Allahu shi bani sani da basira,
In yi yabo bakin ‘karfina.
In yabi Sidi Muhammadu Bawa,
Mai hana sauran bayi ‘kuna.
Yi dad’in tsira Allah da aminci,
Gun manzonka dare har rana.
Da alolinsa da kau sahabbansa,
Da mu mabiyansa dare har rana.
Baicin na cika wannan kalma,
Begen annabi manufana.
Yabon manzon Allah addini,
Shi yafi dace irin sib’ina.
Yabonka Muhammadu nan na fi auki,
Ba ruba bad a d’an damana.
Ba ni da mulki ba ni da aiki,
Begen annabi ne nomana.
Ba ni da guru ba ni da laya,
Sunan annabi ne shingena.
Ba ni da k’arfi ba ni da k’arfe,
In koma Maka ne fatana.
Abin nema a garemu ziyaran,
Wannan d’a mai dad’in suna.
Mai kyau, mai natsuwa, mai kunya,
Sannan ga shi da dad’in suna.
Ina k’aunannka Rasulillahi,
Haske mai dushe zafin rana.
Ina son mai k’aunanka Muhammad,
Ko ya auri d’ayan matana.
Ina kyaman mai k’inka Muhammad,
Ko shi yai mani ragon suna.
Tun da a kai shi yake mashi gandu,
Bai fasaba walau d’ai rana.
Da rana yawan azumi, a darensa,
K’iyamullaili shike duk kwana.
Shirunsa, tunani, kalmominsa,
Gun jama’a wa’azi ko izna.
Allah y a ce ma Ibrahim,
“Na sanya ka maji dadina”.
Ya kuma ce ma Rasulullahi,
“Ka fifita cikin bayi na.
Kai kafi kowane bawa girma,
Don kiwonka da alfarma na
Ba mai daraja tamfalka Muhammad,
Don kiwonka da haddodina”.
Albishirinku masoya Allah,
na ga Amina cikin barcina.
Wadda ta haifi Rasulullahi,
Watan Ramalana a barcin rana.
Na nemi ta sami zama mu yi tad'i.
In cusa shi a wak'ok'i na.
Ban samu ba sabo da lalura,
Don shi na koki irin halina.
Nai fata tahowar fa dalilin,
In koma Maka ne wata rana.
Ko ya zamo shine sanadiyyar
In ga Rasulu cikin barci na.
Ya ce "Bila maza ce ma Aliyu,
Namangi ku zo inuwar sorona".
Mu zo mu ishe yai zaune a zaure,
Ga sahabansa suna kallona.
In gurfana a kan darduma
Hairul Halki yana duba na.
Ya ce mani "Zauna daina sagwangwan,
Kai mani hira kana garkana".
In ce madallah Rasullilahi,
Yau na sami abin nema na.
Tun da na sha inuwar soronka
An warke mani cutocina.
Kuma tun da na zauna cikin sahabbanka,
Yau nai zaune cikin birni na.
Mashigin birnin ya tsarma yak'i,
Ya kuma tsarma hararan arna.
Allah shi ya yabe ka da fari,
Kafin in yi da baubaucina.
Na kuma iske mutanen kirki,
Sun yi da Arbi gaban Hausana.
Kai a ka baiwa Liwa'ul hamdi,
Da tajul izzi da Babban suna.
Wanda ya sa sammai suka zauna,
Taurari da wata har rana.
A kai ma k'asa tuhuwa da yabanya,
Yai ma ruwa a kwari magudana.
Ina k'aunarka Jakadan Allah,
Son, ya zamne cikin bargona.
Don haka in halshe ya yabe ka,
Sai in ji shi cikin kwanya na.
Aka kwab'e halshe na da yabonka,
Har ya zame mani filin gona.
Tuntuni sunayenka Muhammad,
Sun shuka mata baitotina.
Gonar ta yi gamo da yabanya,
Kowa na sha'awar nomana.
Don haka ne fa mutanen kirki,
Kowa ke sha'awar nema na.
In kwana a bene kan darduma,
In sha in ci ana zak'ina.
Ina rok'onka Rasullullahi,
Sa hannunka rik'en dama na.
Ka ce mani "Yadda ka so ka samu,
Yau dai ga shi kana soro na.
Ko yaushe aka tsaida halitta,
Al'amarinka yana hannuna".
Ni na ci albarkanka Muhammad,
Ba ni d'ai ba da 'yan bayana.
Kai tsaye kai yak'i da juhala,
Har muka san darajojin juna.
Ka ci garin yakin kafurrai,
Sorayensu ta komo gona.
Babu ya kai a cikin ta halitta.
Ba za ai shi ba ko wata rana.
Allah shi yi tsira da aminci,
Hal abada a dare har rana.
Kar su gushe ga uban Ibrahim,
Mai zance da wata har rana.
k'asa na alfahari da zamanka,
Tun da ka mai da gumaka gona.
Barzahu na fahari da zamanka,
A tun da ta zammaka soron kwana.
Toya matsafa ratattaka gunki,
Baban Fadima ga hannu na.
Sa hannunka mafi albarkar,
Hannaye, ka rik'e dama na.
Ka ce mani "Yadda ka so ka samu,
Yau banbad'o kana hannuna.
Uwa da ubanka da kakanninka,
Da matayenka kuna hannu na.
Da 'ya'yenka da jikokinka,
Da mai k'aunarka kuna hannuna.
A da Iblis ya cika a yak'i,
Amma yanzu kana hannu na.
Na kwato ka da yardan Allah,
Na jefaka cikin barwana".
Uban Bila baban Salmanul,
Farisa ka ji irin fata na.
Zababbe a halittar Allah,
Kyakkyawa ga sifa har suna.
Mai k'aunar cutarsa ta warke,
Shi ta yabonka dare har rana.
A yabonka Muhammadu ni ne sarki,
Na kau san da mafinfinta na.
Sarauta ta begenka Muhammad,
Ba fahari ba wuni har kwana.
Na gaisheka Rasulullahi,
Amma ka ji irin fata na.
Ran saukar ajali ku halarto,
Har sahabanka wurin gawa na.
Sui mani wanka, kai mani salla,
Har ku had'a ni wurin barci na.
Da albarkanka na Abdullahi,
Da nana Amina nike fata na.
Ka yi min addu'a ga ta'ala Jalla,
Shi gafarta mani aibobi na.
Shi rahama ga musulmi d'urran,
Ba da fari, wuni har kwana.
Ya rufe mu da annuran begenka,
Annabi ka ji irin fata na.
No comments:
Post a Comment