Wannan wakar an rubutata ne a lokacin da Daular Usmaniya ta Sakkwato ta shiga cikin wani halin kaka-ni-kayi. A lokacin da Turawan mulki suka tasarwa Daular haikan! Daga kudancin Daular, ga kuma Rabih daga bangaren Gabas, sa'annan ga kuma yake yake acikin daular, tsakanin Tukurawa da Yusufawa a Kano, da kuma wasu sassa na daular. Marubucin dai shine shahararran Wazirin nan na Sakkwato, wato Waziri Buhari dan Gidado, wanda jika ne ga Sarkin Musulmi Muhammadu Bello. Ya nuna takaicinsa game da yadda abubuwa suka tarwatsewa Daular ta fulani, da kuma yadda ya gaza wajen sulhuntawa tsakanin Sarkin Kano Tukur da Yan'uwansa, wanda hakan yayi sanadiyyar Yakin Basasar Kano. Hakan nema ya jawo ya rasa idonsa. Ya dai rayu, har zamanin da turawa suka ci Sakkwato, ya rasu a farkon karni na 20.
Ga dai wakar tasa;
Jama'a da ku ni ke kun ji aqrani
Tsoho da sabubba, dud da yan sabyani
Ku zan fadama na nesa hal jirani
Na tsorata, tsoro mai yawa ikhwani
Ga abubuwanga da niggani ashjani
In kun bideni ku tambaya mi ag garan
Halin da ajjiya yau dabam ya firgitan
Shagala zaman ashraru ya shiga sai kadan
Kowa da kowa yau ya rage sai kadan
Wannan abin ya tsoratani
Ga abinda nijji da nig gani bisa kowane
Abu na cikinmu ku dubi iko ya dune
Ban san shi da wuri waliyya tab bayyane
Tsoronga Maryamu taggani har tat tuni
ajban li dhalika minka aw ajbani
Kaitonmu ya jama'a ku tashi mu fifika
Ga abinda sun kayi ko kadanne mu taimaka
Bisa gwargwadanmu ku dubi sa'a ta cika
umara'una, ulama'una sun sam tuqa
Sulaha'una, shuhada'una naji bayani
Amma in da zato raina nai tuni
Shibka abinda ka turbuda shi kan gani
Bari firgita don juge-jugen zamani
Baka gadi tsoro gunmu hakkan ka sani
Ko mumini mai quwwatu lil imani
Tunda randa kas san wanda yaika mai sama
Samo rashi, khairan da Sharran ya gama
Bamai ije maka dai cikinsu, tsaya ruma
Komi taho maka hankuri zaka yi zama
Ka wakkalawa ubangiji Rahmani
Kai dan'uwa na so ka lura ka rarrabe
Ga abinda yaffi gareka don ka fice kure
Rike gaskiya ka santa me kake lalube
Inda kasan tuba kakan rike gwadabe
Daba kaji tsoro ba don hidhyani
Kullum ina jin wa'azi inda shuyukina
Nazo karatu naji gun ulama'una
Subhana, kin ji yai yawa don son ghina
Madalla Maryamu kin tuna min na tuna
Can da wuri na zauna cin nasyani
Na kasa farga yau da gobe suna zuwa
Ga mutum shi kasa abinda yayi cikin fa wa
Karfi shi kau da gani, shi kau sha mantuwa
Na kasa tuba ga zunubbai sun yawa
Kuma ga shuyukhi ga halin sibyani
Na roki Allah Jalla shi ka isam mini
Ga abinda yas same ni shi ka biya mini
Ga abinda nis so zahiri in badini
Na tuba ya Allahu gafarta mini
Don Shehu nurin zamanin Usmanu
Tun nan da barzakhu lahira a shi taimaka
Aikin da niyyi na gaskiya shi biya garan
Shi hana ni muggun yalla ko da nufa kadan
Astagfurullaha l' azima shi agazan
Don shehu Abdulqadir Jilani
Domin Rufa'i ubangiji ka raba mana
Rokon da nai maka don badai ka isan mana
Haka na Dasuki gare su nan muka dangana
Da zaman kushewa har kiyama Rabbana
Amsar Takardu agazan Mannanu
3 comments:
Assalamu alaikum. Abu mai kyau ne taskace rubuce-rubucen magabata. Jinjina wajiba ce ga wannan fage. To amma ina ba da shawara don Allah a rika yin adalci iga marubuta. Misali, Wazirin Sakkwato wanda ya rubuta wakar da aka kawo a nan, ba jikan Sarkin Musulmi Muhammad Bello ne ba. Jikan Waziri Gidado da Nana Asma'u ne. aka kuma ba a kawo wakar nan daidai ba. Akwai kurakurai da yawa cikin wannan da aka kawo. Wannan ya nuna ba a yi bincike mai inganci ba, kuma kusan ba a san tarihin Sakkwato ba lokacin kawo wannan waka. Na gode
Assalamu alaikum. Abu mai kyau ne taskace rubuce-rubucen magabata. Jinjina wajiba ce ga wannan fage. To amma ina ba da shawara don Allah a rika yin adalci iga marubuta. Misali, Wazirin Sakkwato wanda ya rubuta wakar da aka kawo a nan, ba jikan Sarkin Musulmi Muhammad Bello ne ba. Jikan Waziri Gidado da Nana Asma'u ne. aka kuma ba a kawo wakar nan daidai ba. Akwai kurakurai da yawa cikin wannan da aka kawo. Wannan ya nuna ba a yi bincike mai inganci ba, kuma kusan ba a san tarihin Sakkwato ba lokacin kawo wannan waka. Na gode
Haka maganar 'ananymous' take. Sai dai tambayata game da jimlar da ke cewa, Waziri Buhari da Gidado ne, wanda jika ne ga Sarkin Musulmi Muhammadu Bello. Shin ana nufin Waziri Buharin ne jikan Muhammadu Bello, ko kuwa Waziri Gidadon ne jikan Muhammadu Bello? To gaskiyar lamari shi ne, Buhari jikan Gidado ne mijin Nana Asma'u, 'yar Shehu Usmanu dan Fodiyo, kuma kaunar Muhammadu Bello. Shi kuwa Gidado dan Lema ne kuma abokin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello.
Post a Comment