Tuesday, April 10, 2007

Wakar Kidayar Mutanen Nijeriya 1973; Daga Hajiya Yar Shehu

An haifi Hajiya Yar Shehu a shekara 1937, a garin Dambatta. Ta halarci makarantar Yanmata dake lardin Sakkwato, bayan ta kammala karatun addini a gida. Ta fara aiki a ma'aikatar lafiya ta Kano a 1953, bayan ta koyar a makarantun Firamare. Daga bisani ta koma kamfanin jiragen sama na Kano, a matsayin mai bada hanyar Tarho, inda ta zama jami'ar kula da ma'aikata na ma'aikatar. Haka kuma member ce a shahararriyar kungiyar mawakan nan, wato Hikima Kulob. Ta dai wallafi wakoki da dama, domin fadakarwa, zaburarwa, illimantarwa, wa'azantarwa, da sauransu, wakokinta sun hada da "Waka da Bayani", Wakar Kidaya, Wakar Zamani dss. wadanda insha Allahu zamu kawo muku su, da dai-dai. Ta rubuta wannan waka, domin fadakar da mutane akan kidayar jama'a wato Census da akayi a 1973. Ga dai Wakar;

BismilLah na fara da sunan Rabbana
Allah Ta'ala Jallah Sarkin gaskiya

Kai ne Sami'un Basiru, Mai ji, Mai gani
Ka tsare mu sharrin, masu sharrin duniya

Domin Muhammadu shugaban duka duniya
Har lahira ma, in ka bashi gaba daya

Don Annabawa har Sahabbai Mursalai
Har dukka dangogin Rasulu abin biya

Kayi taimako agareni kai min kangiya
Kai ne katanga wadda bata zagaya

To zanyi tsari dan Kidaya ne yankuna
Ta Arewa harma duk kasarmu gaba daya

Allah Hakimu hikimarka da ta isa
Kasa mu gane don mu bayyana gaskiya

Don kada mu fada ayyukan shibcin gizo
Da ya kasa dauka, sai ya karo kungiya

Ga gargadina gun sarakai malamai
Lalle ku dage don ku kange areriya

Komai idanu bakuna har kunnuwa
Komai ya baci wuyanku ne zai rataya

Ko Shehu Fodiye ku yaba tuta tasa
Har ma amanar dogare gaba daya

Domin hakan nan sai ku tashi ku taimaka
Akan kidayar na jihannunmu gaba daya

Don kadda a kwaso kyankyaso da su kwarkwata
a zazzage mana nan Arewa mu sha wuya

Allah jikansu na baya manya sun wuce
Giwa saka kawo ban Arewa gaba daya

Dan kadda mu ji ta kururuwa rashe idon kuma
Har ma da makirci na mai kin gaskiya

Kuma kadda jahilci ya sa sarkacen tasa
Ya ja kafa kuma har wuyanmu gaba daya

In anka zo kirga ya tabbata mun zaka
Mun bayyana musu dangunanmu gaba daya

Maza da mata har da yara kankana
Har jinjirai ma wanda sun kwana daya

Kuma har da tsofaffi da basu fita waje
Don Allah duk a fade su kar a rage daya

Domin barin wani, baya ba wani taimako
An fidda dashi acikin mutan Nijeriya

Shi bai ga tsuntsu bai ga tarko ya bace
Sai yai nadama nan cikin Nijeriya

Allah tsare mu da yin hakan, ya yan'uwa
Kuma maganin wannan a bayyana gaskiya

Kuyi tir da masu batun na banza kun jiyya
Makiya jiharmu, munafukanta Arewaci Nijeriya

Har ma suna cewa haraj za'a sa
Domin su wargazar da shirin ta areriya

Kuma don a danne tattalinmu na arziki
Har ma a danne komi nan arewa mu sha wuya

Ba'a kidaya kan haraji kun sani
Yara da mata ba'a sa musu kun jiya

Haka ma a zozzowa da tsofaffi duka
Suma haraji ba'a sa musu kun jiya

Wannan kidaya dai nufinta daban yake
Nan dai asan jimlar mutan Nijeriya

Kuma don a san adadin mutanen jihhunan
Jihar da tafi yawa cikin Nijeriya

In an rabo ita zata samu mafi yawa
Ninkin ba ninkin za'a bata kunjiya

Kan duk ku da ayyukan gona duka
Kuma asibitoci makarantu kun jiya

To zasu samu rabo mafi girma duka
To kadda mu cuci jiharmu nan ta arewiya

Duk wanda ycce ma haraji za'a sa
Ce mai haraji arziki ne ka jiya

Mara lafiya da mahaukata basa biya
ashe haraji lafiya ne kun jiya

Sauki gareshi gun manomi kun jiya
Zakkar abinda ya aikata shi ke biya

Yan kasuwa ma sau guda ne shekara
Ma'aikata ne ba iyaka kun jiya

Dukkan wata kullum akan diba ake
Sisi ake diba a kowace fam Daya

Kai malami har malama kuyi anniya
Ku bada sunan yan uwanku gaba daya

Yaya da jikoki da dangi ba ragi
Har wanda basu gida suna wata nahiya

Dada wanda yaki shiga cikin kirga kusan
Shi zaya sha kunya cikin Nijeriya

Sannan ya zam mugu sharari jahili
Mai taimakawa don a cuci arewiya

To malaman Sansan inai muku gargadi
Dan Allah don manzo Rasulu abin biya

Kuma banda kosawa ku dau hakuri kwarai
A wajen kidaya kadda ku dinga tsamiya

Ku bi sannu-sannu a hankali ba firgita
Kuma ba tsanantawa a kowace tambaya

In ko akayi muku tambaya ta rashin sani
Ku bada amsa kadda ku kosa kun jiya

Kuyi ayyukanku da gaskiya bisa ka'ida
Acikin birane, kauyuka har tsangaya

Ahaiyye iyyenanaiyaye yurai yurai
Malam abin ga da niyyi kada kai tambaya

Na barwa Jallah wa'azu sarki mai sani
Ubangiji ya sani kafin ya darsu ga zuciya

To shugaban kirga muna ta sa ido
Muga ayyukan komi yana kan gaskiya

Don kadda azo da ka taho ayi ta gunaguni
Harma takai mu fagen a dinga hatsaniya

kuma kar ta kai ga fagen abin da-na-sani
Ita ko alama ce ta bacin zuciya

Da-na-sani keya a baya take tutur
In an fade ta ku tabbata an sha wuya

Gabas da Yamma, Tsakiya da Arewiya
Muga kan shirin komi ya zam mana bai daya

Don kada a sayar da dubu a kasa sayan daya
Har ma akai ga fagen ace ya rasa kiya

Alhamdu LilLahi ina yin godiya
Agurin Ta'ala Jallah Sarki shi daya

Tamat bi HamdilLahi waka ta tsaya
Waka a gargadinku nan mu gaba daya

a wajen bayani kada ku damu da tambaya
Yar shehu tai wanga tsari kun jiya

In an ka ce adires ku duba ba wuya
Don ni a kofar mata sai kui tambaya

Nagode Allah har Rasulu abin biya
Alai Sahabbai Tabi'ina da Auliya

Baitinta Sittin ba Biyar ba kunjiya
Na rufe da sunan wanda baya fariya

Wakar Zuwan An Nasara Kasar Hausa; Daga Sarkin Musulmi Attahiru

Shine dai Sarkin Musulmi na karshe, kafi mulkin Turawa. Ya rasu a Burmi a ran 27 ga watan July 1903, bayan sun kafsa da Turawan mulkin mallaka. Ya ki amincewa da Turawan da kuma tsare-tsaren da suka zo masa da su, a saboda haka nema ya rubuta wannan waka, domin ya fadakar da mutanensa illar zama karkashin mulkin Nasara. Hakan ya jawo bore a kasar Hausa, wanda ya sanya, turawan suka yi fito-na-fito dashi. Ganin hakanne ya sanya ya bar garin Sakkwato, inda yayi niyyar yin Hijira zuwa kasa maitsarki. Ya rasu tare da mutane da dama, kuma an kama jama'u da dama, cikinsu kuwa hadda Sarkin Kano Alu. Ga dai wakar

Gudun mutuwa da son rai aggaremu
Da kau kin kaddara abi Annasara

Ina muka yi da dama da hauni suna
Ku tashi mu sa gabanmu mu tsira tsara

Idan ka ce akwai wahala ga tashi
Lahan duka na ga masu biyan Nasara

Idan iko ka kai kak ko ki tashi
Ina iko shi kai ikon Nasara

Idan sun baka kyauta, kar ka karba
Dafi na sun ka baka guba Nasara

Suna foro garemu mu bar zalama
Mazalunta da kansu diyan Nasara

Bakar fitina garesu da kau makida
Ta bata dinin musulmi Annasara

Halin da mu kai ga yau aka bayyanawa
Dalilin ke ga an ka sako Nasara

Ku bar jin masu cewa ba'a ashi
Ina halin zama ga Annnasara

Mu mai da gabanmu Makka mu zo Madina
Madina da Makka dai ab ba Nasara

Batu na Shehu yai yi shi bashi tashi
Sa'a ta ya fade ta ta Annasara

Muna da nufa idan mun samu iko
Mu ja daga, mu kore Annasara

Idan ko sun kashe mu mu san shahada
Muje aljanna sai mu ishe makara.

Sai dai an samu sabani tsakanin masana, a gameda waye ya rubuta wannan waka. Dandatti Abdukadir ya bayyana hujjar cewa, Sarkin Musulmi Attahiru n ya rubuta ta. Amma A B Yahaya shi yana ganin wani malami ne maisuna Malam Labbo dan Mariya Kwasare ya rubutata, inda yace ya samo wannan hujja ce daga Waziri Junaidu.