Ya Allahu Rabbana taimakemu
Mu gargadi yan'uwa ga auren kazama
Auren tsohuwa hasara ga yaro
Gwammaci tsohuwa ga auren kazama
In baka san tane ba kau tambaye ni
In Allah ya yarda kasan kazama
Mummunan halin kazama na fari
Bata fece majina sai da dama
Mai son cin tuwonta sai yaci gashi
Susan hagu na tofi da dama
Hanci majina, idanunta kwantsa
Dattsa ya dadawa bakinta girma
Sai kaga tai gajal da suma da dauda
Ga bauli a kwance, tashinta fama
Bamai son kitso ba, ta kasa aski
Taba ya dafe hakoran kazama
Gude ba kokari ba ga kasa girki
Ga hadama a zuci koshinki fama
Ran girki ba a koshi da jibi
Shi naman miji ki cinye a tsama
In taga ka fito kamar zaka zaure
Sai sababi ya tashi don bata girma
Ka ji "Bar neman fita ina tsame nama
Yau dai kai rabon a zage ka kai ma"
Tunda ka sai kitse ya narke a girki
In aka zo rabo, rabawansa fama.
Wanda ka bashi kankane sai ya raina
Kowa so yake ya karba da dama
Ran nan ma ka sai kashi, na ki zagi
Gun kwarin gidanka mai yada girma
In ta ce dani kazama in rama
Wanda ya san Kumatu yasan kazama
In tace ina da ci ne in rama
"Domin ga Tasallah koshinta fama"
Kwana goma jere, haifanta goma
Ba taran miji ga haifan kazama
Ita ko Bante ta ketara sai ta haifu
In ka san kudi su kare a suna
Ya Allah dadawa matanmu tsabta
Kada Allah ka bamu mata kazama
Tunda mijin kazamiya zai ji kunya
Can Aljanna babu mata kazama.
Barka da zuwa Turakar Sha'irai (Hausa Poets Blogspot). An bude wannan Turakar ranar 23 ga Maris 2007 domin yad'a rubutattun wak'ok'in mawak'an Hausa (amma Sha'iran Najeriya, domin ba mu da masaniya game da sha'iran Jamhuriyar Nijar). Muna bukatar ta'aliki da gyara a kan abubuwan da aka gani a wannan Turakar. Allah Ya ba mu sa'a, Amin.
Tuesday, March 27, 2007
Wakar Keke; Ta [Dr] Aliyu Namangi
Muna shukura ga Rabbal alamina
Da alherin da yai mana ba kadan ba
Muna murna da mulkin ingilishi
Zuwan da sukai kasarmu ba tai tsiya ba
Zama zamaninsu ne aka zo da Faifa
kudi ba masu nauyaya aljihu ba
Dada zarafinsu ne aka zo da jirgi
Kaje Makka ba da tashin Hankali ba
Sa'annan gasu Babur, ga su Mota
Da farko da can bamu san da su ba
Izan tafiya ta faru ka nemi mota
Izan jirgi ba kui daidai da shi ba
Izan kuwa babu Jirgi babu mota
Ka je da kafarka ba keken tsiya ba
Banni da Basukar Ho! Dan jidali
shakiyyi ba abin Babba ya hau ba
A Dan-Mahawayi nih Hau sai ya barni
Tudun-Yakaji ban kawo gari ba
Ya bar ni da jin jiki da zama a turba
Da dai ko juma'a ba a je dani ba
Kudi tirmis! Na bashi Sule-da-Sisi
keke bai mani rangwame ko dari ba
Na ce masa "Basukur rika sawwakewa"
Yace "Malam hala ba ka sanni ne ba"
"Ina da tsiya biyar farkonsu fanca
Na kau buga bindiga ba mai wuta ba"
In babbake zuciya, in tafi da sawu
Cikin daji kamar ba'a je dani ba
Muna tafiya kuma na fizge kaina
Mu fada kwazazzabo ni ban kula ba
Ina da ciki ana ce mai Kurumbo
Karambanin hawa baka saya ba
Hanjina kaca mai kama riga
In fizgo mai hawa ni ban kula ba
Tsiya na can mu je kan kadarko
Madaidaici in ce ba zamu hau ba
In hau bisa kafadar bari in zauna
Kamar mahayin dadai bai hauni shi ba
Su kai kadda da Sale akan kadarko
Sai yace "Haba Sale bazan yadda kai ba"
Dadai suka wantsala hakan kan ya kwace
Ashe ba Sale ne a cikin ruwa ba?
Ya bishi ya bangaje ya buge yana ce
"Azo a gani idan ban yada kai ba"
Malam Sale saida ya tube riga
Yasa kaga Sale har bai sha ruwa ba
ya tashi ya hau tudu keke ya bi shi
Da rigar Sale keke bai sako ba
Su malam Sanda duk suka tar ma keke
Da ban magana yace ba zai saka ba
Ya ma rantse da jirgi har da mota
Ba zashi sako ba in ba'a sa wuka ba
Malam Sanda wai sun shirya da Keke
Wai yana kaunarsa ba domin tsiya ba
Yace "Haba malami kamarka
Bazan iya yadda babban malami ba"
Izan dai zaka hauni ka tara riga
Da wando ba ka hau ni hawan isa ba
Ya tashi hawa bai tattara ba
Ya fizgo malamin ba a jinjima ba
Ya yasai nan da nan a tsakar gidansa
Cikin matansa tun ba a kai dabe ba
Yace "Bari nai kure yashe ka malam
Dama ban kai ka bakin kasuwa ba
Bana son na yada mutum na kirki
Izan ba inda za ai dariya ba
Da motsa kararrawarka da kama burki
Ba zasu hana ni in jefar da kai ba
Yace masa "Bana kara hawanka keke"
Yace masa "ko adankiya ban kula ba"
Hawan da rashin hawan a gareni dai ne
Ban ga abinda zai cutar dani ba
Kamar tafiya ta sauri ko ta fizge
Baka je inda kaso nan da nan ba
Izan kazo ka hau ni ka bani iska
Na sha, ba inda ba zan je dakai ba
Ashe ba mai hawa keke ya more
Izan ba wanda ya iya zanzaro ba.
Da alherin da yai mana ba kadan ba
Muna murna da mulkin ingilishi
Zuwan da sukai kasarmu ba tai tsiya ba
Zama zamaninsu ne aka zo da Faifa
kudi ba masu nauyaya aljihu ba
Dada zarafinsu ne aka zo da jirgi
Kaje Makka ba da tashin Hankali ba
Sa'annan gasu Babur, ga su Mota
Da farko da can bamu san da su ba
Izan tafiya ta faru ka nemi mota
Izan jirgi ba kui daidai da shi ba
Izan kuwa babu Jirgi babu mota
Ka je da kafarka ba keken tsiya ba
Banni da Basukar Ho! Dan jidali
shakiyyi ba abin Babba ya hau ba
A Dan-Mahawayi nih Hau sai ya barni
Tudun-Yakaji ban kawo gari ba
Ya bar ni da jin jiki da zama a turba
Da dai ko juma'a ba a je dani ba
Kudi tirmis! Na bashi Sule-da-Sisi
keke bai mani rangwame ko dari ba
Na ce masa "Basukur rika sawwakewa"
Yace "Malam hala ba ka sanni ne ba"
"Ina da tsiya biyar farkonsu fanca
Na kau buga bindiga ba mai wuta ba"
In babbake zuciya, in tafi da sawu
Cikin daji kamar ba'a je dani ba
Muna tafiya kuma na fizge kaina
Mu fada kwazazzabo ni ban kula ba
Ina da ciki ana ce mai Kurumbo
Karambanin hawa baka saya ba
Hanjina kaca mai kama riga
In fizgo mai hawa ni ban kula ba
Tsiya na can mu je kan kadarko
Madaidaici in ce ba zamu hau ba
In hau bisa kafadar bari in zauna
Kamar mahayin dadai bai hauni shi ba
Su kai kadda da Sale akan kadarko
Sai yace "Haba Sale bazan yadda kai ba"
Dadai suka wantsala hakan kan ya kwace
Ashe ba Sale ne a cikin ruwa ba?
Ya bishi ya bangaje ya buge yana ce
"Azo a gani idan ban yada kai ba"
Malam Sale saida ya tube riga
Yasa kaga Sale har bai sha ruwa ba
ya tashi ya hau tudu keke ya bi shi
Da rigar Sale keke bai sako ba
Su malam Sanda duk suka tar ma keke
Da ban magana yace ba zai saka ba
Ya ma rantse da jirgi har da mota
Ba zashi sako ba in ba'a sa wuka ba
Malam Sanda wai sun shirya da Keke
Wai yana kaunarsa ba domin tsiya ba
Yace "Haba malami kamarka
Bazan iya yadda babban malami ba"
Izan dai zaka hauni ka tara riga
Da wando ba ka hau ni hawan isa ba
Ya tashi hawa bai tattara ba
Ya fizgo malamin ba a jinjima ba
Ya yasai nan da nan a tsakar gidansa
Cikin matansa tun ba a kai dabe ba
Yace "Bari nai kure yashe ka malam
Dama ban kai ka bakin kasuwa ba
Bana son na yada mutum na kirki
Izan ba inda za ai dariya ba
Da motsa kararrawarka da kama burki
Ba zasu hana ni in jefar da kai ba
Yace masa "Bana kara hawanka keke"
Yace masa "ko adankiya ban kula ba"
Hawan da rashin hawan a gareni dai ne
Ban ga abinda zai cutar dani ba
Kamar tafiya ta sauri ko ta fizge
Baka je inda kaso nan da nan ba
Izan kazo ka hau ni ka bani iska
Na sha, ba inda ba zan je dakai ba
Ashe ba mai hawa keke ya more
Izan ba wanda ya iya zanzaro ba.
Subscribe to:
Posts (Atom)