Wednesday, April 4, 2007

Begen Yakin Shuhadar Hadejia; Daga M Ibrahim Katala

Acikin shekara ta 1906 ne, Turawan mulkin mallaka tare da sojojinsu dauke da muggan, makamai suka yiwa birnin Hadejia tsinke. Inda hakan tayi sanadiyyar gwabza wani mummunan fada tsakanin Turawan mulkin mallaka da kuma Jaruman kasar Hadejia masu gwagwarmayar kwatar yancin kai. Hakan yayi sanadiyyar yiwa mutanen Hadejia kisan kiyashi, inda aka kissima cewa, dubban mutane ne suka rasa rayukansu a sanadiyar hakan. Babban abin lura shine, dukkan wadannan dubban bayin Allah da suka rasa rayukansu, sun rasa ne a rana guda, cikinsu kuwa harda Sarkin na Hadeja a wannan zamani, Wato Sarkin Hadejia Muhammadu. Wannan waka ta tattare dukkan abinda ya faru a ranar, ta kuma yi cikkakken bayani gameda yadda Shahidan Hadeja suka jajircewa abinda suka kira, bautar dasu acikin kasarsu. Koba komai, wannan ya nuna yadda yan Afrika suka dauki yancinsu da muhimmanci. Da fatan Allah ya jikansu, nake cewa ga abinda ya samu;

Allahu sarki Shi kadai yake Wahidun
Sammai da kassai, Jallah bashi da kishiya

Shi ba fari, shi ba Baki ba Ubangiji
Ba ja ba, ba alkashi ba, shi ba rawaya

Ba sake-sake ba, ba kamar yarani ba
Shudi da kore Jalla bashi da mai kama

Zatinsa baya tattara, ba rarraba
Da kawai da motsi babu yayi ko daya

Sarkin da ba na biyunsa, ba na ukunsa
Fahami basira zani begen shahidi

Ranar Talata mun ga tashin duniya
Ranar Muhammdu yai shahada zahira

Yayi jawabi ya cane shi bai gudu
Shi bashi mai kamu a daral duniya

Rago akan kora, a bishi a kam masa
Amma sadauki ba gudu sai faduwa

Sarki Muhammdu yai jawabi ya cika
Shi bashi mai kamu ya ja shi ya tunkiya

Dan Mele Sarkin Yaki shi kuma ya cane
Muna da rai Sarkinmu baya kamuwa

Ma'aji Salihi yai jawabi ya cane
Mun dau shahada zahira bahakikiya

Manya da yara duk shirin yaki su kai
Kowa yana wanka, yana kuma Alwala

Kowa yana sallama cikin ahli nasa
Sun sa gabansu a lahira ba dawaya

Jama'ar Hadejawa dada duk suka hallara
Kowa yana ce "yau ma zama shahidai"

Shi bai kamar tsoro, balle ya razana
Kan ya ije ma babu kingin hamzari

Ajali idan yai babu kwana duniya
Kai dai zamo kullum shiri duk safiya

Shi bai kamar tsoro, balle ya razana
Bai san gudu dan Garba sarki jarumi

Mutuwa tafarki ce kowa zaiyi ta
Kullu nafsin kowanne ya dandana

Aka daura sirdinsa ya hau bisa ya tsaya
Yace "mu dau himmar shahada Zahira"

Sarki Muhammdu bashi tsoro ba gudu
Allah, Ma'aiki su yake tsoro kadai

Hauninsa Linzami mayani ya rike
Damansa tsabihi salatin musdafa

Dan maikaratu, tudun kasa ba dawaya
Dan Garba, jikan Sambo sarkin adali

Duka mai shahada auwalinsu Madacima
Suka barace shi da fari, ya mutu shahidi

Farkon hawan yakin Talata kun jiya
Galadima, Sarki Haruna sune awwali

Alkali, Sarkin Yaki, Kaura Ahmada
Sarkin Arewa sun kaje can tsaye

Suka jeru har da nan kofar gabas
Kafin su zabura mairuwa ta tarda dasu

Kasan Igwa, da fari aka yamutsa
Doki mutum na faduwa ba lasafi

Igwa tana tashi madafa na zuba
Yau sai ta Allah babu Sauran shawari

Sadaukan Muhammadu basu tsoro ko gudu
Sun dakace kofar gida sai faduwa

Sabo, da jikan Tete su harbi suke
A nan a kofar fada duk suka tuntsure

Firyan Hadeja, shi da Bori na Salihu
Kofar Gabas suka fadi duk sun tuntsure

Ai babu mai mutuwa gaban ajali dada
Kan surfa gero, kan daka, wasu kan fita

Hukunci idan Allahu yayi nufinsa
Ba mai tsimi balle dabara ko daya

Tamkar kamar inuwarka baka guje mata
Kan kai gudu ta bika, kai tsai ta tsaya

Attas yana yawo kamar burduduwa
Tamkar zubar wake, acan a masussuka

Ya ratsa soraye, ya rada katanguna
Kamar kabewa, ko kamar tunfafiya

Ya sha zarar Soro, ya ratsa katanguna
Kago da zaure sun fi karfin lasafi

Tsarnu da kurna hakka sa durumi dada
Yansa dabinai, cediya da itatuwa

Rannan musulmi munga kayan al'ajab
Allah ma'aiki su kadai ne magani

AbdulWahabu baka yana hannu nasa
Attas ya samar, nan ya datse tsirkiya.

domin karin bayani, sai a nemi litttafin Dr Haruna Wakili, na Mummbayya House Kano, maisuna Zuwan Turawa Hadejia.

Wakar Kuyangin Sakkwato; Daga Sandan Baba1900

Acikin wasu Kundayen adana rubutattun wakoki dake National Archives Kaduna, an tsinci wani File mai No O/AR 2, wanda ke dauke da wata wakar ajami, wadda F Edgar ya samo a shekarun farko na karni na 20. Acikin File na 20 ne wannan waka take, wadda aka hakkake an kattama shi acikin shekara 1911. Bisa ga dukkan alamu Edgar ne ya kwafi wakar da hannunsa, cikin wata takarda falle daya, wanda aka tabbatar da cewa, zai wuya a samu inda ya kwafo wakar. Amma duk da haka ya rubuta sunan wanda ya kwafa, ko kuma ya wallafi wakar wanda ya kira da Sandan Baba. Sai dai kuma bai bayyana kowaye shi wannan Sandan Baba ba, ko kuma mutumin ina ne shi, ko a ina ya ganshi, kwafa yayi daga gurinsa, ko kuma reara masa yayi, shi kuma ya rubuta, Allahu a'alamu? Sai dai a wani File mai no 61, wanda aka sanyawa kwanan wata kamar haka; 1909, an rubuta wata waka maisuna "Wakar Yabo/Bege" , daga Sandan Baba mutumin Sakkwato, inda aka bayyana cewa, Sandan Baba ya rerawa wani malami wai shi Malam Bako wakar, shi kuma ya rubuta ta. Wannan ya dan bada haske na gano cewa, Sandan Baba dai ya reara wakar ne, inda Malam Bako da Frank Edgar suka kwafe ta, ko kuma shi malam Bako ya kwafa, shi kuma Edgar ya samu a wurinsa. Bisa ga dukkan alamu, Edgar bai san Sandan Baba ba, amma yana da masaniya akan Malam Bako.
Wakar dai ta kunshi abubuwa uku, akwai Zambo, Habaici da kuma Yabo. Badai takamaiman kowa akewa wadannan abubuwa, ko duk mutum daya ne, ko kuma mutane da dama. Amma dai kusan sanin kan kowane cewa, abune ba sabo ba ga Yanmatan kasar Hausa, su kirkiri waka don Yabo ko Fallasa, da sigar Gada. Don haka tabbas wakar dai ta Yanmata ce, da suka rera, saboda wasu dalilai da dama.
Ga dai wakar yadda take:

Shiririta ararrata
Kare gadon gida yayyo

Bani bukinka da shara
Sai ranar zuwa aiki in baka taro ka futassan

Farin wake na banza ne
Ko an matsu ba'a gumbatai

Bambeni ka gara gije
Kurche gidansu tag gado

Domin Biri a janye kadarko
Bika da shirin tuma yazzo

Kwa bace ni in rama
Don ba shi ka chi san ba

Anini mai kammarSisi
Da tsakka gashi fudajje

Kwabo kau mai kamar Fataka
Da tsakka gashi fudajje

Mai-Gwanja gaton shigifa
Na mallam-dan-majidadi

Mai kyautar dala da dala
Na malam-dan-majidadi

Diyal laka ta banza ta
Don bata zuwa tayo wanka

Diyal Danko ta banza ta
Don bata fita cikin rana

Zancen daka sai mata da miji
Hanyar bisa dole sai tsuntsu

Garar kasa maganin ajiya
Zago mai fanfatse kaya

Bani zuwa ga yanboko
Gara nazo ga yan madara

Dan boko sai hawan doki
Amma ba kudin sati

Mai rai duk masami ne
Zabarma akwai bidar kuddi

Limamin gidan Joji dogo ketare ka ciro
Har ya manta wando nai

Kuku da Boyi sun rantse
Sai sun dauki yar gwari

Tulu dai ka shan yawo
Randa na nan cikin daki

Mai rai duk shi dau himma
Ayi ta batun bidar kuddi

Dan kawo rinin Allah
Madilla masoyina

Namijin kuti mai kafar kwabi
Har ya raina matatai

Randa na cikin daki
Allah shika bata ruwa ta sha

Tukuruwa mai kaya boye
Gawo da kayarka ka girma

Tataka sai aba doki
Nama sai aba Zaki

Tafarnuwa ta faye yaji
Amma ga maganin sanyi

Dabino farkon ka Baure ne
Acan karshe kake zaki

Anini dan mutan Lokoja
Bana yazo kasar Hausa

Kwa doke ni in rama
Don bashi ka tufasan ba.

Ga mai son jin cikakken bayanin wakar sai ya nemi makalar da Grahm Furniss da Yunusa Ibrahim suka gabatar, mai taken; An Early Twentieth Century Song: "Wakar Kuyangin Sakkwato" A mujallar Harsunan Nijeriya, xvi, 1991/92. CSNL Bayero University Kano. Nigeria.