Acikin wasu Kundayen adana rubutattun wakoki dake National Archives Kaduna, an tsinci wani File mai No O/AR 2, wanda ke dauke da wata wakar ajami, wadda F Edgar ya samo a shekarun farko na karni na 20. Acikin File na 20 ne wannan waka take, wadda aka hakkake an kattama shi acikin shekara 1911. Bisa ga dukkan alamu Edgar ne ya kwafi wakar da hannunsa, cikin wata takarda falle daya, wanda aka tabbatar da cewa, zai wuya a samu inda ya kwafo wakar. Amma duk da haka ya rubuta sunan wanda ya kwafa, ko kuma ya wallafi wakar wanda ya kira da Sandan Baba. Sai dai kuma bai bayyana kowaye shi wannan Sandan Baba ba, ko kuma mutumin ina ne shi, ko a ina ya ganshi, kwafa yayi daga gurinsa, ko kuma reara masa yayi, shi kuma ya rubuta, Allahu a'alamu? Sai dai a wani File mai no 61, wanda aka sanyawa kwanan wata kamar haka; 1909, an rubuta wata waka maisuna "Wakar Yabo/Bege" , daga Sandan Baba mutumin Sakkwato, inda aka bayyana cewa, Sandan Baba ya rerawa wani malami wai shi Malam Bako wakar, shi kuma ya rubuta ta. Wannan ya dan bada haske na gano cewa, Sandan Baba dai ya reara wakar ne, inda Malam Bako da Frank Edgar suka kwafe ta, ko kuma shi malam Bako ya kwafa, shi kuma Edgar ya samu a wurinsa. Bisa ga dukkan alamu, Edgar bai san Sandan Baba ba, amma yana da masaniya akan Malam Bako.
Wakar dai ta kunshi abubuwa uku, akwai Zambo, Habaici da kuma Yabo. Badai takamaiman kowa akewa wadannan abubuwa, ko duk mutum daya ne, ko kuma mutane da dama. Amma dai kusan sanin kan kowane cewa, abune ba sabo ba ga Yanmatan kasar Hausa, su kirkiri waka don Yabo ko Fallasa, da sigar Gada. Don haka tabbas wakar dai ta Yanmata ce, da suka rera, saboda wasu dalilai da dama.
Ga dai wakar yadda take:
Shiririta ararrata
Kare gadon gida yayyo
Bani bukinka da shara
Sai ranar zuwa aiki in baka taro ka futassan
Farin wake na banza ne
Ko an matsu ba'a gumbatai
Bambeni ka gara gije
Kurche gidansu tag gado
Domin Biri a janye kadarko
Bika da shirin tuma yazzo
Kwa bace ni in rama
Don ba shi ka chi san ba
Anini mai kammarSisi
Da tsakka gashi fudajje
Kwabo kau mai kamar Fataka
Da tsakka gashi fudajje
Mai-Gwanja gaton shigifa
Na mallam-dan-majidadi
Mai kyautar dala da dala
Na malam-dan-majidadi
Diyal laka ta banza ta
Don bata zuwa tayo wanka
Diyal Danko ta banza ta
Don bata fita cikin rana
Zancen daka sai mata da miji
Hanyar bisa dole sai tsuntsu
Garar kasa maganin ajiya
Zago mai fanfatse kaya
Bani zuwa ga yanboko
Gara nazo ga yan madara
Dan boko sai hawan doki
Amma ba kudin sati
Mai rai duk masami ne
Zabarma akwai bidar kuddi
Limamin gidan Joji dogo ketare ka ciro
Har ya manta wando nai
Kuku da Boyi sun rantse
Sai sun dauki yar gwari
Tulu dai ka shan yawo
Randa na nan cikin daki
Mai rai duk shi dau himma
Ayi ta batun bidar kuddi
Dan kawo rinin Allah
Madilla masoyina
Namijin kuti mai kafar kwabi
Har ya raina matatai
Randa na cikin daki
Allah shika bata ruwa ta sha
Tukuruwa mai kaya boye
Gawo da kayarka ka girma
Tataka sai aba doki
Nama sai aba Zaki
Tafarnuwa ta faye yaji
Amma ga maganin sanyi
Dabino farkon ka Baure ne
Acan karshe kake zaki
Anini dan mutan Lokoja
Bana yazo kasar Hausa
Kwa doke ni in rama
Don bashi ka tufasan ba.
Ga mai son jin cikakken bayanin wakar sai ya nemi makalar da Grahm Furniss da Yunusa Ibrahim suka gabatar, mai taken; An Early Twentieth Century Song: "Wakar Kuyangin Sakkwato" A mujallar Harsunan Nijeriya, xvi, 1991/92. CSNL Bayero University Kano. Nigeria.
No comments:
Post a Comment