Sunday, March 25, 2007

Wakar Tsuntsaye; Daga Ahmadu Dan Matawalle

Amshi: Rabe! Ribabe!! Bamu jawabin na Garba mai Yammata

1] Tsuntsayen gida da daji, sun hadu sun girka shawara, Jimina itace gwamna tace zata yi musu Sarki.

2] Agwagwa aka bai sarauta, sunce wofi marar karama, yar banza mai kama da gammo, bata da siffar da zasu bita kazama.

3] Hankaka ka bai sarauta, sun ce su dai ba zasu lamunta ba, sun sake shawara suna cewa 'Danfashi' bazai sarki ba.

4] Aka bai Mikiya sarauta, sunce wannan in ta samu mulki, ita wa zaya ganta, sai ko mushe ya fadi zaka ganta da sauri.

5]Borin-Tunke ka bai sarauta, tsuntsaye duk suna ta mamaki, sai wannan ya dubi wannan, wai dan sun sami Shugaba maigirma.

6] Da Shaho yazo da kansa, tsuntsaye sai suke ta mamaki, sai wannan ya dubi wannan, Shaho yazo shi babu sauran wargi.

7] shaho ta bai sarauta, tsuntsaye sai kuzo ku kai caffa, Borin-Tunke ka dau jakarka a hannu.

8] Fadawa kuzo nadin Shaho, Zabin dake cikin dawa, sune yan figini mabusa Sarki.

9] Zalbe ka baiwa mai Kakaki, yan doka tambura ne Burtu.

10] Zagage ka baiwa Balbela, Zakaran Kekuwa kasa yan kurya

11] Ga Tsintara tana algaita, ga Hasbiya tana buga Jauje

12] shaho yana jawabi, Borin tunke ka bai Waziri, Gauraka ne Ciroma mai alfarma.

13] Kuma Tuje ka bai Galadima, Madakin gari ka baiwa Dinya.

14] Sarkin Bayi Shamuwa ce, sannan Sarkin dawa Kitsawa ce, Alkalin gari ka bai Kahuhu.

15] Marke ka baiwa Yari, Sa'annan angulaye kurhu na banzar gari madeba kashi.

16] Sarautar da zata dace!! Farin Barugu shi ka baiwa limami, sannan na baku labari, kuma sannan Kadafkara shine Ladaninsa ko dare ko rana.

Wanda ya rubuta, shine ".........Sahibul BBikru, sahibul Fatyatu, mai yanmata" Ku bini bashin sharhin.
Muhammad Fatuhu Mustapher

Mulkin Audu; Daga Abdullahi Gwandu

Abdullahi Gwandu, ko kuma Abdullahi bin Fodio, kani ne ga mujaddadi Usman bin Fodio. Masani ne, kuma marubucin wakokine, ya rubuta wakoki da dama, cikinsu harda wannan da zamu gabatar, da kumawakar cin birnin Alkalawa da insha Allahu itama nan gabazamu kawota. Sai dai wasu baitocin sun karye, saboda dadewa, da kumarashin ma'ajiyi nagari. Hakan yasa dole na kirkiri wasu baituka, misali a Baiti na23, 33, da kuma na 40. Ga dai wakar yadda take;

Mai dare duk da safiya
Mai sarauta da gaskiya
Rabbu tsarshe mu ghashiya
Mun yi aiki da sunkuya
Mai sarauta da mallaka
Kad da iko da daukaka
Wanga bawa ka tsarkaka
Nashi haush ga zuciya
Jalla kai munkawakkala
Al'amurranmu duk kala
Don ka fisshe mu Dan'bala
Tunga daki na duniya
Mun sake rai shika hawa
Harzunabbanmu sun yawa
Ga tubanmu yai nawa
Mun yi tsufada ma'asiya
Don nabiyunka mai hima
Mai darajjaga mai sama
Wanda yak kai ta kau sama
Bani afuwa da afiya
Mun sani wallah zamuna
Randa mutuwa tafar mana
Babu shakka ta ram muna
Namu matada dukiya
Kaitammu radda anka ce
Yau ina wane? Ya wuce
Duk abinai a ya gushe
Duk magada su sha miya
Randa ranakka tazzaka
Sai ka mance da da jika
Dukiyan naka kaf faka
Bata fansalka ka jiya
Masu jiya su tunzura
Babu iko ga ko daya
Sai su zauna su sa ido
Maigida ya tsakar gado
Bashi murnar abin ado
An fakai yau da tsintsiya
Sai ladama ga ko ina
Sai kira har su jinjina
sunyi taro na adana
Har su kai inda kats Tsaya
In nagarta da sunkuya
Duk ka shaida su dai daya
Ga Nakiri da Munkari
duk suna kan ka sun tsaya
In Bakwai yayi kaddafu
Kai da tsutsa ka garwaya
Ran kiyama ana kira
Duk mutane mu tattara
Bamu so bamu faskara
Yau hukumci ga mai shiya
Ke kasa koma rariya
Duk amayo su ke jiya
Kad ki bar dai da danmaya
Zasu na yau wurin biya
Yau asiri ka bayyana
Kun taho duk da jingina
Wansu can sunka dangana
An nagirshe su sun kiya
Ga safun jinni su duka
Ga wuta ga mala'iku
sunka saka da mu tsaka
Yau ina masu mallaka
Masu iko ga duniya
Masu karfi da dukiya
Gamu dai sai mu tsaitsaya
Yau sarauta ga mai niya
Ga kasa bata takuwa
Ga mu rana ga kwalluwa
Ga zufa harga dudduge
Har kafafu su zuzzuge
Babu bance bale lage
Babu ko masu dariya
Ayi hukunci a rarraba
Kafiri duk a azzaba
Kaji ranar bugun gaba
Mumini duk wurin zama
Nashi dubashi dawwama
Nan ga sarki madawwama
Jalla mun roki gafara
Tun gabanin shiga sara
Don ka sha she mu kausara
Don nabiyunka mahiya
Bamu ceto na Annabi
Rabbu shashe mu salsabi