Ta'ala ina rokonka ranar da zan cika
Kasa in cika Allah cikin daki na
Gaban duk iyali na da 'ya'ya da 'yan'uwa
Allah ina rokon ka sai a gidana
Idan na cika yan'uwa na gaya muku
Da kun ji cikawata ku taru gidana
Idan har da rana abin yazo ko cikin dare
Batun jinkiri kar dai ya faru wurina
Idan anyi sallah an gama kar a dakata
A dauka kawai hanyar zuwa kabarina
Idan anka je da zuwa a sani ciki kawai
Cikin hankali domin tuno lamarina
Kasar kabarin kuma kar a ware daban-daban
A turo gaba daya duk ta watsu a kaina
Idan aka kare gini da an tashi an gama
Ku koma wajen harkarku ya jama'ata
Batun sadakar Uku, ko Bakwai, ko ta Arba'in
Kaza shekara wallahi babu ruwana
Irin masu kukan nan da ihu da razana
Don Allah na roke ku kar kuyi kaina
Ina tausayin ku kwarai zuwa gun jana'iza
Kaza wahalar tafiya hakan kabarina
Kaza wahalar wanka da dauko ni don zuwa
Cikin makara tafiya zuwa karshe na
Hakika a rannan da da ikon da zan iya
Ya sa tausayin a wajen dukan jama'ana
Anan zan tsaya domin wasiyarmu ta tsaya
Mudi Spikin ne uba ga Amina
6 comments:
Yau Allah ya nufa an cika masa wasiyyarsa, Allah ya jikansa, ameen.
Allah kaji kansa kai masa rahama, ka sanya shi cikin amintattaun bayinka, ka yafe laifukansa, ameen.
ALLAH Ya jikan Alh. Mudi spikin, Allah Yai masa rahma, Ya yafe masa. Ameen
Allah yai masa rahama
Allah yajikansa ya sa Aljanna ce makomarsa. Nasamu abubuwa masu amfani acikin wannan wasiyya tasa.
Allah yagafartamasa
Muma insha allahu zamuyi irin cikawarsa dakuma wasiyarsa ga iyayenmu' yanuwanmu, ya yayenmu dakm matayenmu
Post a Comment