Saturday, December 8, 2012

wakar Begen Muhammadu Daga Malam Nasiru Kabara

wannan waka ce da marigayi Malam Nasiru Kabara ya rubutu, domin nuna tsantsar kaunarsa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wassallam. Wakar Begen Muhammad ta Malam Nasiru Kabara Bismillahir Rahmanir al Rahim Wa sallalLahu ala nabiyul karim 1. Begen Muhammadu ya cika mani zuciya acikinta ba sauran muhalli ko daya. 2. Wallahi garwashin bidar sado da shi ya kona sassan zuciya wayyoniya 3. Naso ka Daha kamar ido ga makauniya naso inje ni gareka koda sau daya 4. Naso ziyara gani bani da fiffike kaka nake na gano masoyin zuciya 5. Na so ka son mai wabiya da ta so diya ko ko maridhi yadda yaso lafiya. 6. Ko san abincin nan ga wanda ya yunwata ko ko ruwa ga maji kishi zai sha wuya. 7. Mukhtari ka tafi ban gane ka a duniya kona rabauta inga ko gun kwanciya 8. Acikin mafarki in na samu sai ince “Allahu Akbar uh uhum wayyo niyya” 9. Begenka ya konan kasha har jijiya Naman jikina ya zangwanye bai daya 10. Ya kona hanta har da hanjaijai duka Ya bar hawayen zuciya da idaniya 11. Kaunarka ta kone bukatar zuciya Duk babu sauran ma bukatar duniya 12. Inma akwai sauran bukatar zuciya sai ko ganinka da yamma ko ko safiya 13. Ta yada zancen duniya tatsuniya ta dauki amri wanda ya zam gaskiya. 15. Ta yada zancen zo mu ji ta dake fadi ta kalmashe gizo ta hana masa kokiya 16. Duk zuciyar da ta so ka Daha da gaskiya wallahi ta arzurta ba sauran tsiya 17. Tai sutura, ta tufata aluni bam-da-bam labudda tai shaani irin na hawainiya 18. Wata safiya yayi murmushi wata safiya Riga fara, wata ran ya sanyo shudiya. 19. Wata ran da alkyabba fara, wata ran kuwa ya fashe da kuka nai kamar dan saniya . 20. Kaka ni kai da gani cikin nan duniya wa zani kara gunsa ni wayyo niya 21. Ko nayi kara babu mai ji ko ya zam kukan amale nake, ace ko jiniya 22. Mukhtaru ka faku ga gani nasa yai wuya balle ince masa Daha ni na sha wuya 23. Shine abin kara gareshi gani nasa ya zam kamar koyin farar hankakiya 24. Dan san ganinsa yana da yar farkar wuya na dauki jure so ina ta dawainiya 25. In babu wanda nake da shi zai taimaka na sauke kayan zo taya min dauriya 26. Ni dai ganin Makka a bukatar zuciya inje ni can in samu saukin zuciya 27. Inje mahaifatai in san guri inje insha ruwan zamzam inai wata gewaya 28. Inje Safa, inje ni Marwa in dawaya inje musallai, in ziyarci mazan jiya 29. Sannan in dawo in dawafin salama bayan makaman nan da Daha ya tsaitsaya 30. In wo hajjina kamila in masgaya ni dai nufina gun mazajan gaskiya 31. Koda ina yan rarrafe in ja jiki inje Madina garin Habibi Anbiya 32. Inje ni raudhar nan ta Daha in sunkuya in gaisuwa, in dada da safe in dawaya 33. Ya Rabbi domin Anbiya’I da Auliya Domin sahabban wanda ya cika duniya 34. Ka bani iko nai ziyarar Anbiya’a dan Kudubu, dan Gausu, domin anbiya 35. A Ka saukake hanyar zuwanmu Idaibatu Dan Mujtabai, dan Ni’ima domin Ma’iya 36.Kai agajinka A Rabbu dubi idaniya Domin Tijjani al Khudubu mai Tijjaniya 37. Dan gimbiya tasa na kira ka A Rabbana Ka jikan masoyan Daha, rana da safiya 38. Ganar dani Mukhtari Daha Alaniya Domin ya kore min shuunin Duniya 39. Dauke hijabi Rabbana in gane shi fai nan duniya ya rabbi ko a manamiya 40. Rahmarka ta gama kowanne balle niya da na dauka karata ilaika Ilahiya 41. Ya Rabbi nai kara gareka fa kai daya bayanka waye zaya amsa du’a’I’ya. 42. Ka yi wo salati ga Daha kai Taslimiya a gareshi ya Rabbil wara, ya Bariya 43. Duk sanda mai bege yace ‘kul’ safiya sallu ala Mukhtaru koda sau daya 44. Aufan zuwa Tashdiri fi takmilihi Begen Muhammadu ya cika min zuciya

Thursday, March 12, 2009

Me Zan Fada Ne? Daga Sulaiman I Jahun

Ita wannan waka malam Sulaiman I Jahun ne ya rubutawa wata budurwarsa, a lokacin da suke karatu a jamiár Bayero ta Kano. Bai dai nuna lokacin da yayi ta, bai kuma nuna ko wacece yake yiwa wakar ba. Ga dai wakar.
1] Me zan fada ne wanda zai gamsar da ni
Na sifanta kyanki gami da halayenki.

2] Kyawo na mata dai kina da guda Dubu
Ga jiki da hali ba irin mai naki.

3] Kirar jikinki takan saka ai zautuwa
Kana irin dadin karin bakinki.

4] Lafazi da taushi, kana gashi a kammale
Wallahi ban gajiya da saurarenki.

5] Taushin jikinki kamar dadai ba ko kashi
Kamshi da santsi ba kamar labbanki.

6] Ruwan idonki idan mukai kallo biyu
Sai in kamar in nutse in debi na wanki.

7] Haskensa yafi wata daren sallah fari
Gashin girarsa kamar ciyawar tafki.

8] Abin kamar kullum kina sa tozali
Don kyalkyalin manyan idanun naki.

9] Gashinki ga santsi, abin kuma ga tsawo
Sannan wuluk! da baki, bakin hankaki.

10] Naso in sa kaina ciki inyi lif! da ni
In dunga numfashi ina shafarki.

11] Ki kadan ido in gano fari, in gano baki
Ki kadan, ki tsinkan yau da alámarinki.

12] Goshinki wani Zara yar mowar wata
Haskensa ya wuce alfijir goshinki.

13] Zancen dabiá ko a birnin Sakkwato
Aka reni ya, halinta bai kai naki.

Bege Daga Farfesa Bello Salim

Ban taba buga wakokin soyayya ba a wannan zauren, wannan ya faru ne saboda rashin samunsu akan lokaci, to cikin yadda Allah nayi saá na samu littafin Farfesa Bello Saíd, maisuna DAUSAYIN SOYAYYA. Wanda cike yake da wakokin soyayya. Acikin littafin ne na tsakuro muku wannan waka, da Farfesa Bello Salim ya taba rubutawa wata budurwarsa, tun cikin watan Maris na 1977. Wato kusan shekaru talatin da biyu kenan. Bai dai bayyana wa yayiwa wannan waka ba, to amma ya fito da tsintsar soyayyarsa ga wannan baiwar Allah. Ga dai wakar nan.

1] Kin tambayan wai shin me yakan dame ni ne?
Kullum ina zugurum gaban hotonki.

2] Kullum in zauna sai tunani barkatai
Magana kadan sai na kira sunanki.

3] To zo ki zauna zan gaya miki gaskiya
Domin kisan ni bani son in rufe ki.

4] Zan tambayeki ki zayyana mini zahiri
Kin san sifa ta jiki da halayenki.

5] Ko kin sani saurari nawa batu ki san
Nine madubin gane siffofinki

6] Idanuwana sun zamo taga gaman
Ta cikinsu zaki gano irin kirarki.

7] Zan dan bayanin kanki, fuska har wuya
Gangar jiki, ya zuwa ga yan yatsunki.

8] Zan fayyace siffar jikinki gaba daya
In na gama in hado da halayenki.

9] Yawa da santsi, ga tsawo kuma ga baki
Sheki, suna nan duk a gashin kanki.

10] Kuma dubi gashi naki mai daukar ido
Tamkar gilashin nan dake hannuna.

11] Idanuwanki suna sihirtar dan Adam
SEXY Bature kan canewa idonki.

12] Duk wanda yai arba dake ya ganesu to
Sai zuciya tasa ta taállaka gun ki.

13] Hanci da kunne sunyi das! sun zaunu ras!
Kowa ya gansu ko dole yai shaáwarki.

14] Godewa Allah Jallah Sarki Rahimi
Don mustadaá ne gama bakinki.

15] Wuyan barewa shi mukan ce na da kyau
To ai barewace ta kwaikwayi naki

16] Sauko kadan don ki nazar ki yi bincike
Niíma ta Allah wadda ke kirjinki

17] Cikinki shafaffe abin shaáwa kamar
A ce hatsi baya shiga hanjinki

18] Kuturinki zaunanne gwanintar haliku
Shima kawai yasa mutum begenki

19] Cinya da sharaba sumul sun mulmulu
Yannan ki gode Jallah wanda yayi ki.

20] Taka a sannu sarauniya kiyi rangwada
Dan kyan dake sawunki har yatsunki.

21] Zan bar batun kirar jiki zan dakata
Don banda kalmomin siffanta jikinki.

22] Sai dai in gode Jallah sarki Wahidun
Da ya ban idanu har na samu ganinki.

23] A takaice yanzu ki dakata kuma kiy kawai
Saurari sharhina ga halayenki.

24] Hakuri a gunki da hankali kuma ga natso
Tamkar ace mata su zo Kwas gunki.

25] Saurin fushi, tsiwa, fada ko yaudara
Ba ko guda a wajenki gandun kirki.

26] Wadanga siffofi da nai zance bisa
Su sunka sa kullum nake begenki.

27] A ina kike jin zaá san mace kamila
Mai kyan sifa, sannan da halin kirki?

28] Ko an nutsa, an bincika, an rairaye
Sai anyi saá zaá san tamkarki.

29] To shi yasa abadan a kullum safiya
Ni banda tasirin da ya wuce naki.

30] Kuma godiya kullum nake gun Rabbana
Sarkin da yai ikon in ganki, in soki.

31] Kana inyo roko garai Shi mai duka
Yasa ki kaunaci Bello da mai sonki.

Thursday, November 6, 2008

Wakar Talauci da Wadata; Darho

Al'adal Hausawa su kan rena matsiyaci, su kan yaba mai-dukiya,
suna rena baba matsiyaci, suna yaba yaro mai-kurdi, don haka
wani mutum ya wake halin Hausawa duka, sunansa Darho. Ita ke
nan :

A wannan waka, za'a ga anyi amfani da Hausa mai tsauri, domin kuwa, wannan tsohuwar waka ce. An rubuta ta ba tun yau ba. Ita ma na cikin wakokin da Malam Umar Salga ya baiwa Mischlisch a Kumasi.

1 Muna soma waka da suna na Allah,
Gama za mu tsari na halin tsiya .

2 Muna son kidaya t a halin talauci
Da halin wadata f a don ku jiya .

3 Kamannun talauci baki ne gajere
Da doro da tura da annakiya.

4 Kadan yabi yaro, shi tsofas dashi ,
Shi tantakore shi , shi yi kaman kugiya.

5 Idan ya bi tsofo, shi kan Rarasa shi ,
Shi rame, shi komo kaman tsarkiya .

6 Mutum mai-nagarta, kadan ya talauta ,
A maishe shi mugun, da ba gaskiya.

7 Mutum mai-karimci, kadan ya talauta ,
A ce, bashi kyauta da ko kokiiya.

8 Talakan mutum ba shi zance a taro ,
Fa zancensa sai ko cikin zuciya.

9 Kadan ya yi,zance a kan gaskiyarsa,
A ce masa, karya ka kai mun kiya.

A lalata zancen, a yaryamutsa shi ,
A maishe shi wauta abin dariya .

Fa baba talaka a maishe shi yaro,
A ce masa gebe kaman saniya .

Ace masa raggo, ace bashi lura ,
Ace masa, baban da ba moriya.

Kadan anyi taron buki, baa sa shi ,
Fasai za a watse, a kan tambaya.

Kadan za a taro na suna da amre,
Fa sai anyi nisa , a ce, shiyi biya.

Kadan an yi t aro , kamalsa daban ce,
Da wandonsa tsofo da 'yar Z ariya .

Fushin mai talauci abin dariya ne,
Fushinsa da murnalsa duka dai daya.

Talakan mutum ba shi samun aboki,
Fa wa ke abuta da dan shegiya?

18 Fa mai son talaka f a Allah Ta’alah,
Da ya y i talaka cikin jar wuya.

Fa mugun hali duk shi na gun talaka ,
Kadan dai ana son fadin gaskiya.

kazamta da wauta da bata zumunta
Da rowa da ka r ya da aikin riya .

A mugun jini babu tamkar talaka
Gidan duniyan nana ko mu jiya .

Idan ya y i zance da fara 'a ace mai,
dumi a gare shi cakoikoiniya.

Idan ya y i kawaici, a ce masa
Mugu da keta gare shi cikin zuciya.

Ka san, ba nagarta ga mai-yin talauci ,
Kadan za shi zance, a kan ce: tsaya .

Da zancenka mugu na wofi a duniya,
Zama ba ka zancen, da za’a biya .

Fa dangin talaka su nai masa kushe,
Su ce masa zumu ne, da ba moriya.

Ayyukan talaka dadai ba su kyawu
Ga bakin mutane f a har zuciya.

Idan yai da zaf i , su ce, babu tsabta ,
Yana tsarmatawa ga aiki jiya .

Idan yai da kyawu su ce, babu samri,
Yana da nawa, ya ki yi tun j i y a .

Yawan dariya gun talaka , mutane
Su maishe shi wawa kaman kanikiya .

Idan ya y i kawaici, su ce masa, mugu,
Cikinsa da zurfi kaman tumniya.

Fa inda talauci mutum ne, mutane,
Muna damre mu kekewaya.

Mu j e har bugensa, mu far masa da yaiki,
Mu ci shi , mu kamai, mu sa karkiya .

Mu ti kai mu kayes, mu damre, mu yanka,
Mu ja shi , mu yes can, mu ba maikiya.

35 Fa inda haki ne, muna ciccireshi ,
Shi bushe mu tara mu kone tsiya .

Fa haja ta talaka dadai ba ta kyawu,
Zuma nai a kan ce kaman tsamiya.

Idan yakuwa ce a kan ce da tsami,
Madi nai akance da kunkunniya.

diya tai dadai ba t a kyawu ga kowa,
A kan ce, gajera1 ga mai-cibiya.


Da kai gurgurrare, dada ga kumatu
Kaman diya ne na tumfaf iya.

Da cassa da ganni da kwarfin idanu
Da bakinta dogo kaman tsishiya .

A ce mata da kirci dada babu zama
Da warin jiki , sai ka ce rajiya .

Idan t a f i kyawu, a kan ce, da tsiwa,
Fa bata da kumya kaman shegiya.

Mutane, talauci mu ki shi da gaske,
Zama da talauci shina da wuya.

Idan an y i yunwa, abincin talaka
Fa ganyen rama, dorawa, gasaya.

Da rogo, da taura, da gaude, da tsada '
Da dumya da tafasa da har rojiya .

Da faru da gudai, kadanya, tamaka,
Dada magoraza, ciwo kinciya.

Talaka ana kinta amre gaduniya,
A sa mata aibu a rarrataya .

A ce mata kazama, tana barka zana,
A ce, bata shara f a , babu roriya .

Idan malami yai talauci ya shuda,
A kan ce, tababben ga nan ya biya.

A kan ce, karatunsa ya f irgita shi ,
A maishe shi wawa, abin dariya.

Idan yayi zance da nassi , a kyale,
Idan yayi harda, ace, ku jiya .


52 Fa ya tuna haukansa yau tun da s a f e ,
Makoftasu kan ce, fa ai tun jiya . "

Diya ta talaka idan baka ce,
A kan ce, bakinta da muni, jiya .

Idan kuwa, f arace ace tayi muni,
Farin ya faye, sai ka ce zabiya.

Idan tai gajerta ace babu kyawu,
A ce, dunkulalla kaman makaya.

Idan doguwa ce, akan ce, fatalwa,
Tsawon ya faye, kai , abin da wuya.

Dada kun ji halin talauci ku l u r a ,
Ku kilshe , ku tashi bidal dukiya.

Ku shirga Safara, ka j e har Fatoma,
Ku komo t a Bobo, ku zo Daboya.

Ku juya t a Jije , ku juyo ta Dor i
Ku jirgo ta Moshi ku zo har Kaya

Ku komo t a Salaga, ku j e har Kumashi,
Ku zaga t a Guwa, har Agaya.

Ku j e har Kano babu nisa wuce can,
Wadai kuma ka komo Zariya.

Ka ratse ta Kura ka samo baki can,
Ka komo t a Jega, ''tafo har Gaya.

Biyo har t a Sayi, ka komo t a Mangu,
Ka ratsa Dagomba, ka zo Kobiya.

Bidal dukiya wajibi ne gare mu,
Fa ko don mu kimsa zaman duniya.


Da sadaka da amre da suna da laiya ,
Sayen littafai sai akwai dukiya.

Bari da da haji da ci da marayi,
Wadannan ku san, sai akwai ajiya.

Da sa da karatu da gyaran zumunta
Da tanyon makofta f a duk, kun jiya .

Fa mun roki Allah, ya tsarshe mu tsanani
Na duniya da cuta da yunwa, tsiya .

WADATA
1 Muna soma tsari na halin wadata,
Fa jinsa da dadi cikin zuciya.

2 Mutum mawadaci akwai shi da girma,
Ana sonsa Hausa cikin zuciya.

3 Ana durkusa masa, ana bashi girma,
Ana son zumuntansa don dukiya.

4 Idan ya yi zance a taro a yarda,
Ace gaskiya ka fadi mun jiya .

5 Ku san, mawadaci ya kan kirfa karya ,
A ce babu wawa ku zo ku jiya .

6 Idan dumi nai ga taron mutane,
A kan ce, fa mai-fara'a ne shiya .

7 A ce walwala a gare shi ga duniya,
Ya kan bada labari ana dariya .

8 Idan yai karairansa , babu iyaka,
A yarda, a gyara, a ce gaskiya.

9 Fa shi ke da wayo ku san hankalinsa,
Kaman ya f i kowa cikin duniya.

Dada bambadawa suna yin yabonsa,
Suna ce, da kyawu kaman Utiya .

Ubansa wane, uwatasa wance,
Fa kakansa wane, mutanen jiya .

Da da nasa wane da 'ya tasa wance,
Da jikansa wane, fa to kun jiya.

Shi kan bada kyauta ta riga da wando
Da kurdi da tsaba har saniya.

Yana bada zanua da damma da rago,
Ya kan bada kyauta ta har godiya.

Mutum mai-wadata f a shi ke da kyauta,
Mutane su kan ce, fa ba ya shiya.

Idan ba shi zance, shina damre fuska,
Su ce, mai-kawaici, fa don gaskiya.

Su ce, ba shi zancensa, sai ya kamata,
Mutum mai-nagarta ina ya shiya ?


Diya tai dadai ba ta muni ga kowa,
A kan ce, da kyawu kaman Utiya.

A ce, doguwa ce idanu ya madara
Da fatar jiki sai ka ce maraya.

Ace tayi yatsa ya 'ya'ya na marga,
Ace ga duwawunta fa1 tsakiya .

Da mukurun barage hatsaya ta damra,
Ta sa kwandage munduwa sokiya.

Fa hannunta tafshi zama ta wadata,
Gama ba ta aikin da ya faifaya .

Idan kuwa baka ce, su kan ce, da kyawu,
Gama dai bakinta shina walkiya.

Idan kuwa fara ce, su ce, t a f i kyawu,
Farin nata koka Balarabiya.

Idan tai gajerta , su ce, babu komi,
Tana dai da kyawu, zama ta tsaya.

Gajertalta dai-dai kaman nan a ke so,
Zama tayi hanci da kan cibiya.

Idan doguwa ce, su kan ce, da kyawu,
Tsawon ya kamata, gama tai wuya.

A kan sota , mutum ya f i goma,
Ana ce, diya ce ta mai-dukiya.

Fa ga t a da nono, f a sun cika kirji ,
Idanunta kace idon hazbiya.

Kadan an y i amrenta garalta tari ,
Gama dai diya ce ta cin duniya .

A kan dauki kaya da kurdi da zanua,
A yauci gari, don a tambaya.

Mutum mawadaci akwai shi da girma,
Idan ya yi ado, sai a ce godiya.

Fa matansa, ku san, suna ba shi girma,
Suna boye sunansa don dukiya.

Suna durkusa masa, suna ba shi tur ba ,
Su ratse , suna boye fuska, jiya . "

Kadan ya cane, wanga aiki ku bar shi ,
Zama ba ni so nai , su ce, mun jiya .


36 Ku san bashi diba dukiyarsa, ya ba su
Matan nan gama dai , nufin su gare shi ajiya .

37 Fa tari talaka ya kan c i da mata,
Fa har tafi mata ta mai-dukiya.

38 Fa banza, gama babu saura a daki,
Kaman dai ruwa, an zuba rariya .

39 Kaman nan f a kyautar talaka ga mata,
Fa ko yayi , ba godiya, kun jiya?

40 Kadan dan karatu ya samu wada nan,
A kan ce da shi shaihu ne, ya iya.

41 Karatunsa dadi, rubutunsa sosai,
Hadisi, usuli duk ya biya.

42 Idan ya y i murya, a kan ce da dadi,
Kaman an y i gogen ga mai-tsagiya."

Idan an y i yunwa, mutum mawadaci
Abincinsa anberuwa, t a l i y a .

Da kaki, gurasa da waina da taushe,
Tuwo mai-fari, ga miya har miya.

Da kuskus da shashakaqq an garwaya su
Shinashir yana can cikin jar miya.

Fura kuwa ta gero a dama da nono, '
Zama dai ta safe zuma ya jiya .

Gidan mawadaci idan an gane shi ,
A kan san, wadatalsa ba tambaya.

Da soro ginane da darninsa sabo
Da shifkinsa mai-kyau f a an baibaya.


Gida na talaka kazamin gida ne
Da darni tsutsa , sai haki mai-kaya.

Da dai matsatsi da bununsa tsofo
Da kunkunniya, an dade tafaya .

Mutum mawadaci abokinsa sarki
Da malam da tsofon mutum mai-biya.

52 Mutane ku fuce matsari na waka,
Fa s h i ma talakan f a ne, kun jiya .

53 Fa na goda Allah, da na kare tsari
Na halin wada duk da halin tsiya .

54 Da tsira da girma da so duk da yarda,
Su taru ga manzo uban Rakiya.

Thursday, October 30, 2008

Wakar Abinda

Ita dai wannan wakar, malam Umaru Salga ne ya baiwa Mischlich, wani baturen mulki na kasar Jamus, a yayin da yake kokarin tattara bayanai akan tarihin kasar Hausa, domin manazarta dake can kasar Jamus. A cewarsa, "wani almajiri ne ya auri wata mata maisuna Abinda, amma kuma ita Abinda kazama ce ta kin karawa, to a saboda haka sai ya shirya mata wannan waka. Ka nemi kasidar M. B. Dufill domin samun karin bayani.


1 Abinda kazama ce kwarai, ba kadan na ba.

2 Ina son k i bar halin da duk, bai kamata ba.

3 K i zam yin fa shara, kuma kina dumke farkuwa.

4 Iya t a mutane, duk ba ta bar abin ga ba.

5 Tuwonki k i zam gyara, kisa 'yan ruwa kadan.

6 Tuwon j iya kin bata , shi mu ba mu c i shi ba.

7 Idan kin y i min damun fura , saita yamutse.

8 Fa ko na ji yunwa, ba ni iya shan furalkiba.

9 Abin ga da kumya kuma da haushi ga zuciya.

10 Abinda k i bar halin ga, duka bai kamata ba.

Wakar Madugu Yahaya; 18th Century


Ita dai wannan wakar wani marokine yayita, shi wannan mawaki da ake kira Yahaya, ba zama yake a gida yana waka ba. A zamanin da ake tafiya fatauci a kasar zuwa, zuwa kasashen ketare, shi sai ya bi ayari, inda duk aka sauka a zango, ya jawo kayan kidansa, yanawa madugai waka. Ba dai takamaiman lokacin da aka yi wannan waka, to amma wanio manazarci da ake kira M. B. Duffill, yayi hasashen cewa, an rubutatane a karshen karni na 18, ko kuma a farkon karni na 19. Ga mai neman cikakken bayani ga wannan waka, sai ya nemi kasidar da M. B. Dufill ya buga a mujallar SOAS, Vol 13, (1986).

Allah ya k aimu Hausa, ba don iya magana ba.

Madugu Yahaya shi bai iya magana ba .

In an tambaya, ya kan ce: Shiga! debi!

Shiga! debi! Borgu, ba zance ne ba.

Yanzu ga Waru zamne, ga washagari.

Ga waga banye, a ce: Shiga! debi!

Madugu Yahaya, shi bai iya tafiya ba.

Zangon azuhur shi kan ce masa hantsi .

Rana faduwa shi kan ce, la'asar ne.

Mai-baki da garatse ' ' kaman bakin gwando.

Kuma baki da garatse namij in yauni.

Ana tashi, ko ana yankan damna?

Miji da kurkunu, ga jak i da alafa .

Ga mata da guragu, '' kuma babu ruwan gora.

Ana yin salla Sayi, ko salon mussar wofi ?

Gurin salla Sayi aka dauke mini wando.

Malam Iyal yana gyaran sage, dada ya ga k irarra .

18 Wanga hannu da gargaza, wancan kuwa ga yauni.

19 Yana ciza gargaza, yana ciza yauni .

20 Yana cewa: Tudun nan muka jida , ko muna kai ga tudun can?

21 Sani dan Muhamman, baban gwani na Jega.

Thursday, May 31, 2007

Ya Ghiyathul Mustagithina; Daga Hayatu bin Sa'id

Hayatu bin Sa'id baya bukatar gabatarwa ga mutane, domin ga wanda yasan tarihin daular Fulani ta Sakkwato, yasan irin gwagwarmayar da aka sha da shi, da kuma yadda yayiwa Daular tawaye. Wanda, bayan hakan yayi mubayi'a ga Muhammad bin Abdullahi al Mahdi,na Sudan. Mahdi ya nada shi a matsayin halifansa a Daular Sakkwato, inda ya nemi Sarkin MUsulmi na wannan lokacin da yayi masa mubayi'a. Rashin samun nasarar hakan ce ta sanya ya koma ya hada kai da Rabih bin Salih (Rabeh). Inda daga baya suka samu sabani, ya dai rasu a wani karo da suka yi da Rabih. Ya rubuta wannan waka ce, a wani shagube da yayiwa yan'uwansa, a saboda irin mummunar fahimtar da suka yi masa.
Ga dai wakar;

1Ya Ghiyathul mustaghithina
2-na wa khairal nasirina
3Agaza ni kadda ka barni
4Ga dibarata ta kaini
5Yi dibara mai dibara
6Rahmanu ka jikaina
6Rabbu dubanni da rahma
7Anta khairil Rahimina
8Rahamakka sabiqata
9Jin kanka wabilina
10Babu mai yi sai da yin ka
11Wanga zance haka nan na
12Kai kayi ba taliki ba
13Taliki kau ajizina
14Rabbu kai ad dai Qadirun
16Jallah Sarki Qadirina
17Babu sarki daga Allah
18Shi fa Sarkin Gaskiyana
19Wanda yai sammai da kassai
20Wanda yayi dare da rana
21Wanda yai duniya da Barzakh
22Bata tsar mai ko ina na
23Wanda yai ran al-Qiyama
24Shi Azizi na gwanina
25Wanda yai wuta yayi al-Jan
26-na hakika Fatirina
27Agaza ni na kiraka
28Don Muhammadu yo i'ana
29Rabbu tsarshen daga kaidin
30Masu kaidi mufsidina
31Masu hasda da Adawa
32Da gamani kha'inina
33Sare kunci duk na makri
34Jallah Khairul makhirina
35Jallah kai ka tsadda Nuhu
36Shi da Hudu ga kafirina
37Jallah kai ka tsadda Ibra
38-him ga kaumun mu'tadina
39Kai fa kacce kana haqqun
40Fika nasarul muminina
41Don Muhammadu ya ilahil
42Arshi tsarshen makiyana
43Bani ikon shafe bid'a
44Bani ikon raya sunna
45Yo ijaba nai salati
46Ga Muhammadu dan Amina
47Hakaza Allai Sahabbai
48Duk jama'a tabi'ina