Saturday, April 7, 2007

Wakar Buhari; Daga Wazirin Sakkwato Buhari 1903

Wannan wakar an rubutata ne a lokacin da Daular Usmaniya ta Sakkwato ta shiga cikin wani halin kaka-ni-kayi. A lokacin da Turawan mulki suka tasarwa Daular haikan! Daga kudancin Daular, ga kuma Rabih daga bangaren Gabas, sa'annan ga kuma yake yake acikin daular, tsakanin Tukurawa da Yusufawa a Kano, da kuma wasu sassa na daular. Marubucin dai shine shahararran Wazirin nan na Sakkwato, wato Waziri Buhari dan Gidado, wanda jika ne ga Sarkin Musulmi Muhammadu Bello. Ya nuna takaicinsa game da yadda abubuwa suka tarwatsewa Daular ta fulani, da kuma yadda ya gaza wajen sulhuntawa tsakanin Sarkin Kano Tukur da Yan'uwansa, wanda hakan yayi sanadiyyar Yakin Basasar Kano. Hakan nema ya jawo ya rasa idonsa. Ya dai rayu, har zamanin da turawa suka ci Sakkwato, ya rasu a farkon karni na 20.
Ga dai wakar tasa;

Jama'a da ku ni ke kun ji aqrani
Tsoho da sabubba, dud da yan sabyani
Ku zan fadama na nesa hal jirani
Na tsorata, tsoro mai yawa ikhwani
Ga abubuwanga da niggani ashjani

In kun bideni ku tambaya mi ag garan
Halin da ajjiya yau dabam ya firgitan
Shagala zaman ashraru ya shiga sai kadan
Kowa da kowa yau ya rage sai kadan
Wannan abin ya tsoratani

Ga abinda nijji da nig gani bisa kowane
Abu na cikinmu ku dubi iko ya dune
Ban san shi da wuri waliyya tab bayyane
Tsoronga Maryamu taggani har tat tuni
ajban li dhalika minka aw ajbani

Kaitonmu ya jama'a ku tashi mu fifika
Ga abinda sun kayi ko kadanne mu taimaka
Bisa gwargwadanmu ku dubi sa'a ta cika
umara'una, ulama'una sun sam tuqa
Sulaha'una, shuhada'una naji bayani

Amma in da zato raina nai tuni
Shibka abinda ka turbuda shi kan gani
Bari firgita don juge-jugen zamani
Baka gadi tsoro gunmu hakkan ka sani
Ko mumini mai quwwatu lil imani

Tunda randa kas san wanda yaika mai sama
Samo rashi, khairan da Sharran ya gama
Bamai ije maka dai cikinsu, tsaya ruma
Komi taho maka hankuri zaka yi zama
Ka wakkalawa ubangiji Rahmani

Kai dan'uwa na so ka lura ka rarrabe
Ga abinda yaffi gareka don ka fice kure
Rike gaskiya ka santa me kake lalube
Inda kasan tuba kakan rike gwadabe
Daba kaji tsoro ba don hidhyani

Kullum ina jin wa'azi inda shuyukina
Nazo karatu naji gun ulama'una
Subhana, kin ji yai yawa don son ghina
Madalla Maryamu kin tuna min na tuna
Can da wuri na zauna cin nasyani

Na kasa farga yau da gobe suna zuwa
Ga mutum shi kasa abinda yayi cikin fa wa
Karfi shi kau da gani, shi kau sha mantuwa
Na kasa tuba ga zunubbai sun yawa
Kuma ga shuyukhi ga halin sibyani

Na roki Allah Jalla shi ka isam mini
Ga abinda yas same ni shi ka biya mini
Ga abinda nis so zahiri in badini
Na tuba ya Allahu gafarta mini
Don Shehu nurin zamanin Usmanu

Tun nan da barzakhu lahira a shi taimaka
Aikin da niyyi na gaskiya shi biya garan
Shi hana ni muggun yalla ko da nufa kadan
Astagfurullaha l' azima shi agazan
Don shehu Abdulqadir Jilani

Domin Rufa'i ubangiji ka raba mana
Rokon da nai maka don badai ka isan mana
Haka na Dasuki gare su nan muka dangana
Da zaman kushewa har kiyama Rabbana
Amsar Takardu agazan Mannanu

Kogi; Daga Limamin Daura Usman 1899

Wannan Waka dai an rubuta ta ne a daidai lokacin da Turawa suka shigo Arewacin Nijeriya. Limamin Daura Usman ne ya rubutata, domin yayi kira ga Sarakunan Kasar Daura, dasu daina zalunci, ya kuma nusar da talakawan kasar illar zalunci. A dalilin rubuta wakar, sarakunan Fulanin Daura suka kore shi, inda ya tsere zuwa Sakkwato, a daidai lokacin da Turawa suka koro Sarkin Musulmi Attahiru. Ana kyautata zaton, ya mutu aBurmi tare da Sarkin Musulmi Attahiru. Ga dai wakar;

Kusan zulmu zulmatun ne a yaum al qiyamati
Fada ta rasulillahi manzo muhammada

Ku shimfida adalci gabas, duk da Yamma da
Kudu da Arewa, du ga ummar Muhammada

Ina Dogarai har Jeka fada da kwarakwarai
Da mata na fada, ku zo ku saurara fa'ida

Kaza yan lifidda, har da yan bindiga duka
Zagage ku saurara har ku samo fa fa'ida

Kaza yan baraya harda yan garkuwa duka
Da yan figini du da mai so yasan fa'ida

Fa kai kuwa wawa dai na wauta cikin gari
Ka dawo ga hanya kasan rahamar Ahmada

Fa ku kuwa yan sarki ku bar bin garuruwa
kuna kwace amfanin mutane mufassada

Kuna yin Kilisa don leka gidaddaje
Kuna gane matanmu kuna sabawa Muhammada

Fa ku kau talakawa fakirai ku zam ku ji
Saraki na sarki ne, Talakka na rabbana

Ina masu sanya ruwa a nono su sai
A kaisu sa'ira gobe nesa ga Ahmada

Wadansu su sa gawasa da kaya su garwaya
Fa domin su sai da guba, su sabi Muhammada

Wadansu dafare su kan sa su garwaya
Su sai she si don basu kamnar Muhammada

Wadansu da yan kuka su barka su garwaya
Suna shan azaba, gobe nesa ga Ahmada

Wadansu suna sanya ruwa su kara da kankani
Abin na haramun ne na nesa ga Ahmada

Ana masu kanwa? to ku saurara nan fadin
Ku tuba ga algushu, na nesa ga Ahmada

Su dibo fara toka su kawo su garwaya
Su saishe to domin basu kamnar Muhammada