Malam Aliyu Aqilu dai ba bako bane ga wanda yasan wakokin Hausa. Asalinsa mutumin Sakkwato ne, duk da yake a Kano yafi shahara, kuma anan iyalinsa suke, ana kuma Allah yayi masa rasuwa. An haife shi a shekara 1918, a garin Jega na kasar Gwandu, wanda a yanzu ke jihar Kebbi. Cikin malaman da yayi karatun alqur'ani a gunsu sun hada da ; mahaifinsa Aliyu Madaha, da kuma Alhaji Muhtar Tsoho, da Malam Muhammadu dan Takusa, da M Ban-Allah, da kuma malam AbdulMumini. Ya fara zuwa Kano tun yana da kamar shekaru 15, babban malaminsa a Kano shine: Malam Mahmudu na malam Salga, kuma Muqaddaminsa na Tijjaniya shine Malam Salga. Ya zauna a Borno shekara 23. Malam Akilu Aliyu gogaggen dan siyasa ne, kuma mai bin akidun siyasar NEPU, kuma sana'ar da aka fi saninsa da ita, itace dinki. Ya samu Digirin girmamawa (Honorary Doctorate Degree) daga Jamiar Bayero ta Kano, kafin rasuwarsa. Ya wallafi wakoki da dama, cikinsu kuwa sun hada da na addini, siyasa, zaman tare, tafiye-tafiye dss. To acikinsu ne na zabo mana daya daga ciki, kafin in Allah ya yarda mu kawo muku sauran, wannan waka kuwa itace wadda fasihin Sha'irin yayiwa Saniya. Ga dai wakar;
Ya mai ni'ima mayawaiciya
Ya mai kudura makadaiciya
Haske da basira naka ne
Ya Rabbu ka buden zuciya
Domin inyi waka yar kadan
Mai yar magana mashahuriya
Amma a takaice a dan mu san
Dimbin amfanin Saniya
Sunce mata dadi goma wai
Wannan magana na dai jiya
Wato maganar na ji ta ne
Karba tata sai na waiwaya
A'a karbarta da lokaci
Sai na juya na waiwaya
Ba goma bama wane dari
Metan suke har da guda daya
Wa za shi iya shi kididdige
Dadadan dadin Saniya
Nan dai a takaice guda darin
Zan zo muku yanzu da dai daya
To sai muyi tsit domin mu ji
Zan fara bayanin Saniya
Mamaki ne da tu'ajjibi
acikin sha'anonin saniya
Tirkashi! O'oi, wane mutum
Sanbarka dau duka saniya
Kin dau kaya kin dau mutum,
Da abinci mutum ya rataya
Kallonta shi sanya farinciki
Kukanta shi sanyaya zuciya
Shafarta shi sa maka walwala
Dubarta idonka shi sanyaya
Ba'a samu guda ba na yasuwa
Daga kowane sashin saniya
Madara, Kindirmo, Dakkashi
Kangar da Cukui daga Saniya
Kassanta ana Alli dasu
Ya kyautu anan in waiwaya
Kashinta ana shafe dashi
Losonmu na da Nijeriya
Kirginta ana wasaki da shi
Mun san haka duk Nijeriya
Har gobe ana kiri da shi
Da gareshi ake bulaliya
Na lura ana Waga dashi
Da gareshi ake yin tsirkiya
Shike daure karaga da shi
Tsani, Barho da Takobiya
shike yin takalma da shi
Kwakkwaran kirgin Saniya
Na lura da shi ke yin kube
Na wuka, Barho da Takobiya
Ka tuna fa da shi ke Janjami
Sai mai girma kan rataya
Baza na yawaita maganganu
Ga yar sa'at magajarciya
Ba nuna gadara ko isa
Ko kasaita matsananciya
Daga nan ya zuwa can ko ina
Acikin duka sassan duniya
Na hanga, zaune a hankali
Kuma na maka duba na tsaya
Wai ko zan gano na yasuwa
Wani dan gutsure daga Saniya
Anya kuwa a same shi dai?
Amsa naka so na tambaya
Shin ko ko akwai abu ne daban
Marashin fa'ida daga saniya
Indai da akwai a fada muji
Daga Sa ya zuwa kan Saniya
Guzuma ta zamo ko Dangwala
Ko Karsana ce ma Sauraya
Amsa a'a ai babu shi
Abu yasasshe daga Saniya
Wannan kuwa ta gamsar da ni
Amsa ke nan makatarciya
Mai haske gata a wartsake
Har yau mai dada zuciya
Wakar sunan dana bata shi
Dadadan dadin Saniya
Wannan jin dadin ya isa
Daga kowane sashin Duniya
Kar wai ku cane gefe guda
Daga kowane barin kun jiya
Me zamu kwatanta ne da shi
Ga misali, sai dai lafiya
Wannan itace duk kan gaba
Daga duk jin dadin duniya
Amma a wadata kowace
Daga kowane fannin duniya
Jama'u-Jama'u duk an hadu
Cewa dai babu ya saniya
Fifiko nata yana gaba
ga na dabbobi duka saniya
Yai nisa basu tara da shi
Ko sunyi gudu sun garzaya
Ba za fa su shawo kan sa ba
Ko sun zaga sun kewaya
Kai ban zaci sa riske shi ba
Ko sun tafiya matsananciya
Abu ne mawuyaci dankari!
Har yanzu wuyar mawuyaciya
Gaba dai, gaba dai, gaba dai, gaba
Gaba, Nagge, da aiki saniya
Ja al'amarinki madaukaki
Gaba dai ba baya ba Saniya
Ja dai sha'aninki na arziki
Ke baki shiga sha'anin tsiya
Madalla, madalla dake
Tsarinki da kyawo saniya
Sannunki nace na gaida ke
ni na yabi aikin saniya
Girman daraja, girman isa
Sannan darajar mayawaiciya
Taure yace a sanar dake
sakon akuya da na Tunkiya
Sun mika wuya sun sallama
Cewa a nada ki sarauniya
Sun sa hannu da guda-guda
Sun lamunce daga zuciya
Rago tuni shi ya sallama
Dauke shi jakada saniya
Dabbar da ta ja gaba dake
Ta dau wahala matsananciya
Gurbin riba sai faduwa
Sai rarraba hajjar mujiya
Tsini akaje nema gaba
Kunda ta gagara tun jiya
Wannan magana bata fadi ba
Wa zaya gaya mini "Kai tsaye"
Jama'a daga nan zan dakata
In sanya alama in tsaya
Ni naku Aliyu Aqilu ne
amsa a wajen maitambaya.
3 comments:
Assalam, naji dadin samun wannar wakar. Don ALLAH kusa mana wadda yake cewa.
Yaro nemi diyar dattawa
sanda kake zaka neman aure
Bame gemu ko saje ba
bame gogeggen wando ba
.....................
me magana tasa takar kaure
wanda yace E baya a'a
........................
Allah Ya saka da aiheri, don Allah a yi kokari a sa mana wasu wakokin nasa da na sauran mawakan Hausa (rubutattu).
Menene ma’anar wasaki
Post a Comment