Shine dai Sarkin Musulmi na karshe, kafi mulkin Turawa. Ya rasu a Burmi a ran 27 ga watan July 1903, bayan sun kafsa da Turawan mulkin mallaka. Ya ki amincewa da Turawan da kuma tsare-tsaren da suka zo masa da su, a saboda haka nema ya rubuta wannan waka, domin ya fadakar da mutanensa illar zama karkashin mulkin Nasara. Hakan ya jawo bore a kasar Hausa, wanda ya sanya, turawan suka yi fito-na-fito dashi. Ganin hakanne ya sanya ya bar garin Sakkwato, inda yayi niyyar yin Hijira zuwa kasa maitsarki. Ya rasu tare da mutane da dama, kuma an kama jama'u da dama, cikinsu kuwa hadda Sarkin Kano Alu. Ga dai wakar
Gudun mutuwa da son rai aggaremu
Da kau kin kaddara abi Annasara
Ina muka yi da dama da hauni suna
Ku tashi mu sa gabanmu mu tsira tsara
Idan ka ce akwai wahala ga tashi
Lahan duka na ga masu biyan Nasara
Idan iko ka kai kak ko ki tashi
Ina iko shi kai ikon Nasara
Idan sun baka kyauta, kar ka karba
Dafi na sun ka baka guba Nasara
Suna foro garemu mu bar zalama
Mazalunta da kansu diyan Nasara
Bakar fitina garesu da kau makida
Ta bata dinin musulmi Annasara
Halin da mu kai ga yau aka bayyanawa
Dalilin ke ga an ka sako Nasara
Ku bar jin masu cewa ba'a ashi
Ina halin zama ga Annnasara
Mu mai da gabanmu Makka mu zo Madina
Madina da Makka dai ab ba Nasara
Batu na Shehu yai yi shi bashi tashi
Sa'a ta ya fade ta ta Annasara
Muna da nufa idan mun samu iko
Mu ja daga, mu kore Annasara
Idan ko sun kashe mu mu san shahada
Muje aljanna sai mu ishe makara.
Sai dai an samu sabani tsakanin masana, a gameda waye ya rubuta wannan waka. Dandatti Abdukadir ya bayyana hujjar cewa, Sarkin Musulmi Attahiru n ya rubuta ta. Amma A B Yahaya shi yana ganin wani malami ne maisuna Malam Labbo dan Mariya Kwasare ya rubutata, inda yace ya samo wannan hujja ce daga Waziri Junaidu.
7 comments:
Mecece hujjar shi Farfesa Dandatti? Zai kyautu mu san ta.
Jiya jiyan nan na gama karanta tarihin gudun Sarkin Musulmi Attahiru 1, wanda Malam Danjuma Katsina ya rubuta. Karanta wannan wakar ya kara mani ilmi a kan dalilan yin hijirar da su Sultan din su ka yi. SHEME
Bani da cikakken bayanin hujjarsa, amma zan bincika
Assalamu alaikum, wannan ita ce rana ta farko da na fara shigowa wannan dandali, kuma ya ban shaawa kwarai da gasken gaske. inshaAllahu zan ci gaba da shigo shi daga lokaci zuwa lokaci. Amma yanzu ga rokona daya da tambaya ta daya. rokon nawa shine;- Don Allah ina so ku yi kokari ku sanya wakokin karni na 20 irin su TBBAN HAKIKAN da makamantan su. fatawa ta biyu kuma shine ni kaina ina da wakoki da nayi kuma in ba abokaina na kur-kusa da ni ba babu wanda ya san da su. kuna ina so in yada su ta wannan dandali, to shin ta yaya zn sko su don amfanin jamaa?. Ku huta lafiya, nine naku din-din-din;- RABIU ISA AYAGI P.O.Box 14224 Email; rabiuisaayagi@yahoo.com OR burwaye@gmail.com
The information here is great. I will invite my friends here.
Thanks
I googled to find anything written about my hero Mal Saadu Zungur, when I came across this interesting blog. I am so much taking with most of the poems here and fell more respect to the great heroes/poets who wrote them. I definately will invite my friends to this site.
MAL Muhammadu ayi wa ilmi adalci wajen yin nuni da duk inda aka samo wani rubutu ko sadaran rubutu wanda ba kai ka rubuta ba. Ina ganin baitin da ka sa kasan hoton ka, daga talifin marigayi Aliyu Akilu ka samo shi. Allah ya sa mu dace.
Dear Maryam Bagel.
On your interest on Malam Sa'adu Zungur, pls see Yakubu, A.M. (1999), Sa'adu Zungur: an anthology of the Social and Political Writings of a Nigerian Nationalist, published by Nigerian Defence Academy, Kaduna. It is the most indepth study, to the best of my knowledge, of this illustrious/ Nigerian.
Post a Comment