Thursday, March 12, 2009

Me Zan Fada Ne? Daga Sulaiman I Jahun

Ita wannan waka malam Sulaiman I Jahun ne ya rubutawa wata budurwarsa, a lokacin da suke karatu a jamiár Bayero ta Kano. Bai dai nuna lokacin da yayi ta, bai kuma nuna ko wacece yake yiwa wakar ba. Ga dai wakar.
1] Me zan fada ne wanda zai gamsar da ni
Na sifanta kyanki gami da halayenki.

2] Kyawo na mata dai kina da guda Dubu
Ga jiki da hali ba irin mai naki.

3] Kirar jikinki takan saka ai zautuwa
Kana irin dadin karin bakinki.

4] Lafazi da taushi, kana gashi a kammale
Wallahi ban gajiya da saurarenki.

5] Taushin jikinki kamar dadai ba ko kashi
Kamshi da santsi ba kamar labbanki.

6] Ruwan idonki idan mukai kallo biyu
Sai in kamar in nutse in debi na wanki.

7] Haskensa yafi wata daren sallah fari
Gashin girarsa kamar ciyawar tafki.

8] Abin kamar kullum kina sa tozali
Don kyalkyalin manyan idanun naki.

9] Gashinki ga santsi, abin kuma ga tsawo
Sannan wuluk! da baki, bakin hankaki.

10] Naso in sa kaina ciki inyi lif! da ni
In dunga numfashi ina shafarki.

11] Ki kadan ido in gano fari, in gano baki
Ki kadan, ki tsinkan yau da alámarinki.

12] Goshinki wani Zara yar mowar wata
Haskensa ya wuce alfijir goshinki.

13] Zancen dabiá ko a birnin Sakkwato
Aka reni ya, halinta bai kai naki.

Bege Daga Farfesa Bello Salim

Ban taba buga wakokin soyayya ba a wannan zauren, wannan ya faru ne saboda rashin samunsu akan lokaci, to cikin yadda Allah nayi saá na samu littafin Farfesa Bello Saíd, maisuna DAUSAYIN SOYAYYA. Wanda cike yake da wakokin soyayya. Acikin littafin ne na tsakuro muku wannan waka, da Farfesa Bello Salim ya taba rubutawa wata budurwarsa, tun cikin watan Maris na 1977. Wato kusan shekaru talatin da biyu kenan. Bai dai bayyana wa yayiwa wannan waka ba, to amma ya fito da tsintsar soyayyarsa ga wannan baiwar Allah. Ga dai wakar nan.

1] Kin tambayan wai shin me yakan dame ni ne?
Kullum ina zugurum gaban hotonki.

2] Kullum in zauna sai tunani barkatai
Magana kadan sai na kira sunanki.

3] To zo ki zauna zan gaya miki gaskiya
Domin kisan ni bani son in rufe ki.

4] Zan tambayeki ki zayyana mini zahiri
Kin san sifa ta jiki da halayenki.

5] Ko kin sani saurari nawa batu ki san
Nine madubin gane siffofinki

6] Idanuwana sun zamo taga gaman
Ta cikinsu zaki gano irin kirarki.

7] Zan dan bayanin kanki, fuska har wuya
Gangar jiki, ya zuwa ga yan yatsunki.

8] Zan fayyace siffar jikinki gaba daya
In na gama in hado da halayenki.

9] Yawa da santsi, ga tsawo kuma ga baki
Sheki, suna nan duk a gashin kanki.

10] Kuma dubi gashi naki mai daukar ido
Tamkar gilashin nan dake hannuna.

11] Idanuwanki suna sihirtar dan Adam
SEXY Bature kan canewa idonki.

12] Duk wanda yai arba dake ya ganesu to
Sai zuciya tasa ta taállaka gun ki.

13] Hanci da kunne sunyi das! sun zaunu ras!
Kowa ya gansu ko dole yai shaáwarki.

14] Godewa Allah Jallah Sarki Rahimi
Don mustadaá ne gama bakinki.

15] Wuyan barewa shi mukan ce na da kyau
To ai barewace ta kwaikwayi naki

16] Sauko kadan don ki nazar ki yi bincike
Niíma ta Allah wadda ke kirjinki

17] Cikinki shafaffe abin shaáwa kamar
A ce hatsi baya shiga hanjinki

18] Kuturinki zaunanne gwanintar haliku
Shima kawai yasa mutum begenki

19] Cinya da sharaba sumul sun mulmulu
Yannan ki gode Jallah wanda yayi ki.

20] Taka a sannu sarauniya kiyi rangwada
Dan kyan dake sawunki har yatsunki.

21] Zan bar batun kirar jiki zan dakata
Don banda kalmomin siffanta jikinki.

22] Sai dai in gode Jallah sarki Wahidun
Da ya ban idanu har na samu ganinki.

23] A takaice yanzu ki dakata kuma kiy kawai
Saurari sharhina ga halayenki.

24] Hakuri a gunki da hankali kuma ga natso
Tamkar ace mata su zo Kwas gunki.

25] Saurin fushi, tsiwa, fada ko yaudara
Ba ko guda a wajenki gandun kirki.

26] Wadanga siffofi da nai zance bisa
Su sunka sa kullum nake begenki.

27] A ina kike jin zaá san mace kamila
Mai kyan sifa, sannan da halin kirki?

28] Ko an nutsa, an bincika, an rairaye
Sai anyi saá zaá san tamkarki.

29] To shi yasa abadan a kullum safiya
Ni banda tasirin da ya wuce naki.

30] Kuma godiya kullum nake gun Rabbana
Sarkin da yai ikon in ganki, in soki.

31] Kana inyo roko garai Shi mai duka
Yasa ki kaunaci Bello da mai sonki.