Sarkin Zazzau Aliyu Dan Sidi shahararren Sarkin ne a Arewacin Nigeria, yayi fice saboda irin fasaharsa da illiminsa, shi kuma ne sarkin Zazzau na farko da Turawa suka nada. Turawanne kuma suka sauke shi, bayan sun samu sabanin ra'ayi akan wasu sauye-sauyen zamani. Ya zama sarki yana da Shekara Sitiin da hudu (64), yayi sarautar Zazzau daga 1903-1920 . Jikan Sarkin Zazzau Musa ne, Bamalli. Wani abin sha'awa gameda da tarihinsa shine, shi dai bai taso a gidan Sarautar Zazzau ba, ya taso a gidan malanta ne, a hannun malaminsa Limamin Durum wato malam Abubakar. Ya taba samun sabani da Sarkin Zazzau Kwasau (Mai kogin Jini dan Sambo), wanda hakan ya sanya bar Kasar Zazzau, ya shiga yawace-yawace, inda har ya Zauna a kasar Kwantagora a zamanin Sarkin Kwantagora Ibrahim Nagwamatse. Ya wallafi wakoki da dama, cikinsu kuwa akwai Tabarkoko, Saudul Kulubi, Wakar Diga da kuma wannan waka ta Birnin Kano.
Ance wannan waka yayi tane, yayi wata Dabar bankwana da Sarakunan Arewacin Nijeriya suka shiryawa Gwamna Arewacin na Zamanin Turawa wato sir Hugh Clifford, a Birnin na Kano acikin shekara 1914. A zamaninsa akan masa kirari da "Aliyu na Awwa mai iya Sarki" . Sarkin Zazzau Aliyu dan Sidi Batijjane ne na kwarai, domin mun kawo muku wakarsa da yayiwa Shehun Darikar ta Tijjaniya wato Shehu Ahmad Tijjani, ga mai so sai ya duba cikin kudayen Turaka wato Archives. Ga dai Malam Aliyu dan Sidi a Birnin Kano.
Muna gode Allah da yayi nufi
Yasa muka taru a kofar Kano
Muna yin Salati bisa ga Muhammad
Dalilinsa anka yi mu akayi Kano
Mu kara salati bisa ga sahabbai
Mu sami dalilinsu komi anu
Zama hali ma nahnu shi muka zance
Da niy yi shiri zani birnin Kano
Diya min Muharram ga ran Lahadi
Na hau bisa jirgi zuwa na Kano
Ga Chalawa ni kwana guda muka tashi
Muna gaisuwa da dawakan Kano
Dawaki na baki kaza yan gari
Fa har muka sadu da Sarkin Kano
Da fa muka gaisa ya juya na bishi
Dada har ya kaini masauki Kano
Ina gaida masu zuwa daga nesa
Da shaihu na Kukawa ga shi Kano
Da Mahoni Laraba Gaidan Kano
Kaza Lamido Adamawa a birnin Kano
Katagum, Hadejia, kaza duk da Gombe
Misau Jama'are a birnin Kano
Da Zazzau da Bauchi, kaza Katsina
Da Daura, Gumel gasu birnin Kano
Kazaure da kau Sakkwato har da Gwandu
Kabawa da Argungu birnin Kano
Mutan Gwadabawa da Kwanni da Yabo
Gamuwa da Anka a birnin Kano
Da Meri da Augi mutanen Yamma
Mutan Jega ga su a birnin Kano
Mutan Wukari, mutanen Ibi
Da Loko da Lokoja a birnin Kano
Da Yawuri har Kwantagora Rijau
Mutan Wushishi da Bussa a Birnin Kano
Kushurki da Kunguna har Kuriga
da Gwari na Waki a taron Kano
Mutanen Maginga mtan Kanbuwa
Na Sulame gasu a birnin Kano
Illori, Nufawa, Lafai, Agaye
Fa hatta Abuja a birnin Kano
Fa har Tunkiya gata ga Damisa
Mashayansu dai sunyi kiwo Kano
Kutawa mutanen Kafi, Lafiya
Da jam'an ta Baroro a birnin Kano
Da Mahmudu Ningi da Sarkin Bura
Da Sarkin na Bassa a birnin Kano
Ina gaida Sarkin Kano Yayi Aiki
da anka yi taro garinsa Kano
Gidaje na sabka dada har liyafa
Da taryan sarakai su sabka Kano
Da sabkan farare da sabkan bakake
da birni da kauye a birnin Kano
dalili gareni in san yayi aiki
Zama nayi ko da nika je Kano
Da shi da ya sabkar da su masu sabka
Ta'ala shi bamu sawaba Kano
Fa naje da yare iri da yawa
Da busa da ganga a taron Kano
Fitawa da doki dako Feluwa
Da sayi suna sukuwa nan Kano
Mutane da doki da niz zo dasu
jimillansu hamsa zuwana Kano
Kurama, Katab har da Cawai duka
Fa duk sunyi wasa a taron Kano
Da Jaba da Gwari mutan Rumaya
Kadara fa na kai su taron Kano
Ga babban suka na dawakan saraki
Na Zazzau fa sun ka ci taron Kano
Da anka yi wasa fage ya hadu
Muhudanmu sun yi ado nan Kano
Ka rarra, ka Kabra, ku san tumkiya
Bata iya kabra ba Kano
Da tauri da tsauri idan anka goga
Guda sai shi yanke guda a Kano
Ba'an gwada karfe ba, sai inda karfe
Duwatsu fashewa su kai a Kano
Ka zaga Kano har kasan dan Kano
Na birnin Kano wanda yasan Kano
Ka kau tambaye shi tsakani da Allah
Ya bayyana maka taron Kano
Na yawata Kano gani ga dan Kano
Dada har nasan anguwa a Kano
akwai anguwan madawkin Kano
Da sunanta Yola a birnin Kano
Daneji, da Soron dinki akwai su
akwai Lungunawa da Sheshe Kano
Da Marmara duk unguwa ce duka
da Kunduke Kwankwaso duk a Kano
Akwai Wudilawa akwai Na'ibawa
Da Ibadi Fasa-keya a birnin Kano.
Caranci, Gudundi, akkwai Jarkasa
Makankari, Garko duk a Kano
Kusura, Kudancin Kano da Wazirci
Da Siradi akwai ta Kano
Karofi na Wanka da Shuni akwaisu
Madatai da Daushi akwai su Kano
Karofi na Sudawa, Zangon Ciki
Da Dandago, Diso akwai su Kano
Akwai unguwar Durunmin Kaigama
Da Bulbulas, Guntu akwai su Kano
Da Yalwa da Dala, Madaboo duka
Suna nan Arewa da Kurmin Kano
Akwai wata ko unguwa Masaka
Da Sarari da Sagagi Birnin Kano
Awai unguwa Waitaka a Kano
Akwai Durumin Dakata min Kano
Mahanga, Kutumbawa duk unguwa ce
Da Damtsenka Tsage a Birnin Kano
Akwai Cediya ta Kuda unguwa ce
Akwai Kalaman Dusu duk a Kano
Da Lallokin Lemu, da kau Makwarari
Makwalla fa duk unguwa ce Kano
Dabinon Awansu da Mandawari
Da Alfindiki Kwalwa duk a Kano
Tsaya in gajarta guda don kau yawaita
In kawo wurinta da niyyi Kano
Fa har muka kare naje Nasarawa
Garin makarantan su Sambon Kano
Akwai makaranta karatun Bature
Acan Nasarawa ta kofar Kano
akwai yara masu Karatu na allo
Akwai masallaci ginanne Kano
AKwai Makaranta ta al Kur'ani
Da litattafanmu a birnin Kano
Akwai wani dakin zaman masu ciwo
Akwai matsarinsu a kofan Kano
Masaka, madunka, da mai Sassaka
Gidansu guda makarantan Kano
Makera, Badukai da masu kudi
Cikin makaranta ta kofar Kano
Cikin shekara goma sha dai ga daula
Aliyu binu Sidi zuwanshi Kano
Ya wake ta yan baya domin su ji
Su san wakacin tafiyanshi Kano.
1 comment:
[url=http://firgonbares.net/][img]http://firgonbares.net/img-add/euro2.jpg[/img][/url]
[b]coreldraw 12 program access, [url=http://firgonbares.net/]torrent nero 9 fully cracked[/url]
[url=http://firgonbares.net/][/url] to sell software product where to buy pirated software
microsoft office pro 2003 complete download [url=http://firgonbares.net/]kaspersky webscanner[/url] microsoft software online
[url=http://firgonbares.net/]software microsoft word[/url] microsoft windows mobile software
[url=http://firgonbares.net/]microsoft office 2003 professional training video[/url] software store pictures
purchase oem software [url=http://firgonbares.net/]9 Advanced Mac Retail[/b]
Post a Comment