Acikin shekara ta 1906 ne, Turawan mulkin mallaka tare da sojojinsu dauke da muggan, makamai suka yiwa birnin Hadejia tsinke. Inda hakan tayi sanadiyyar gwabza wani mummunan fada tsakanin Turawan mulkin mallaka da kuma Jaruman kasar Hadejia masu gwagwarmayar kwatar yancin kai. Hakan yayi sanadiyyar yiwa mutanen Hadejia kisan kiyashi, inda aka kissima cewa, dubban mutane ne suka rasa rayukansu a sanadiyar hakan. Babban abin lura shine, dukkan wadannan dubban bayin Allah da suka rasa rayukansu, sun rasa ne a rana guda, cikinsu kuwa harda Sarkin na Hadeja a wannan zamani, Wato Sarkin Hadejia Muhammadu. Wannan waka ta tattare dukkan abinda ya faru a ranar, ta kuma yi cikkakken bayani gameda yadda Shahidan Hadeja suka jajircewa abinda suka kira, bautar dasu acikin kasarsu. Koba komai, wannan ya nuna yadda yan Afrika suka dauki yancinsu da muhimmanci. Da fatan Allah ya jikansu, nake cewa ga abinda ya samu;
Allahu sarki Shi kadai yake Wahidun
Sammai da kassai, Jallah bashi da kishiya
Shi ba fari, shi ba Baki ba Ubangiji
Ba ja ba, ba alkashi ba, shi ba rawaya
Ba sake-sake ba, ba kamar yarani ba
Shudi da kore Jalla bashi da mai kama
Zatinsa baya tattara, ba rarraba
Da kawai da motsi babu yayi ko daya
Sarkin da ba na biyunsa, ba na ukunsa
Fahami basira zani begen shahidi
Ranar Talata mun ga tashin duniya
Ranar Muhammdu yai shahada zahira
Yayi jawabi ya cane shi bai gudu
Shi bashi mai kamu a daral duniya
Rago akan kora, a bishi a kam masa
Amma sadauki ba gudu sai faduwa
Sarki Muhammdu yai jawabi ya cika
Shi bashi mai kamu ya ja shi ya tunkiya
Dan Mele Sarkin Yaki shi kuma ya cane
Muna da rai Sarkinmu baya kamuwa
Ma'aji Salihi yai jawabi ya cane
Mun dau shahada zahira bahakikiya
Manya da yara duk shirin yaki su kai
Kowa yana wanka, yana kuma Alwala
Kowa yana sallama cikin ahli nasa
Sun sa gabansu a lahira ba dawaya
Jama'ar Hadejawa dada duk suka hallara
Kowa yana ce "yau ma zama shahidai"
Shi bai kamar tsoro, balle ya razana
Kan ya ije ma babu kingin hamzari
Ajali idan yai babu kwana duniya
Kai dai zamo kullum shiri duk safiya
Shi bai kamar tsoro, balle ya razana
Bai san gudu dan Garba sarki jarumi
Mutuwa tafarki ce kowa zaiyi ta
Kullu nafsin kowanne ya dandana
Aka daura sirdinsa ya hau bisa ya tsaya
Yace "mu dau himmar shahada Zahira"
Sarki Muhammdu bashi tsoro ba gudu
Allah, Ma'aiki su yake tsoro kadai
Hauninsa Linzami mayani ya rike
Damansa tsabihi salatin musdafa
Dan maikaratu, tudun kasa ba dawaya
Dan Garba, jikan Sambo sarkin adali
Duka mai shahada auwalinsu Madacima
Suka barace shi da fari, ya mutu shahidi
Farkon hawan yakin Talata kun jiya
Galadima, Sarki Haruna sune awwali
Alkali, Sarkin Yaki, Kaura Ahmada
Sarkin Arewa sun kaje can tsaye
Suka jeru har da nan kofar gabas
Kafin su zabura mairuwa ta tarda dasu
Kasan Igwa, da fari aka yamutsa
Doki mutum na faduwa ba lasafi
Igwa tana tashi madafa na zuba
Yau sai ta Allah babu Sauran shawari
Sadaukan Muhammadu basu tsoro ko gudu
Sun dakace kofar gida sai faduwa
Sabo, da jikan Tete su harbi suke
A nan a kofar fada duk suka tuntsure
Firyan Hadeja, shi da Bori na Salihu
Kofar Gabas suka fadi duk sun tuntsure
Ai babu mai mutuwa gaban ajali dada
Kan surfa gero, kan daka, wasu kan fita
Hukunci idan Allahu yayi nufinsa
Ba mai tsimi balle dabara ko daya
Tamkar kamar inuwarka baka guje mata
Kan kai gudu ta bika, kai tsai ta tsaya
Attas yana yawo kamar burduduwa
Tamkar zubar wake, acan a masussuka
Ya ratsa soraye, ya rada katanguna
Kamar kabewa, ko kamar tunfafiya
Ya sha zarar Soro, ya ratsa katanguna
Kago da zaure sun fi karfin lasafi
Tsarnu da kurna hakka sa durumi dada
Yansa dabinai, cediya da itatuwa
Rannan musulmi munga kayan al'ajab
Allah ma'aiki su kadai ne magani
AbdulWahabu baka yana hannu nasa
Attas ya samar, nan ya datse tsirkiya.
domin karin bayani, sai a nemi litttafin Dr Haruna Wakili, na Mummbayya House Kano, maisuna Zuwan Turawa Hadejia.
7 comments:
ASSALAM NAYI FARINCIKIN GANIN WANNAN KOKARI DA KAYI ALLAH YA SAKA AMMA NI,ABINDA NAKE SON SAMU SHINE TARIN HADEJAWA DA YAKIN DA SUKAYI GABA DAYA,WATAU,YAKIN SU NA GIDA DA KUMA TARAWA.
assalam gaskiya na jinjina maka da wannan kokari da kayi,amma ni nafi son na samu tarihin hadejawa da yakin da suka yi gaba dayan su.
karfarryish
[url=http://healthplusrx.com/migraine]migraine[/url]
KambillianO
Wannan waka ta raunana zuciyata. Lalai bakaramar wahala akasha ba a kasar hausa lokacin zuwan turwa. Wannan ya can-can ci yazama darasi a azuziwa, domin bai dace ace mutane basu sanbe da irin wayannan dimbin tarihi
I've read some excellent stuff here. Definitely worth bookmarking for revisiting. I surprise how so much attempt you put to make such a great informative web site.
Here is my weblog; Bucket truck
My page - used bucket trucks
I’m not that muсh οf a online гeader to be honest but уour sites really nicе, keep
it up! I'll go ahead and bookmark your site to come back down the road. Cheers
My blog post: how to make money uying and selling cars
I lοve rеading an article that wіll make mеn and wоmеn thіnκ.
Also, many thanκs fοr allowіng for me tο сomment!
Нere is my site search engine optimization dallas
Post a Comment