Wannan dai itace wakar Tabarkoko, wadda sarkin Zazzau Aliyu Dansidi ya wallafa. Wakar dai gugar zana ce, ko kuma ince shagube da bai nuna wanda yake yiwa ba. Amma ana zaton ko yayi tane domin yiwa fadawansa shagube, game da yadda suke tafiyar da rayuwarsu.
Aboka zo nan mu bata
ka dubi dan dai ga wata
wada daban da batta
Haske na rana da wata
Ba zasu zam daidai ba
He dubi dai tsettsewa
Ya samu kifi a wuya
shina zaton babu kaya
Inta kafe mai ga wuya
ba zasu debe mai ba
He dubi dai irame
Can tai gida a rame
Can dauri kau ta rame
kyaushe mijin Irame
gallonsu ba zaki ba
Abin ga dai gama na
kare shi tono magana
zai iske kura a hana
ba dun akwai wata magana
da bai fito rannan ba
Ai ga fage ga doki
Noman fako ba taki
ai maganan ta sake
da dan kare da na doki
ba zasu zam daidai ba
Mu namu ga ta da taki
babu biri ba zaki
barde dubu mai doki
da zamanin kai taki
da bamu samu nai ba
Saura garin ya waye
duk kokuwan tai kaye
Damu ga yan tawaye
da masu da da maye
zamansu bai zam dai ba
Karya take zabira
bata zama gurara
Iska daban da sarara
matar maza da bera
kudinsu bai zam dai ba
Na ganshi duk ya kwabe
Yayi tabo ya tabe
yayi bago ya rabe
Neman jini ga babe
Ba za'a samu nai ba
Zo ka taba dai ka jiya
Yau muke koko jiya?
Haure ka ciwo ijiya
in yayi sai ayi jinya
ba za'a debewa ba
Ko ka iso, ko ka tsaya
Taunan aya ko ka iya?
Amale cimansa kaya
Jaki, da sa, ko akuya
Ba zasu taunawa ba
Kaya ga Rakumi shike
Takarkari sai taiki
Saimo akanwa taki
Tsaiko akanwa daki
bukka ba ta dauka ba.
Makaryata, mahassada
basu iya komi da guda
na yanzu ba ko da na da
tara su dai duk ka gwada
ba su zamo daidai ba
Babba da jaka ya zaka
Yana bidan kifi tsaka
gulbin da dorina tsaka
Gefen kadanni ya saka
kafansa ba zai kai ba
Yada guda ka dau guda
Duk ka fasa su ba guda
hanya mararraba guda
gaba-gaba akan guda
cikinsu bai ba daya ba
Ga kutu ga Tabarkoko
Ga dole-dole tai hako
ni naga tana ga fako
kai mai bago shiga sako
Wurin ba'a zo mai ba
Kwaddo ina kadangare
Naji kafarsa ta kare
ya bar diyanshi gangare
in yayi nan sai a tare
ni ban gano zai kai ba
Ko kaga mai digirgire
wuya awa gadar zare
Takuna zance hantsare
da zamanin bakin zare
da basu sa riga ba
Ga tsada mai dan tashi
kullum ta dau albashi
ba ta ci bata hana bashi
ran da safiya tai fashi
ba za'a koka mai ba
Ga wani tantalwashi
na biyunsu mai kan bashi
na ukkunsu bashi da nashi
Da dai ana tuna bashi
da basu sa riga ba
Nazundu mai zaka fada
kullum ka gana da rada
roko awa dan makada
a baka bashi a dada
ba zashi fasawa ba
Ga wani wai shi ya iya
yaje ya jawo igiya
ta nannade mai a wuya
yana kira da waiwaya
ba za'a debe mai ba
Shin me ya samu shamuwa
na ga tana ta dimuwa
naga ruwan da kainuwa
ba dun kasan da kaguwa
da bata sauka anan ba
Da kunkuru da bushiyta
halinsu dai noke wuya
ga zamani na waiwaya
da zamanin mazan jiya
ni naga da basu kai ba
Debi yawa, sam ma kadan
yanzu yawa ta zam kadan
a hankali kadan-kadan
Gidan yawa kan yi kadan
Abinga ba banza ba
Nai muku waka ta batu
ku zo ku nemi yan batu
awa su lugegen batu
tara fasihai na batu
ba zasu ganewa ba
Mai wagga waka ta batu
Ali Amiru wan Shatu
Shine abokin Warqatu
Dadai da sirri na batu
Da bashi boyewa ba
Allahu shi yai mu duka
Baki fari yai su duka
Shudi da Korensu duka
Da Ja da Rawaya duka
Shi dai kayi ba wani ba
Zama fa shi dai ya iya
Shi yo mutum shi tafiya
Wadansu ko shi yi su tsaya
Shi yai itace da kaya
Nufinsa ne ba wani ba
Shi yai dawa da karkara
Shi yai dawa da karkara
Shi yai kwai, yai zakara
Yai zabuwa, yai fakara
Shi ad damu ba wani ba
Bautanmu dai hasana'u
Zam haufu, duk dada rija'u
Ku lura ko asma'u
Nisa'u masu gina'u
Sha'aninsu ba karko ba
Asma'u an sanki da dai
Halinki ki ne ko can dadai
Shirinki kullum na kwadai
Maso biyu,bashi da dai
Batun ga ba karyaba
Ywaita rokon Jalla
Ka wakkale ga Allah
Ka zam kula da Salla
A baka ni'ima walla
Anan da can ba waiba
Muyi zikiri da salati
Mu karkare afati
Gobe mu san najjati
Ga shugaban hajati
Muhammadu bawani ba