Wannan waka ta jawowa Malam Mudi dauri a gidan yari. Domin a fahimtar Turawan Mulki wannan wani sako ne da kan iya tunzura talakawa suyi bore, kuma kan iya jefa kasa cikin juyin-juya hali irin na Kwaminisanci. Mudi Spikin ya rubuta wannan waka a 1948. Ga dai wakar
Ya yan'uwa ku zo don ku ji ni
Zan wo bayani akan Rusiya
Gama Ingilishi fa sun tashi haikan
Suka suke yi akan Rusiya
Da babbata hanyarsu don kar a so su
Don kar su zo nan mutan Rusiya
Shine nake so in wo dan bayani
Domin ku gane kasar Rusiya
Kasa ce ta kirki da himma garesu
Da kaunar mutane kasar Rusiya
Wakilinsu Malik sunansa ke nan
Sunan musulmi da ba fariya
Ni dai ace yau zan samu iko
Ni sai in koma kasar Rusiya
Kamar na iya tsunts inje can in Zauna
Idan na tuno su mutan Rusiya
Girmama kowa dabi'arsu ce
Ibada kamar Hajji sai Rusiya
Da son musulunci da bayar da zakka
Yawan azumi sai kasar Rusiya
Kwalta na banza damu bamu samu
Da kafur akeyi acan Rusiya
Da banki na rance idan har kana so
Ko fam Dubu Goma baki daya
Musaki acan sai ya zauna da Gwamna
Wajen shawara babu kin gaskiya
Sa'annan da sauran abubba na kirki
Suna da yawa a kasar Rusiya
Gidaje dubu Goma ne don Musakai
A yau su kasar wane ba ko daya
Akwai Talakawa akwai Tajirai
Kamar dai kasarmu ta Nijeriya
Anan gaba na tabbata babu shakka
Nijeriya zamu zam Rusiya
Mu zam mun fice daga gun Ingilishi
Mutanen daba sa rikon gaskiya
Sun barmu babu kudi babu gona
Babu abin yi cikin gaskiya
Sun shekaru yanzu Hamsin kasarmu
Ba taimako babu son gaskiya
Ta'ala Rahimu kadai taimakemu
Ka kawo mutan Rasha Nijeriya
Idan aka ce wa ya tsara ta waka
Ya bayyana halin mutan Rusiya
Ba zan boye suna ba ko za'a nema
Mudi spikin maso Rusiya
Gama bani tsoro na dauri hakika
Akan Rasha ma sai in bar duniya
5 comments:
Allah Ya jiƙan sa da rahama.
🤲
Rayuwa kenan.
Allah jikan maza
Allah ya gafarta masa
Allah ya masa Rahama
Allah ya gafarta masa
Post a Comment