baka kyauta, kar ka karba
Dafi na sun ka baka guba Nasara

Suna foro garemu mu bar zalama
Mazalunta da kansu diyan Nasara

Bakar fitina garesu da kau makida
Ta bata dinin musulmi Annasara

Halin da mu kai ga yau aka bayyanawa
Dalilin ke ga an ka sako Nasara

Ku bar jin masu cewa ba'a ashi
Ina halin zama ga Annnasara

Mu mai da gabanmu Makka mu zo Madina
Madina da Makka dai ab ba Nasara

Batu na Shehu yai yi shi bashi tashi
Sa'a ta ya fade ta ta Annasara

Muna da nufa idan mun samu iko
Mu ja daga, mu kore Annasara

Idan ko sun kashe mu mu san shahada
Muje aljanna sai mu ishe makara.

Sai dai an samu sabani tsakanin masana, a gameda waye ya rubuta wannan waka. Dandatti Abdukadir ya bayyana hujjar cewa, Sarkin Musulmi Attahiru n ya rubuta ta. Amma A B Yahaya shi yana ganin wani malami ne maisuna Malam Labbo dan Mariya Kwasare ya rubutata, inda yace ya samo wannan hujja ce daga Waziri Junaidu.

Saturday, April 7, 2007

Wakar Buhari; Daga Wazirin Sakkwato Buhari 1903

Wannan wakar an rubutata ne a lokacin da Daular Usmaniya ta Sakkwato ta shiga cikin wani halin kaka-ni-kayi. A lokacin da Turawan mulki suka tasarwa Daular haikan! Daga kudancin Daular, ga kuma Rabih daga bangaren Gabas, sa'annan ga kuma yake yake acikin daular, tsakanin Tukurawa da Yusufawa a Kano, da kuma wasu sassa na daular. Marubucin dai shine shahararran Wazirin nan na Sakkwato, wato Waziri Buhari dan Gidado, wanda jika ne ga Sarkin Musulmi Muhammadu Bello. Ya nuna takaicinsa game da yadda abubuwa suka tarwatsewa Daular ta fulani, da kuma yadda ya gaza wajen sulhuntawa tsakanin Sarkin Kano Tukur da Yan'uwansa, wanda hakan yayi sanadiyyar Yakin Basasar Kano. Hakan nema ya jawo ya rasa idonsa. Ya dai rayu, har zamanin da turawa suka ci Sakkwato, ya rasu a farkon karni na 20.
Ga dai wakar tasa;

Jama'a da ku ni ke kun ji aqrani
Tsoho da sabubba, dud da yan sabyani
Ku zan fadama na nesa hal jirani
Na tsorata, tsoro mai yawa ikhwani
Ga abubuwanga da niggani ashjani

In kun bideni ku tambaya mi ag garan
Halin da ajjiya yau dabam ya firgitan
Shagala zaman ashraru ya shiga sai kadan
Kowa da kowa yau ya rage sai kadan
Wannan abin ya tsoratani

Ga abinda nijji da nig gani bisa kowane
Abu na cikinmu ku dubi iko ya dune
Ban san shi da wuri waliyya tab bayyane
Tsoronga Maryamu taggani har tat tuni
ajban li dhalika minka aw ajbani

Kaitonmu ya jama'a ku tashi mu fifika
Ga abinda sun kayi ko kadanne mu taimaka
Bisa gwargwadanmu ku dubi sa'a ta cika
umara'una, ulama'una sun sam tuqa
Sulaha'una, shuhada'una naji bayani

Amma in da zato raina nai tuni
Shibka abinda ka turbuda shi kan gani
Bari firgita don juge-jugen zamani
Baka gadi tsoro gunmu hakkan ka sani
Ko mumini mai quwwatu lil imani

Tunda randa kas san wanda yaika mai sama
Samo rashi, khairan da Sharran ya gama
Bamai ije maka dai cikinsu, tsaya ruma
Komi taho maka hankuri zaka yi zama
Ka wakkalawa ubangiji Rahmani

Kai dan'uwa na so ka lura ka rarrabe
Ga abinda yaffi gareka don ka fice kure
Rike gaskiya ka santa me kake lalube
Inda kasan tuba kakan rike gwadabe
Daba kaji tsoro ba don hidhyani

Kullum ina jin wa'azi inda shuyukina
Nazo karatu naji gun ulama'una
Subhana, kin ji yai yawa don son ghina
Madalla Maryamu kin tuna min na tuna
Can da wuri na zauna cin nasyani

Na kasa farga yau da gobe suna zuwa
Ga mutum shi kasa abinda yayi cikin fa wa
Karfi shi kau da gani, shi kau sha mantuwa
Na kasa tuba ga zunubbai sun yawa
Kuma ga shuyukhi ga halin sibyani

Na roki Allah Jalla shi ka isam mini
Ga abinda yas same ni shi ka biya mini
Ga abinda nis so zahiri in badini
Na tuba ya Allahu gafarta mini
Don Shehu nurin zamanin Usmanu

Tun nan da barzakhu lahira a shi taimaka
Aikin da niyyi na gaskiya shi biya garan
Shi hana ni muggun yalla ko da nufa kadan
Astagfurullaha l' azima shi agazan
Don shehu Abdulqadir Jilani

Domin Rufa'i ubangiji ka raba mana
Rokon da nai maka don badai ka isan mana
Haka na Dasuki gare su nan muka dangana
Da zaman kushewa har kiyama Rabbana
Amsar Takardu agazan Mannanu

Kogi; Daga Limamin Daura Usman 1899

Wannan Waka dai an rubuta ta ne a daidai lokacin da Turawa suka shigo Arewacin Nijeriya. Limamin Daura Usman ne ya rubutata, domin yayi kira ga Sarakunan Kasar Daura, dasu daina zalunci, ya kuma nusar da talakawan kasar illar zalunci. A dalilin rubuta wakar, sarakunan Fulanin Daura suka kore shi, inda ya tsere zuwa Sakkwato, a daidai lokacin da Turawa suka koro Sarkin Musulmi Attahiru. Ana kyautata zaton, ya mutu aBurmi tare da Sarkin Musulmi Attahiru. Ga dai wakar;

Kusan zulmu zulmatun ne a yaum al qiyamati
Fada ta rasulillahi manzo muhammada

Ku shimfida adalci gabas, duk da Yamma da
Kudu da Arewa, du ga ummar Muhammada

Ina Dogarai har Jeka fada da kwarakwarai
Da mata na fada, ku zo ku saurara fa'ida

Kaza yan lifidda, har da yan bindiga duka
Zagage ku saurara har ku samo fa fa'ida

Kaza yan baraya harda yan garkuwa duka
Da yan figini du da mai so yasan fa'ida

Fa kai kuwa wawa dai na wauta cikin gari
Ka dawo ga hanya kasan rahamar Ahmada

Fa ku kuwa yan sarki ku bar bin garuruwa
kuna kwace amfanin mutane mufassada

Kuna yin Kilisa don leka gidaddaje
Kuna gane matanmu kuna sabawa Muhammada

Fa ku kau talakawa fakirai ku zam ku ji
Saraki na sarki ne, Talakka na rabbana

Ina masu sanya ruwa a nono su sai
A kaisu sa'ira gobe nesa ga Ahmada

Wadansu su sa gawasa da kaya su garwaya
Fa domin su sai da guba, su sabi Muhammada

Wadansu dafare su kan sa su garwaya
Su sai she si don basu kamnar Muhammada

Wadansu da yan kuka su barka su garwaya
Suna shan azaba, gobe nesa ga Ahmada

Wadansu suna sanya ruwa su kara da kankani
Abin na haramun ne na nesa ga Ahmada

Ana masu kanwa? to ku saurara nan fadin
Ku tuba ga algushu, na nesa ga Ahmada

Su dibo fara toka su kawo su garwaya
Su saishe to domin basu kamnar Muhammada

Thursday, April 5, 2007

Wakar Zuwa Birnin Kano; Daga Aliyu Dansidi Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau Aliyu Dan Sidi shahararren Sarkin ne a Arewacin Nigeria, yayi fice saboda irin fasaharsa da illiminsa, shi kuma ne sarkin Zazzau na farko da Turawa suka nada. Turawanne kuma suka sauke shi, bayan sun samu sabanin ra'ayi akan wasu sauye-sauyen zamani. Ya zama sarki yana da Shekara Sitiin da hudu (64), yayi sarautar Zazzau daga 1903-1920 . Jikan Sarkin Zazzau Musa ne, Bamalli. Wani abin sha'awa gameda da tarihinsa shine, shi dai bai taso a gidan Sarautar Zazzau ba, ya taso a gidan malanta ne, a hannun malaminsa Limamin Durum wato malam Abubakar. Ya taba samun sabani da Sarkin Zazzau Kwasau (Mai kogin Jini dan Sambo), wanda hakan ya sanya bar Kasar Zazzau, ya shiga yawace-yawace, inda har ya Zauna a kasar Kwantagora a zamanin Sarkin Kwantagora Ibrahim Nagwamatse. Ya wallafi wakoki da dama, cikinsu kuwa akwai Tabarkoko, Saudul Kulubi, Wakar Diga da kuma wannan waka ta Birnin Kano.
Ance wannan waka yayi tane, yayi wata Dabar bankwana da Sarakunan Arewacin Nijeriya suka shiryawa Gwamna Arewacin na Zamanin Turawa wato sir Hugh Clifford, a Birnin na Kano acikin shekara 1914. A zamaninsa akan masa kirari da "Aliyu na Awwa mai iya Sarki" . Sarkin Zazzau Aliyu dan Sidi Batijjane ne na kwarai, domin mun kawo muku wakarsa da yayiwa Shehun Darikar ta Tijjaniya wato Shehu Ahmad Tijjani, ga mai so sai ya duba cikin kudayen Turaka wato Archives. Ga dai Malam Aliyu dan Sidi a Birnin Kano.






Muna gode Allah da yayi nufi
Yasa muka taru a kofar Kano

Muna yin Salati bisa ga Muhammad
Dalilinsa anka yi mu akayi Kano

Mu kara salati bisa ga sahabbai
Mu sami dalilinsu komi anu

Zama hali ma nahnu shi muka zance
Da niy yi shiri zani birnin Kano

Diya min Muharram ga ran Lahadi
Na hau bisa jirgi zuwa na Kano

Ga Chalawa ni kwana guda muka tashi
Muna gaisuwa da dawakan Kano

Dawaki na baki kaza yan gari
Fa har muka sadu da Sarkin Kano

Da fa muka gaisa ya juya na bishi
Dada har ya kaini masauki Kano

Ina gaida masu zuwa daga nesa
Da shaihu na Kukawa ga shi Kano

Da Mahoni Laraba Gaidan Kano
Kaza Lamido Adamawa a birnin Kano

Katagum, Hadejia, kaza duk da Gombe
Misau Jama'are a birnin Kano

Da Zazzau da Bauchi, kaza Katsina
Da Daura, Gumel gasu birnin Kano

Kazaure da kau Sakkwato har da Gwandu
Kabawa da Argungu birnin Kano

Mutan Gwadabawa da Kwanni da Yabo
Gamuwa da Anka a birnin Kano

Da Meri da Augi mutanen Yamma
Mutan Jega ga su a birnin Kano

Mutan Wukari, mutanen Ibi
Da Loko da Lokoja a birnin Kano

Da Yawuri har Kwantagora Rijau
Mutan Wushishi da Bussa a Birnin Kano

Kushurki da Kunguna har Kuriga
da Gwari na Waki a taron Kano

Mutanen Maginga mtan Kanbuwa
Na Sulame gasu a birnin Kano

Illori, Nufawa, Lafai, Agaye
Fa hatta Abuja a birnin Kano

Fa har Tunkiya gata ga Damisa
Mashayansu dai sunyi kiwo Kano

Kutawa mutanen Kafi, Lafiya
Da jam'an ta Baroro a birnin Kano

Da Mahmudu Ningi da Sarkin Bura
Da Sarkin na Bassa a birnin Kano

Ina gaida Sarkin Kano Yayi Aiki
da anka yi taro garinsa Kano

Gidaje na sabka dada har liyafa
Da taryan sarakai su sabka Kano

Da sabkan farare da sabkan bakake
da birni da kauye a birnin Kano

dalili gareni in san yayi aiki
Zama nayi ko da nika je Kano

Da shi da ya sabkar da su masu sabka
Ta'ala shi bamu sawaba Kano

Fa naje da yare iri da yawa
Da busa da ganga a taron Kano

Fitawa da doki dako Feluwa
Da sayi suna sukuwa nan Kano

Mutane da doki da niz zo dasu
jimillansu hamsa zuwana Kano

Kurama, Katab har da Cawai duka
Fa duk sunyi wasa a taron Kano

Da Jaba da Gwari mutan Rumaya
Kadara fa na kai su taron Kano

Ga babban suka na dawakan saraki
Na Zazzau fa sun ka ci taron Kano

Da anka yi wasa fage ya hadu
Muhudanmu sun yi ado nan Kano

Ka rarra, ka Kabra, ku san tumkiya
Bata iya kabra ba Kano

Da tauri da tsauri idan anka goga
Guda sai shi yanke guda a Kano

Ba'an gwada karfe ba, sai inda karfe
Duwatsu fashewa su kai a Kano

Ka zaga Kano har kasan dan Kano
Na birnin Kano wanda yasan Kano

Ka kau tambaye shi tsakani da Allah
Ya bayyana maka taron Kano

Na yawata Kano gani ga dan Kano
Dada har nasan anguwa a Kano

akwai anguwan madawkin Kano
Da sunanta Yola a birnin Kano

Daneji, da Soron dinki akwai su
akwai Lungunawa da Sheshe Kano

Da Marmara duk unguwa ce duka
da Kunduke Kwankwaso duk a Kano

Akwai Wudilawa akwai Na'ibawa
Da Ibadi Fasa-keya a birnin Kano.

Caranci, Gudundi, akkwai Jarkasa
Makankari, Garko duk a Kano

Kusura, Kudancin Kano da Wazirci
Da Siradi akwai ta Kano

Karofi na Wanka da Shuni akwaisu
Madatai da Daushi akwai su Kano

Karofi na Sudawa, Zangon Ciki
Da Dandago, Diso akwai su Kano

Akwai unguwar Durunmin Kaigama
Da Bulbulas, Guntu akwai su Kano

Da Yalwa da Dala, Madaboo duka
Suna nan Arewa da Kurmin Kano

Akwai wata ko unguwa Masaka
Da Sarari da Sagagi Birnin Kano

Awai unguwa Waitaka a Kano
Akwai Durumin Dakata min Kano

Mahanga, Kutumbawa duk unguwa ce
Da Damtsenka Tsage a Birnin Kano

Akwai Cediya ta Kuda unguwa ce
Akwai Kalaman Dusu duk a Kano

Da Lallokin Lemu, da kau Makwarari
Makwalla fa duk unguwa ce Kano

Dabinon Awansu da Mandawari
Da Alfindiki Kwalwa duk a Kano

Tsaya in gajarta guda don kau yawaita
In kawo wurinta da niyyi Kano

Fa har muka kare naje Nasarawa
Garin makarantan su Sambon Kano

Akwai makaranta karatun Bature
Acan Nasarawa ta kofar Kano

akwai yara masu Karatu na allo
Akwai masallaci ginanne Kano

AKwai Makaranta ta al Kur'ani
Da litattafanmu a birnin Kano

Akwai wani dakin zaman masu ciwo
Akwai matsarinsu a kofan Kano

Masaka, madunka, da mai Sassaka
Gidansu guda makarantan Kano

Makera, Badukai da masu kudi
Cikin makaranta ta kofar Kano

Cikin shekara goma sha dai ga daula
Aliyu binu Sidi zuwanshi Kano

Ya wake ta yan baya domin su ji
Su san wakacin tafiyanshi Kano.

Dadadan Dadin Saniya; Daga Dr Aliyu Aqilu

Malam Aliyu Aqilu dai ba bako bane ga wanda yasan wakokin Hausa. Asalinsa mutumin Sakkwato ne, duk da yake a Kano yafi shahara, kuma anan iyalinsa suke, ana kuma Allah yayi masa rasuwa. An haife shi a shekara 1918, a garin Jega na kasar Gwandu, wanda a yanzu ke jihar Kebbi. Cikin malaman da yayi karatun alqur'ani a gunsu sun hada da ; mahaifinsa Aliyu Madaha, da kuma Alhaji Muhtar Tsoho, da Malam Muhammadu dan Takusa, da M Ban-Allah, da kuma malam AbdulMumini. Ya fara zuwa Kano tun yana da kamar shekaru 15, babban malaminsa a Kano shine: Malam Mahmudu na malam Salga, kuma Muqaddaminsa na Tijjaniya shine Malam Salga. Ya zauna a Borno shekara 23. Malam Akilu Aliyu gogaggen dan siyasa ne, kuma mai bin akidun siyasar NEPU, kuma sana'ar da aka fi saninsa da ita, itace dinki. Ya samu Digirin girmamawa (Honorary Doctorate Degree) daga Jamiar Bayero ta Kano, kafin rasuwarsa. Ya wallafi wakoki da dama, cikinsu kuwa sun hada da na addini, siyasa, zaman tare, tafiye-tafiye dss. To acikinsu ne na zabo mana daya daga ciki, kafin in Allah ya yarda mu kawo muku sauran, wannan waka kuwa itace wadda fasihin Sha'irin yayiwa Saniya. Ga dai wakar;

Ya mai ni'ima mayawaiciya
Ya mai kudura makadaiciya

Haske da basira naka ne
Ya Rabbu ka buden zuciya

Domin inyi waka yar kadan
Mai yar magana mashahuriya

Amma a takaice a dan mu san
Dimbin amfanin Saniya

Sunce mata dadi goma wai
Wannan magana na dai jiya

Wato maganar na ji ta ne
Karba tata sai na waiwaya

A'a karbarta da lokaci
Sai na juya na waiwaya

Ba goma bama wane dari
Metan suke har da guda daya

Wa za shi iya shi kididdige
Dadadan dadin Saniya

Nan dai a takaice guda darin
Zan zo muku yanzu da dai daya

To sai muyi tsit domin mu ji
Zan fara bayanin Saniya

Mamaki ne da tu'ajjibi
acikin sha'anonin saniya

Tirkashi! O'oi, wane mutum
Sanbarka dau duka saniya

Kin dau kaya kin dau mutum,
Da abinci mutum ya rataya

Kallonta shi sanya farinciki
Kukanta shi sanyaya zuciya

Shafarta shi sa maka walwala
Dubarta idonka shi sanyaya

Ba'a samu guda ba na yasuwa
Daga kowane sashin saniya

Madara, Kindirmo, Dakkashi
Kangar da Cukui daga Saniya

Kassanta ana Alli dasu
Ya kyautu anan in waiwaya

Kashinta ana shafe dashi
Losonmu na da Nijeriya

Kirginta ana wasaki da shi
Mun san haka duk Nijeriya

Har gobe ana kiri da shi
Da gareshi ake bulaliya

Na lura ana Waga dashi
Da gareshi ake yin tsirkiya

Shike daure karaga da shi
Tsani, Barho da Takobiya

shike yin takalma da shi
Kwakkwaran kirgin Saniya

Na lura da shi ke yin kube
Na wuka, Barho da Takobiya

Ka tuna fa da shi ke Janjami
Sai mai girma kan rataya

Baza na yawaita maganganu
Ga yar sa'at magajarciya

Ba nuna gadara ko isa
Ko kasaita matsananciya

Daga nan ya zuwa can ko ina
Acikin duka sassan duniya

Na hanga, zaune a hankali
Kuma na maka duba na tsaya

Wai ko zan gano na yasuwa
Wani dan gutsure daga Saniya

Anya kuwa a same shi dai?
Amsa naka so na tambaya

Shin ko ko akwai abu ne daban
Marashin fa'ida daga saniya

Indai da akwai a fada muji
Daga Sa ya zuwa kan Saniya

Guzuma ta zamo ko Dangwala
Ko Karsana ce ma Sauraya

Amsa a'a ai babu shi
Abu yasasshe daga Saniya

Wannan kuwa ta gamsar da ni
Amsa ke nan makatarciya

Mai haske gata a wartsake
Har yau mai dada zuciya

Wakar sunan dana bata shi
Dadadan dadin Saniya

Wannan jin dadin ya isa
Daga kowane sashin Duniya

Kar wai ku cane gefe guda
Daga kowane barin kun jiya

Me zamu kwatanta ne da shi
Ga misali, sai dai lafiya

Wannan itace duk kan gaba
Daga duk jin dadin duniya

Amma a wadata kowace
Daga kowane fannin duniya

Jama'u-Jama'u duk an hadu
Cewa dai babu ya saniya

Fifiko nata yana gaba
ga na dabbobi duka saniya

Yai nisa basu tara da shi
Ko sunyi gudu sun garzaya

Ba za fa su shawo kan sa ba
Ko sun zaga sun kewaya

Kai ban zaci sa riske shi ba
Ko sun tafiya matsananciya

Abu ne mawuyaci dankari!
Har yanzu wuyar mawuyaciya

Gaba dai, gaba dai, gaba dai, gaba
Gaba, Nagge, da aiki saniya

Ja al'amarinki madaukaki
Gaba dai ba baya ba Saniya

Ja dai sha'aninki na arziki
Ke baki shiga sha'anin tsiya

Madalla, madalla dake
Tsarinki da kyawo saniya

Sannunki nace na gaida ke
ni na yabi aikin saniya

Girman daraja, girman isa
Sannan darajar mayawaiciya

Taure yace a sanar dake
sakon akuya da na Tunkiya

Sun mika wuya sun sallama
Cewa a nada ki sarauniya

Sun sa hannu da guda-guda
Sun lamunce daga zuciya

Rago tuni shi ya sallama
Dauke shi jakada saniya

Dabbar da ta ja gaba dake
Ta dau wahala matsananciya

Gurbin riba sai faduwa
Sai rarraba hajjar mujiya

Tsini akaje nema gaba
Kunda ta gagara tun jiya

Wannan magana bata fadi ba
Wa zaya gaya mini "Kai tsaye"

Jama'a daga nan zan dakata
In sanya alama in tsaya

Ni naku Aliyu Aqilu ne
amsa a wajen maitambaya.

Wednesday, April 4, 2007

Begen Yakin Shuhadar Hadejia; Daga M Ibrahim Katala

Acikin shekara ta 1906 ne, Turawan mulkin mallaka tare da sojojinsu dauke da muggan, makamai suka yiwa birnin Hadejia tsinke. Inda hakan tayi sanadiyyar gwabza wani mummunan fada tsakanin Turawan mulkin mallaka da kuma Jaruman kasar Hadejia masu gwagwarmayar kwatar yancin kai. Hakan yayi sanadiyyar yiwa mutanen Hadejia kisan kiyashi, inda aka kissima cewa, dubban mutane ne suka rasa rayukansu a sanadiyar hakan. Babban abin lura shine, dukkan wadannan dubban bayin Allah da suka rasa rayukansu, sun rasa ne a rana guda, cikinsu kuwa harda Sarkin na Hadeja a wannan zamani, Wato Sarkin Hadejia Muhammadu. Wannan waka ta tattare dukkan abinda ya faru a ranar, ta kuma yi cikkakken bayani gameda yadda Shahidan Hadeja suka jajircewa abinda suka kira, bautar dasu acikin kasarsu. Koba komai, wannan ya nuna yadda yan Afrika suka dauki yancinsu da muhimmanci. Da fatan Allah ya jikansu, nake cewa ga abinda ya samu;

Allahu sarki Shi kadai yake Wahidun
Sammai da kassai, Jallah bashi da kishiya

Shi ba fari, shi ba Baki ba Ubangiji
Ba ja ba, ba alkashi ba, shi ba rawaya

Ba sake-sake ba, ba kamar yarani ba
Shudi da kore Jalla bashi da mai kama

Zatinsa baya tattara, ba rarraba
Da kawai da motsi babu yayi ko daya

Sarkin da ba na biyunsa, ba na ukunsa
Fahami basira zani begen shahidi

Ranar Talata mun ga tashin duniya
Ranar Muhammdu yai shahada zahira

Yayi jawabi ya cane shi bai gudu
Shi bashi mai kamu a daral duniya

Rago akan kora, a bishi a kam masa
Amma sadauki ba gudu sai faduwa

Sarki Muhammdu yai jawabi ya cika
Shi bashi mai kamu ya ja shi ya tunkiya

Dan Mele Sarkin Yaki shi kuma ya cane
Muna da rai Sarkinmu baya kamuwa

Ma'aji Salihi yai jawabi ya cane
Mun dau shahada zahira bahakikiya

Manya da yara duk shirin yaki su kai
Kowa yana wanka, yana kuma Alwala

Kowa yana sallama cikin ahli nasa
Sun sa gabansu a lahira ba dawaya

Jama'ar Hadejawa dada duk suka hallara
Kowa yana ce "yau ma zama shahidai"

Shi bai kamar tsoro, balle ya razana
Kan ya ije ma babu kingin hamzari

Ajali idan yai babu kwana duniya
Kai dai zamo kullum shiri duk safiya

Shi bai kamar tsoro, balle ya razana
Bai san gudu dan Garba sarki jarumi

Mutuwa tafarki ce kowa zaiyi ta
Kullu nafsin kowanne ya dandana

Aka daura sirdinsa ya hau bisa ya tsaya
Yace "mu dau himmar shahada Zahira"

Sarki Muhammdu bashi tsoro ba gudu
Allah, Ma'aiki su yake tsoro kadai

Hauninsa Linzami mayani ya rike
Damansa tsabihi salatin musdafa

Dan maikaratu, tudun kasa ba dawaya
Dan Garba, jikan Sambo sarkin adali

Duka mai shahada auwalinsu Madacima
Suka barace shi da fari, ya mutu shahidi

Farkon hawan yakin Talata kun jiya
Galadima, Sarki Haruna sune awwali

Alkali, Sarkin Yaki, Kaura Ahmada
Sarkin Arewa sun kaje can tsaye

Suka jeru har da nan kofar gabas
Kafin su zabura mairuwa ta tarda dasu

Kasan Igwa, da fari aka yamutsa
Doki mutum na faduwa ba lasafi

Igwa tana tashi madafa na zuba
Yau sai ta Allah babu Sauran shawari

Sadaukan Muhammadu basu tsoro ko gudu
Sun dakace kofar gida sai faduwa

Sabo, da jikan Tete su harbi suke
A nan a kofar fada duk suka tuntsure

Firyan Hadeja, shi da Bori na Salihu
Kofar Gabas suka fadi duk sun tuntsure

Ai babu mai mutuwa gaban ajali dada
Kan surfa gero, kan daka, wasu kan fita

Hukunci idan Allahu yayi nufinsa
Ba mai tsimi balle dabara ko daya

Tamkar kamar inuwarka baka guje mata
Kan kai gudu ta bika, kai tsai ta tsaya

Attas yana yawo kamar burduduwa
Tamkar zubar wake, acan a masussuka

Ya ratsa soraye, ya rada katanguna
Kamar kabewa, ko kamar tunfafiya

Ya sha zarar Soro, ya ratsa katanguna
Kago da zaure sun fi karfin lasafi

Tsarnu da kurna hakka sa durumi dada
Yansa dabinai, cediya da itatuwa

Rannan musulmi munga kayan al'ajab
Allah ma'aiki su kadai ne magani

AbdulWahabu baka yana hannu nasa
Attas ya samar, nan ya datse tsirkiya.

domin karin bayani, sai a nemi litttafin Dr Haruna Wakili, na Mummbayya House Kano, maisuna Zuwan Turawa Hadejia.

Wakar Kuyangin Sakkwato; Daga Sandan Baba1900

Acikin wasu Kundayen adana rubutattun wakoki dake National Archives Kaduna, an tsinci wani File mai No O/AR 2, wanda ke dauke da wata wakar ajami, wadda F Edgar ya samo a shekarun farko na karni na 20. Acikin File na 20 ne wannan waka take, wadda aka hakkake an kattama shi acikin shekara 1911. Bisa ga dukkan alamu Edgar ne ya kwafi wakar da hannunsa, cikin wata takarda falle daya, wanda aka tabbatar da cewa, zai wuya a samu inda ya kwafo wakar. Amma duk da haka ya rubuta sunan wanda ya kwafa, ko kuma ya wallafi wakar wanda ya kira da Sandan Baba. Sai dai kuma bai bayyana kowaye shi wannan Sandan Baba ba, ko kuma mutumin ina ne shi, ko a ina ya ganshi, kwafa yayi daga gurinsa, ko kuma reara masa yayi, shi kuma ya rubuta, Allahu a'alamu? Sai dai a wani File mai no 61, wanda aka sanyawa kwanan wata kamar haka; 1909, an rubuta wata waka maisuna "Wakar Yabo/Bege" , daga Sandan Baba mutumin Sakkwato, inda aka bayyana cewa, Sandan Baba ya rerawa wani malami wai shi Malam Bako wakar, shi kuma ya rubuta ta. Wannan ya dan bada haske na gano cewa, Sandan Baba dai ya reara wakar ne, inda Malam Bako da Frank Edgar suka kwafe ta, ko kuma shi malam Bako ya kwafa, shi kuma Edgar ya samu a wurinsa. Bisa ga dukkan alamu, Edgar bai san Sandan Baba ba, amma yana da masaniya akan Malam Bako.
Wakar dai ta kunshi abubuwa uku, akwai Zambo, Habaici da kuma Yabo. Badai takamaiman kowa akewa wadannan abubuwa, ko duk mutum daya ne, ko kuma mutane da dama. Amma dai kusan sanin kan kowane cewa, abune ba sabo ba ga Yanmatan kasar Hausa, su kirkiri waka don Yabo ko Fallasa, da sigar Gada. Don haka tabbas wakar dai ta Yanmata ce, da suka rera, saboda wasu dalilai da dama.
Ga dai wakar yadda take:

Shiririta ararrata
Kare gadon gida yayyo

Bani bukinka da shara
Sai ranar zuwa aiki in baka taro ka futassan

Farin wake na banza ne
Ko an matsu ba'a gumbatai

Bambeni ka gara gije
Kurche gidansu tag gado

Domin Biri a janye kadarko
Bika da shirin tuma yazzo

Kwa bace ni in rama
Don ba shi ka chi san ba

Anini mai kammarSisi
Da tsakka gashi fudajje

Kwabo kau mai kamar Fataka
Da tsakka gashi fudajje

Mai-Gwanja gaton shigifa
Na mallam-dan-majidadi

Mai kyautar dala da dala
Na malam-dan-majidadi

Diyal laka ta banza ta
Don bata zuwa tayo wanka

Diyal Danko ta banza ta
Don bata fita cikin rana

Zancen daka sai mata da miji
Hanyar bisa dole sai tsuntsu

Garar kasa maganin ajiya
Zago mai fanfatse kaya

Bani zuwa ga yanboko
Gara nazo ga yan madara

Dan boko sai hawan doki
Amma ba kudin sati

Mai rai duk masami ne
Zabarma akwai bidar kuddi

Limamin gidan Joji dogo ketare ka ciro
Har ya manta wando nai

Kuku da Boyi sun rantse
Sai sun dauki yar gwari

Tulu dai ka shan yawo
Randa na nan cikin daki

Mai rai duk shi dau himma
Ayi ta batun bidar kuddi

Dan kawo rinin Allah
Madilla masoyina

Namijin kuti mai kafar kwabi
Har ya raina matatai

Randa na cikin daki
Allah shika bata ruwa ta sha

Tukuruwa mai kaya boye
Gawo da kayarka ka girma

Tataka sai aba doki
Nama sai aba Zaki

Tafarnuwa ta faye yaji
Amma ga maganin sanyi

Dabino farkon ka Baure ne
Acan karshe kake zaki

Anini dan mutan Lokoja
Bana yazo kasar Hausa

Kwa doke ni in rama
Don bashi ka tufasan ba.

Ga mai son jin cikakken bayanin wakar sai ya nemi makalar da Grahm Furniss da Yunusa Ibrahim suka gabatar, mai taken; An Early Twentieth Century Song: "Wakar Kuyangin Sakkwato" A mujallar Harsunan Nijeriya, xvi, 1991/92. CSNL Bayero University Kano. Nigeria.

Sunday, April 1, 2007

Yabon Manzon Allah Daga Dr Aliyu Namangi

Allahu shi bani sani da basira,
In yi yabo bakin ‘karfina.

In yabi Sidi Muhammadu Bawa,
Mai hana sauran bayi ‘kuna.

Yi dad’in tsira Allah da aminci,
Gun manzonka dare har rana.

Da alolinsa da kau sahabbansa,
Da mu mabiyansa dare har rana.

Baicin na cika wannan kalma,
Begen annabi manufana.

Yabon manzon Allah addini,
Shi yafi dace irin sib’ina.

Yabonka Muhammadu nan na fi auki,
Ba ruba bad a d’an damana.

Ba ni da mulki ba ni da aiki,
Begen annabi ne nomana.

Ba ni da guru ba ni da laya,
Sunan annabi ne shingena.

Ba ni da k’arfi ba ni da k’arfe,
In koma Maka ne fatana.

Abin nema a garemu ziyaran,
Wannan d’a mai dad’in suna.

Mai kyau, mai natsuwa, mai kunya,
Sannan ga shi da dad’in suna.

Ina k’aunannka Rasulillahi,
Haske mai dushe zafin rana.

Ina son mai k’aunanka Muhammad,
Ko ya auri d’ayan matana.

Ina kyaman mai k’inka Muhammad,
Ko shi yai mani ragon suna.

Tun da a kai shi yake mashi gandu,
Bai fasaba walau d’ai rana.

Da rana yawan azumi, a darensa,
K’iyamullaili shike duk kwana.
Shirunsa, tunani, kalmominsa,
Gun jama’a wa’azi ko izna.

Allah y a ce ma Ibrahim,
“Na sanya ka maji dadina”.

Ya kuma ce ma Rasulullahi,
“Ka fifita cikin bayi na.

Kai kafi kowane bawa girma,
Don kiwonka da alfarma na

Ba mai daraja tamfalka Muhammad,
Don kiwonka da haddodina”.

Albishirinku masoya Allah,
na ga Amina cikin barcina.

Wadda ta haifi Rasulullahi,
Watan Ramalana a barcin rana.

Na nemi ta sami zama mu yi tad'i.
In cusa shi a wak'ok'i na.

Ban samu ba sabo da lalura,
Don shi na koki irin halina.

Nai fata tahowar fa dalilin,
In koma Maka ne wata rana.

Ko ya zamo shine sanadiyyar
In ga Rasulu cikin barci na.

Ya ce "Bila maza ce ma Aliyu,
Namangi ku zo inuwar sorona".

Mu zo mu ishe yai zaune a zaure,
Ga sahabansa suna kallona.

In gurfana a kan darduma
Hairul Halki yana duba na.

Ya ce mani "Zauna daina sagwangwan,
Kai mani hira kana garkana".

In ce madallah Rasullilahi,
Yau na sami abin nema na.

Tun da na sha inuwar soronka
An warke mani cutocina.

Kuma tun da na zauna cikin sahabbanka,
Yau nai zaune cikin birni na.

Mashigin birnin ya tsarma yak'i,
Ya kuma tsarma hararan arna.

Allah shi ya yabe ka da fari,
Kafin in yi da baubaucina.

Na kuma iske mutanen kirki,
Sun yi da Arbi gaban Hausana.

Kai a ka baiwa Liwa'ul hamdi,
Da tajul izzi da Babban suna.

Wanda ya sa sammai suka zauna,
Taurari da wata har rana.

A kai ma k'asa tuhuwa da yabanya,
Yai ma ruwa a kwari magudana.

Ina k'aunarka Jakadan Allah,
Son, ya zamne cikin bargona.

Don haka in halshe ya yabe ka,
Sai in ji shi cikin kwanya na.

Aka kwab'e halshe na da yabonka,
Har ya zame mani filin gona.

Tuntuni sunayenka Muhammad,
Sun shuka mata baitotina.

Gonar ta yi gamo da yabanya,
Kowa na sha'awar nomana.

Don haka ne fa mutanen kirki,
Kowa ke sha'awar nema na.

In kwana a bene kan darduma,
In sha in ci ana zak'ina.

Ina rok'onka Rasullullahi,
Sa hannunka rik'en dama na.

Ka ce mani "Yadda ka so ka samu,
Yau dai ga shi kana soro na.

Ko yaushe aka tsaida halitta,
Al'amarinka yana hannuna".

Ni na ci albarkanka Muhammad,
Ba ni d'ai ba da 'yan bayana.

Kai tsaye kai yak'i da juhala,
Har muka san darajojin juna.

Ka ci garin yakin kafurrai,
Sorayensu ta komo gona.

Babu ya kai a cikin ta halitta.
Ba za ai shi ba ko wata rana.

Allah shi yi tsira da aminci,
Hal abada a dare har rana.

Kar su gushe ga uban Ibrahim,
Mai zance da wata har rana.

k'asa na alfahari da zamanka,
Tun da ka mai da gumaka gona.

Barzahu na fahari da zamanka,
A tun da ta zammaka soron kwana.

Toya matsafa ratattaka gunki,
Baban Fadima ga hannu na.

Sa hannunka mafi albarkar,
Hannaye, ka rik'e dama na.

Ka ce mani "Yadda ka so ka samu,
Yau banbad'o kana hannuna.

Uwa da ubanka da kakanninka,
Da matayenka kuna hannu na.

Da 'ya'yenka da jikokinka,
Da mai k'aunarka kuna hannuna.

A da Iblis ya cika a yak'i,
Amma yanzu kana hannu na.

Na kwato ka da yardan Allah,
Na jefaka cikin barwana".

Uban Bila baban Salmanul,
Farisa ka ji irin fata na.

Zababbe a halittar Allah,
Kyakkyawa ga sifa har suna.

Mai k'aunar cutarsa ta warke,
Shi ta yabonka dare har rana.

A yabonka Muhammadu ni ne sarki,
Na kau san da mafinfinta na.

Sarauta ta begenka Muhammad,
Ba fahari ba wuni har kwana.

Na gaisheka Rasulullahi,
Amma ka ji irin fata na.

Ran saukar ajali ku halarto,
Har sahabanka wurin gawa na.

Sui mani wanka, kai mani salla,
Har ku had'a ni wurin barci na.

Da albarkanka na Abdullahi,
Da nana Amina nike fata na.

Ka yi min addu'a ga ta'ala Jalla,
Shi gafarta mani aibobi na.

Shi rahama ga musulmi d'urran,
Ba da fari, wuni har kwana.

Ya rufe mu da annuran begenka,
Annabi ka ji irin fata na.

Wakar Yabon Bawa Jangwarzo (1790)

Bada razana kigon tama
Dan Alasan mai tambari
Bada razana kyauren gari
Bawa kai na magajin gari
Ki gudu sunan sa ne
Sa gudu sunan sa ne
Ni ban ki biya Bawa ba
Ga sirdina aje
Linzami na aje
Kaimi na nan aje
Turkena na nan kafe
Sai rashin doki ag garan
Ba batun yaki munka zo ba
Gaisuwar mutuwa mun ka zo
Da batun yaki mun kazo
Wurno bata yini ko ta kwan
Shiki da dole, tawayen gari
Kankanana nan kajinmu ne
Wadan Galadi, wadan Tubali
Manya-manyan kajinka ne
Kar ka tam musu, sai ran buki
Dan Taka'ida jigon gari
Uban Dawaki Salami
Yai karo da samarin Jitau
sun jisshe shi gaton kaddaji
Hal wayau ma bai tashi ba
Mutan Badarawa ku daina bugun Tanmbari
bawa bai zaka dominku ba
Ku zo mubi jigon gari
Ko mu samu Dawaki mu hau
Da muna tafiya ta gaya mun ka bi
Ko kaya bata soke mu ba
Bawa na Babari, dan Alasan mai shisshinniya
Dan Taka'ida shingen gari
Bawa kai naka bi, babu wargi
ku zo ku bi mai bada kaya
Ko kusan girma nan garai
Ni abinda nike so da kai
Ko ina zaka zo dud da ni
Ni gareka nike taulahi
don in sami farin zuciya
Baiwa kai ka tsiro cin gari
Dan Alasan mai arziki
Yan'uwa ku zo u bi mai arziki
Ko mu sami dawaki mu hau