Fatara mai sa a lalace
Ta ki yarda ma kasan rance
Yinwa mai kai maza kwance
Ta kashe ba sai da aibi ba
Yau Lebura ne kamar Zakka
Aiki rani zuwa kaka
In gwamnati zata sa doka
Lebura baza su karya ba
Aiki kullum cikin taro
Ana abu sai kace horo
In dai Allah ake tsoro
Da lebura bai talauci ba
Bamu san haka zaku fara ba
Kuyi alkawari ku karya ba
Kaya ba za shi zango ba
Lebura bai bada iko ba
Jirgin sama fankamin wofi
Mota bata zuwa rafi
Ta nutsa ta haya ana tafi
Wannan bamu fara samu ba
A hake titi a sa kwalta
Mai mota yai gare keta
Wani Lebura bai da ko mota
Amma bazai ji ciwo ba
Da mun kare ace sauka
Ayi ma ham don a ruda ka
In ka ki gudu a take ka
Ko yau ba za'a canja ba
A dauki diga a wurgata
Kan tsandauri a sara ta
A tara kasa a kwashe ta
Mota ba zata huta ba
Wannan magana ku duba ta
Aiki kullum kamar bauta
In lebura su ake cuta
Allah sa baza su tabe ba
Kai gidan kwano kana yanga
Ai lebura in yasa targa
Kowa ya fito ya zazzaga
Ya dade bai hangi kwanon ba
Ga katako a jejjera
Shima kwanon a tattara
A bar ka dashi ace dora
Mun san ba zaka dora ba
Dubi tara gyada kamar Dala
Kauye da cikin Kano Jalla
A daura guda kamar hula
Amma ba zata goce ba
Kaji nauyin goro huhun nan
Daya ko daukar guda sannan
Ga wagunu fankamemen nan
Lebura ba za su kasa ba
shin Lebura ko waliyyi ne
Ko jikin da ice da karfe ne
Ko dan lada suke yi ne
Ba don karfen bature ba
Icen tunba a sare shi
Ai katako a tsage shi
Wane ne zasu tsage shi
Kan lebura baiyi aiki ba
Ai lebura sai a gode ma
A tara kudi a mika ma
In ba don kai ba tun da ma
Aiki ba zai yi kirki ba
Jirgi da muke gani babba
Ba za ya zuba ya dauka ba
in lebura baiyi lodi ba
Kaya ba za shi zango ba
Ran nan da na dauki mota ta
Muka je yashi ya kama ta
Da lebura sunki tura ta
Don ni ba zata motsa ba
Jirgin ruwa in yazo kwata
Da lebura za su sa keta
Suki yin aiki su kwankwanta
Shi ba zai je ya sauke ba
Tun sanda muke zuwa kanti
Da lebura dan dako Mati
Wani mummuna gwanin datti
Amma ba'a fishi aiki ba
Ai mai amalanke jigo ne
Babban kura ko gwamna ne
Mutum ko shi minista ne
Bazai iya raina lebo ba
In za'a daka asan gari
Daukar kaya ana zari
Kaga lebura har yana tari
Amma bai fasa aiki ba
Du lebura yan kasa ne ku
Ni banda nufin in raina ku
ku amince min cikin ranku
Da nufin ba zamu saba ba
Nan zamu tsaya mu saurara
In lebura su ake kwara
Zamani zai yi wo kora
kowa ba za ya tsere ba
Kai lebura me ya dame ka
Ga Lawan ya zo ya nuna ka
Da nufin a fahimci aikinka
Amma ba don a raina ba
Kullum aka samu mai sona
Zai wo sako zuwa guna
kulkul acikin Kano tona
Lungu nake ba a titi ba
Kowa ya karanta waka ta
Sha Takwas muka tsara baitinta
Don lebura mun ka tsara ta
Amma ba don minista ba
Barka da zuwa Turakar Sha'irai (Hausa Poets Blogspot). An bude wannan Turakar ranar 23 ga Maris 2007 domin yad'a rubutattun wak'ok'in mawak'an Hausa (amma Sha'iran Najeriya, domin ba mu da masaniya game da sha'iran Jamhuriyar Nijar). Muna bukatar ta'aliki da gyara a kan abubuwan da aka gani a wannan Turakar. Allah Ya ba mu sa'a, Amin.
Monday, March 26, 2007
Gaskiya Bata Sake Gashi; M Mu'azu Hadejia
Tarihin Malam Mu'azu Hadejia, dan takaitacce ne. Ya rasu yana da Shekara 38, domin acikin 1958 ya rasu. an haifi Malam Mu'azu Hadeja a garin Hadeja, cikin 1920. shine Bahaushe na farko da ya fara rubuta Wakokinsa da rubutun Boko. Wannan kuwa ya faru ne, saboda acikin marubuta mawakan Hausa, shine wanda ya fara samun cikakken illimin boko. Dangidan Sarautar Hadejia ne, shine dalilin da wakokinsa suka fi maida himma wajen yada aqidun NPC a madadin NEPU. Kila wannanne ya janyo takaddama tsakaninsa da Malam Mudi Spikin. Bayan kammala karatunsa ne, ya fara aikin koyarwa a birnin Kano, har kuma ya rasu aikin da yake yi kenan.
Nayi ta kokarin in san ko yabar baya, amma har yanzu ban samu abin kamawa ba. Na kuma yi kokarin in san ko yana da iyali a birnin Kano, shima dai ban samu abin kamawa ba. Sai dai naji Shata na yiwa Inuwa Mai mai Kirari da "Baban Mu'azu, wanne Mu'azu? Mu azun Hadeja. Haji Inuwa Baban Yahaya" Na kuwa so hakanne don ko zan sami wasu wakokinsa da ba'a buga ba. Naji ya kan yiwa kansa kirari da "V T maineman albarka". Ga dai wata wakarsa, kafinmu kawo muku wasu.
Bin Allah shine babban bi
Kuma sai kabi wanda ya haife ka
Ka kiyaye hududulLahi suna
nan amru da nahyu suna kanka
Wallahi Uwa da Uba sune
Hanyarka ta neman albarka
In sun gajiya bisa zamani
Sai ka dau wahalarsu da karfinka
Yi fata kadda ka sabe su
Wata rana Allah zai saka
Abinda ka shuka don ka sani
Shine ka tsirowa gonarka
In hairi, hairi zaka gani
In sharri, sharri zai bi ka
Wa adi'ulLahu fadar Allah
Kuma girmama wanda ya girme ka
Duk wanda ya raina fadar Allah
Shi ya bata ya auka halaka
Duk wanda ya raina fadar Allah
Shine muka cewa Dan Iska
Har shina wa kansa kirari, sau
rara kaji taken dan iska
Dan iska sandan Kuka da sun
gumi nai ba;a yin taki
Dusar buntu ba'a ba dabba
To kaji kirarin dan iska
Dan iska naman Balbela
Ba a cin shi da na Hankaka
Kilishin Jaba sai dan iska
Ba mai ci sai ko mai shirka
Kashin Bera baya taki
Balle kayi dokin ga-na-ka
Kiwon Yimka, kiwon banza
Wata ran zai gallabi yayanka
Ajiyar Bera ajiyar wofi
Bari murna sabon dan iska
Ni zan hore ka abokina
Bari jawo dan iska ajika
In har ka yarda ya rabe ka
Ba'alin jama'a sa tsarge ka
Zai koya ma mugun hali
Watakil a kira ka da dan iska
Da 'wa kullu karinin' duba man
Ta'alimi ka samu zancenka
Kuma ka zama Shaidanil insi
Sai hirzi kai da masoyanka
Kuma ka zama Fattani domin
Allah ma bai son ka
Ka girmama Allah da Ma'aiki
Da iyaye duk da sarakinka
Wa ulul amri minkum duba
Ka kiyaye fadar mahaliccinka
In ka rainawa sarakinka
Ka rainawa mahaliccinka
Bari jin kyashin baiwar Allah
Mai kaskantawa da daukaka
Shi yadda ya so haka nan zai yi
Da yayi su sarakai, kai talaka
Da yaso zai baka duniya
Ba komai ce ba ga Rabbaka
In yaso sai kaga ka gajiya
Har ka gaza amfanin kan ka
Kai dai riki aikin alheri
Kowa kaya nasa zai dauka
Shine sarki mai fifiko
Da kasanka, wadansu ko sun fi ka
Wani na da Jaka zambar Goma
Wani bashi Kwabo balle fataka
Wani kullum mota za shi shiga
Wani kullum kaya zai dauka
Da tuwon Baure da gudun kurna
Wainar shinkafa Annafaka
Ga Alkaki duk da Alkubus
Allah ya baiwa wadansu haka
Wani sai shi tsugunna kan titi
In anci a miko mai sadaka
Wani mata nai hudu ne, kuma ga
Soraye, Benaye, Taska
shimfidu, da kujeru, Darduma
ko ina sai kamshi ke binka
Sai fenti zane iri-iri
Ga lantarki, kuma ga fanka
Wani bin Zaure shi kayi domin
Wani kasuwa zai je shi faka
Suturar wani ganye ko walki
Ba rigarma balle shi saka
Shi kance daurin Allah,
Ya daure bawa nai a daka
Wani ga sutura nan iri da iri
Ya jibge wasu cikin adaka
Kullum sai ya sake tsari
Duk wadda yaso ita za shi saka
A gidan wani guda zaka ji don
A gidan wani kuka za'a saka
Kai ba'awa Allah tilas
Shi yadda yaso haka zai baka
Da abin dariya dana mamaki
Ba sa karewa ba shakka
Wai kura ce aka ce ta tu
ba da sata don tsoron halaka
Makiyayi sai amince har
Ya kafa mata turke cikin maruka
Shi mai hakuri shike dafa du
tse ya sha romo mai albarka
Ya Allah taimaki bayinka
Duk wanda yake son manzonka
Mu'azu Hadejia nan ya tsaya
V T mai neman albarka
Nayi ta kokarin in san ko yabar baya, amma har yanzu ban samu abin kamawa ba. Na kuma yi kokarin in san ko yana da iyali a birnin Kano, shima dai ban samu abin kamawa ba. Sai dai naji Shata na yiwa Inuwa Mai mai Kirari da "Baban Mu'azu, wanne Mu'azu? Mu azun Hadeja. Haji Inuwa Baban Yahaya" Na kuwa so hakanne don ko zan sami wasu wakokinsa da ba'a buga ba. Naji ya kan yiwa kansa kirari da "V T maineman albarka". Ga dai wata wakarsa, kafinmu kawo muku wasu.
Bin Allah shine babban bi
Kuma sai kabi wanda ya haife ka
Ka kiyaye hududulLahi suna
nan amru da nahyu suna kanka
Wallahi Uwa da Uba sune
Hanyarka ta neman albarka
In sun gajiya bisa zamani
Sai ka dau wahalarsu da karfinka
Yi fata kadda ka sabe su
Wata rana Allah zai saka
Abinda ka shuka don ka sani
Shine ka tsirowa gonarka
In hairi, hairi zaka gani
In sharri, sharri zai bi ka
Wa adi'ulLahu fadar Allah
Kuma girmama wanda ya girme ka
Duk wanda ya raina fadar Allah
Shi ya bata ya auka halaka
Duk wanda ya raina fadar Allah
Shine muka cewa Dan Iska
Har shina wa kansa kirari, sau
rara kaji taken dan iska
Dan iska sandan Kuka da sun
gumi nai ba;a yin taki
Dusar buntu ba'a ba dabba
To kaji kirarin dan iska
Dan iska naman Balbela
Ba a cin shi da na Hankaka
Kilishin Jaba sai dan iska
Ba mai ci sai ko mai shirka
Kashin Bera baya taki
Balle kayi dokin ga-na-ka
Kiwon Yimka, kiwon banza
Wata ran zai gallabi yayanka
Ajiyar Bera ajiyar wofi
Bari murna sabon dan iska
Ni zan hore ka abokina
Bari jawo dan iska ajika
In har ka yarda ya rabe ka
Ba'alin jama'a sa tsarge ka
Zai koya ma mugun hali
Watakil a kira ka da dan iska
Da 'wa kullu karinin' duba man
Ta'alimi ka samu zancenka
Kuma ka zama Shaidanil insi
Sai hirzi kai da masoyanka
Kuma ka zama Fattani domin
Allah ma bai son ka
Ka girmama Allah da Ma'aiki
Da iyaye duk da sarakinka
Wa ulul amri minkum duba
Ka kiyaye fadar mahaliccinka
In ka rainawa sarakinka
Ka rainawa mahaliccinka
Bari jin kyashin baiwar Allah
Mai kaskantawa da daukaka
Shi yadda ya so haka nan zai yi
Da yayi su sarakai, kai talaka
Da yaso zai baka duniya
Ba komai ce ba ga Rabbaka
In yaso sai kaga ka gajiya
Har ka gaza amfanin kan ka
Kai dai riki aikin alheri
Kowa kaya nasa zai dauka
Shine sarki mai fifiko
Da kasanka, wadansu ko sun fi ka
Wani na da Jaka zambar Goma
Wani bashi Kwabo balle fataka
Wani kullum mota za shi shiga
Wani kullum kaya zai dauka
Da tuwon Baure da gudun kurna
Wainar shinkafa Annafaka
Ga Alkaki duk da Alkubus
Allah ya baiwa wadansu haka
Wani sai shi tsugunna kan titi
In anci a miko mai sadaka
Wani mata nai hudu ne, kuma ga
Soraye, Benaye, Taska
shimfidu, da kujeru, Darduma
ko ina sai kamshi ke binka
Sai fenti zane iri-iri
Ga lantarki, kuma ga fanka
Wani bin Zaure shi kayi domin
Wani kasuwa zai je shi faka
Suturar wani ganye ko walki
Ba rigarma balle shi saka
Shi kance daurin Allah,
Ya daure bawa nai a daka
Wani ga sutura nan iri da iri
Ya jibge wasu cikin adaka
Kullum sai ya sake tsari
Duk wadda yaso ita za shi saka
A gidan wani guda zaka ji don
A gidan wani kuka za'a saka
Kai ba'awa Allah tilas
Shi yadda yaso haka zai baka
Da abin dariya dana mamaki
Ba sa karewa ba shakka
Wai kura ce aka ce ta tu
ba da sata don tsoron halaka
Makiyayi sai amince har
Ya kafa mata turke cikin maruka
Shi mai hakuri shike dafa du
tse ya sha romo mai albarka
Ya Allah taimaki bayinka
Duk wanda yake son manzonka
Mu'azu Hadejia nan ya tsaya
V T mai neman albarka
Batijjaniya; Daga Alu Dansidi Sarkin Zazzau
Sarkin Zazzau Alu dan Sidi, shine sarkin Zazzau na farko da turawa suka fara nadawa, bayan sun ci kasar Zazzau. Ya mulki kasar Zazzau, tun daga 1903 zuwa 1922. Ya samu matsala da turawa, domin banbancin ra'ayi, wanda hakan ya sanya suka cire shi. Fasihin marubucin wakoki ne, kuma zamu kawo muku wakokinsa da dama. Da yake cikakken Batijjane ne, wato mabiyin darikar Tijjaniya, shi yasa muka fara da wakarsa ta Shehi Ahmadu Tijjani.
Na sha ruwan bege dada ni bani ji
Da gani ba, sai na zo gurin Tijjani
In na fito can zani nan in dawayo
Ni zani birnin Fas wurin Tijjani
kai mai zuwa Fas dakata mani zani nan
In yo ziyarar Ahmadu Tijjani
Shehunmu Ahmadu anka ba al-Fatihi
Budi Lima ughliqa sai Tijjani
shi anka ba al-Khatimi ga lima Sabaqa
Kuma Nasirul Haqqinmu sai Tijjani
Bil haqqi wal hadi kasan shi anka ba
Wa ila siratul mustaqim Tijjani
Wabi alihi ya Rabbi haqqa li Qadarihi
Miqdarihi ya al'Azim Tijjani
Sabkakkiya take inda Rabbil Izzati
Ita anka saukowa Wali Tijjani
Domin wadanda su kai shahada ran Badar
Don Makka duk da Madina don Tijjani
Ya Rabbi don Taurata har Injilu duk
Da Zabura har Furqanu don Tijjani
Domin safa don Marwa don Hajaral lazi
Sunansa Arfa, Rabbu don Tijjani
Domin Badiha Rabbu domin Zamzamu
Da Mukamar Ibrahimu don Tijjani
don hajaral Aswadu wanda kaba alkawal
Ran tambaya kalubale Tijjani
Na sha ruwan bege dada ni bani ji
Da gani ba, sai na zo gurin Tijjani
In na fito can zani nan in dawayo
Ni zani birnin Fas wurin Tijjani
kai mai zuwa Fas dakata mani zani nan
In yo ziyarar Ahmadu Tijjani
Shehunmu Ahmadu anka ba al-Fatihi
Budi Lima ughliqa sai Tijjani
shi anka ba al-Khatimi ga lima Sabaqa
Kuma Nasirul Haqqinmu sai Tijjani
Bil haqqi wal hadi kasan shi anka ba
Wa ila siratul mustaqim Tijjani
Wabi alihi ya Rabbi haqqa li Qadarihi
Miqdarihi ya al'Azim Tijjani
Sabkakkiya take inda Rabbil Izzati
Ita anka saukowa Wali Tijjani
Domin wadanda su kai shahada ran Badar
Don Makka duk da Madina don Tijjani
Ya Rabbi don Taurata har Injilu duk
Da Zabura har Furqanu don Tijjani
Domin safa don Marwa don Hajaral lazi
Sunansa Arfa, Rabbu don Tijjani
Domin Badiha Rabbu domin Zamzamu
Da Mukamar Ibrahimu don Tijjani
don hajaral Aswadu wanda kaba alkawal
Ran tambaya kalubale Tijjani
Yabon Allah; Daga Wazirin Gwandu Umaru Nasarawa
Malam Umaru Nasarawa dai ba boyayye bane, domin a zamaninsa kowa yasan irin gudunmawar da ya bayar wajen raya adabin Hausa ta fannin wakoki. Ya rubuta wakoki da dama, wanda insha Allah zamu kawo su. Amma ga wanda bai san shi ba, to shine mahaifin tsohon gwamnan jihar Kaduna a zamanin soja, wato; Abubakar Dangiwa Umar. Wannan wakar dai sunanta Yabon Allah. Ga kuma yadda take.
Yabo gun Jalla daidai na
Garan kuma wajibina na
Na jin kai nai da yan nuna
Garan ya amshi roko na
Tutur! Na zam shukura
Ga sarkin nan da naiyi kira
Da sunayensa naiyi bara
Zuwa ga biyan bukatuna
Da farko duk abinda ni kai
Da fari dai salati ni kai
Ga Annabi duk abinda ni kai
Da shi nika fara wake na
Sahabbai nai da Alu duka
Gama sun taimake shi duka
Ina ko daulaminsu duka
Da aikina da horo na
Abokina taho ka jiya
Ina rokonka kar ka kiya
Ka samu guri guda ka tsaya
Idan ka amshi roko na
Tsaya gun Jalla dai ka fake
Da imaninka kar ka fake
Ka bishi ka togi inda shike
Mu dogara nan masoyi na
Biyar Allahu ta wajaba
Sana'a ta mafi riba
Tutur! Batu na bai da tambaba
Tsaya in baka shaiduna
Ruwa bana sun ka kai ga wuya
Har na rasa inda zani tsaya
Balle juyi, balle tafiya
Ganin am fara zunde na
Rawata an suke ta duka
Gama an dungushe ni haka
Ganin ta kai ni ag ga haka
Dada nir raina wayo na
Dada sai nik kirai Ahadun
Guda, wannan da as-Samadun
Da nim matsu ni nufai da gudun
Gama shi am maceci na
Da nat tasamma inda shike
Cikin huruminsa ni iske
Aminci nan gare shi shike
Dada nid debe tsoro na
Da dai nig gane Sarkina
Da ba a bida garai shi hana
Ga kofofinsa niz zauna
Dada ni buda baki na
Dana roka da ya bani
Dani dauko ga Qur'ani
Ashe ma anyi min izini
In tai in kara koke na
Da najji hakanga nish shirya
Bido Zababbiya ka jiya
Cikinta kana ganin hanya
Da zam bi ta zam mahorina
Taho sa hankali ka kula
Kabar gajiya, kabar shagala
Tutur! mu tsare yabon Allah
Cikin zarafin zamowa na
La'in mun zo ga Qur'ani
Bisa horonka don ka sani
Ina tsaya ran dare da wuni
Ina shukuri da Bege na
Tabara yabonka jalli na
Gareni abin tsimina na
Sahihin maganina na
Da shi nika warke rauni na
Da lotto duk yabonka ni kai
Dana matsu duk kiranka ni kai
Bida bisa agajinka ni kai
Ka warwatse aduwai na
Kana nan inda nis sanka
Tutur! Ka amsa sunanka
Mujibun kow kireka haka
Kana ji baka yin kwana
Da kyau nas soka nab bika
Da kowa baiyi ma shirka
Ilahul Arshi baicinka
Wane ka biyan bukatu na
Ina wani banda kai Rabbu
Da ba a bida shice babu
Ina wani mai kade aibu
Gareni shi karbi rokona
Ku kawo wanda kun ka sani
Da komi za ayi shi sani
Da an roke shi bashi hani
Fada mini shi, ka ban suna
Kace Allahu sarki na
Wani nai dug gazajje na
Abi nai duk kadan dai na
Ina shika jure roko na
Bida ga waninka mik kai ni
Dadai duk wanda yas sanni
Cikin ni'imarka yag ganni
Kana da kula da raino na
Ka cetan kar a kaushe ni
Ga duk hanyar da shaidani
Rajimi kar shi rudeni
Shi hau kan yan dibaru na
Ta'ala kai da ka hora
Mu zan koko mu zan ta bara
Gareka mu zam bidan Nasara
Dashi ni kayo umurni na
Ta'ala Jallah mai iko
Ina nan dai ina dako
Ina ta kiranka kullum ko
Ina kuma kara kwazo na
Da farin na kiraye ka
Da sauri nig ga jinkanka
Ina gode ma baiwarka
Dashi ni ka rera wake na
Ta'ala bani fasa bara
Tutur! Ni ke duk cikin zakara
Ginarka gareka ga sutura
Wadarka, ka kore bakakina
Bukatu na matso ni su kai
Dana matsu ko kiranka ni kai
Tutur! Sonka bani ni kai
Ina nika kama bakina
Bukatu gasu sun gilma
Ilahi gani na soma
Kiran nan wanda nif fara
Da farko nigga dace na
Da farin gafara zambu
Nike roko wurin Rabbu
Da aikina nayin aibu
Da son raina da wayo na
Ka hori ga zuciya ta tsaya
Bida ga waninka duk ta kiya
Balle inyo haraminya
Garai in banna baki na
Isheni ga duk abinda nik kai
Biya min duk bukin da ni kai
Gama kasan nufar da ni kai
Ya Rabbi ka amshi rokona
Yabo gun Jalla daidai na
Garan kuma wajibina na
Na jin kai nai da yan nuna
Garan ya amshi roko na
Tutur! Na zam shukura
Ga sarkin nan da naiyi kira
Da sunayensa naiyi bara
Zuwa ga biyan bukatuna
Da farko duk abinda ni kai
Da fari dai salati ni kai
Ga Annabi duk abinda ni kai
Da shi nika fara wake na
Sahabbai nai da Alu duka
Gama sun taimake shi duka
Ina ko daulaminsu duka
Da aikina da horo na
Abokina taho ka jiya
Ina rokonka kar ka kiya
Ka samu guri guda ka tsaya
Idan ka amshi roko na
Tsaya gun Jalla dai ka fake
Da imaninka kar ka fake
Ka bishi ka togi inda shike
Mu dogara nan masoyi na
Biyar Allahu ta wajaba
Sana'a ta mafi riba
Tutur! Batu na bai da tambaba
Tsaya in baka shaiduna
Ruwa bana sun ka kai ga wuya
Har na rasa inda zani tsaya
Balle juyi, balle tafiya
Ganin am fara zunde na
Rawata an suke ta duka
Gama an dungushe ni haka
Ganin ta kai ni ag ga haka
Dada nir raina wayo na
Dada sai nik kirai Ahadun
Guda, wannan da as-Samadun
Da nim matsu ni nufai da gudun
Gama shi am maceci na
Da nat tasamma inda shike
Cikin huruminsa ni iske
Aminci nan gare shi shike
Dada nid debe tsoro na
Da dai nig gane Sarkina
Da ba a bida garai shi hana
Ga kofofinsa niz zauna
Dada ni buda baki na
Dana roka da ya bani
Dani dauko ga Qur'ani
Ashe ma anyi min izini
In tai in kara koke na
Da najji hakanga nish shirya
Bido Zababbiya ka jiya
Cikinta kana ganin hanya
Da zam bi ta zam mahorina
Taho sa hankali ka kula
Kabar gajiya, kabar shagala
Tutur! mu tsare yabon Allah
Cikin zarafin zamowa na
La'in mun zo ga Qur'ani
Bisa horonka don ka sani
Ina tsaya ran dare da wuni
Ina shukuri da Bege na
Tabara yabonka jalli na
Gareni abin tsimina na
Sahihin maganina na
Da shi nika warke rauni na
Da lotto duk yabonka ni kai
Dana matsu duk kiranka ni kai
Bida bisa agajinka ni kai
Ka warwatse aduwai na
Kana nan inda nis sanka
Tutur! Ka amsa sunanka
Mujibun kow kireka haka
Kana ji baka yin kwana
Da kyau nas soka nab bika
Da kowa baiyi ma shirka
Ilahul Arshi baicinka
Wane ka biyan bukatu na
Ina wani banda kai Rabbu
Da ba a bida shice babu
Ina wani mai kade aibu
Gareni shi karbi rokona
Ku kawo wanda kun ka sani
Da komi za ayi shi sani
Da an roke shi bashi hani
Fada mini shi, ka ban suna
Kace Allahu sarki na
Wani nai dug gazajje na
Abi nai duk kadan dai na
Ina shika jure roko na
Bida ga waninka mik kai ni
Dadai duk wanda yas sanni
Cikin ni'imarka yag ganni
Kana da kula da raino na
Ka cetan kar a kaushe ni
Ga duk hanyar da shaidani
Rajimi kar shi rudeni
Shi hau kan yan dibaru na
Ta'ala kai da ka hora
Mu zan koko mu zan ta bara
Gareka mu zam bidan Nasara
Dashi ni kayo umurni na
Ta'ala Jallah mai iko
Ina nan dai ina dako
Ina ta kiranka kullum ko
Ina kuma kara kwazo na
Da farin na kiraye ka
Da sauri nig ga jinkanka
Ina gode ma baiwarka
Dashi ni ka rera wake na
Ta'ala bani fasa bara
Tutur! Ni ke duk cikin zakara
Ginarka gareka ga sutura
Wadarka, ka kore bakakina
Bukatu na matso ni su kai
Dana matsu ko kiranka ni kai
Tutur! Sonka bani ni kai
Ina nika kama bakina
Bukatu gasu sun gilma
Ilahi gani na soma
Kiran nan wanda nif fara
Da farko nigga dace na
Da farin gafara zambu
Nike roko wurin Rabbu
Da aikina nayin aibu
Da son raina da wayo na
Ka hori ga zuciya ta tsaya
Bida ga waninka duk ta kiya
Balle inyo haraminya
Garai in banna baki na
Isheni ga duk abinda nik kai
Biya min duk bukin da ni kai
Gama kasan nufar da ni kai
Ya Rabbi ka amshi rokona
Subscribe to:
Posts (Atom)