Fatara mai sa a lalace
Ta ki yarda ma kasan rance
Yinwa mai kai maza kwance
Ta kashe ba sai da aibi ba
Yau Lebura ne kamar Zakka
Aiki rani zuwa kaka
In gwamnati zata sa doka
Lebura baza su karya ba
Aiki kullum cikin taro
Ana abu sai kace horo
In dai Allah ake tsoro
Da lebura bai talauci ba
Bamu san haka zaku fara ba
Kuyi alkawari ku karya ba
Kaya ba za shi zango ba
Lebura bai bada iko ba
Jirgin sama fankamin wofi
Mota bata zuwa rafi
Ta nutsa ta haya ana tafi
Wannan bamu fara samu ba
A hake titi a sa kwalta
Mai mota yai gare keta
Wani Lebura bai da ko mota
Amma bazai ji ciwo ba
Da mun kare ace sauka
Ayi ma ham don a ruda ka
In ka ki gudu a take ka
Ko yau ba za'a canja ba
A dauki diga a wurgata
Kan tsandauri a sara ta
A tara kasa a kwashe ta
Mota ba zata huta ba
Wannan magana ku duba ta
Aiki kullum kamar bauta
In lebura su ake cuta
Allah sa baza su tabe ba
Kai gidan kwano kana yanga
Ai lebura in yasa targa
Kowa ya fito ya zazzaga
Ya dade bai hangi kwanon ba
Ga katako a jejjera
Shima kwanon a tattara
A bar ka dashi ace dora
Mun san ba zaka dora ba
Dubi tara gyada kamar Dala
Kauye da cikin Kano Jalla
A daura guda kamar hula
Amma ba zata goce ba
Kaji nauyin goro huhun nan
Daya ko daukar guda sannan
Ga wagunu fankamemen nan
Lebura ba za su kasa ba
shin Lebura ko waliyyi ne
Ko jikin da ice da karfe ne
Ko dan lada suke yi ne
Ba don karfen bature ba
Icen tunba a sare shi
Ai katako a tsage shi
Wane ne zasu tsage shi
Kan lebura baiyi aiki ba
Ai lebura sai a gode ma
A tara kudi a mika ma
In ba don kai ba tun da ma
Aiki ba zai yi kirki ba
Jirgi da muke gani babba
Ba za ya zuba ya dauka ba
in lebura baiyi lodi ba
Kaya ba za shi zango ba
Ran nan da na dauki mota ta
Muka je yashi ya kama ta
Da lebura sunki tura ta
Don ni ba zata motsa ba
Jirgin ruwa in yazo kwata
Da lebura za su sa keta
Suki yin aiki su kwankwanta
Shi ba zai je ya sauke ba
Tun sanda muke zuwa kanti
Da lebura dan dako Mati
Wani mummuna gwanin datti
Amma ba'a fishi aiki ba
Ai mai amalanke jigo ne
Babban kura ko gwamna ne
Mutum ko shi minista ne
Bazai iya raina lebo ba
In za'a daka asan gari
Daukar kaya ana zari
Kaga lebura har yana tari
Amma bai fasa aiki ba
Du lebura yan kasa ne ku
Ni banda nufin in raina ku
ku amince min cikin ranku
Da nufin ba zamu saba ba
Nan zamu tsaya mu saurara
In lebura su ake kwara
Zamani zai yi wo kora
kowa ba za ya tsere ba
Kai lebura me ya dame ka
Ga Lawan ya zo ya nuna ka
Da nufin a fahimci aikinka
Amma ba don a raina ba
Kullum aka samu mai sona
Zai wo sako zuwa guna
kulkul acikin Kano tona
Lungu nake ba a titi ba
Kowa ya karanta waka ta
Sha Takwas muka tsara baitinta
Don lebura mun ka tsara ta
Amma ba don minista ba
No comments:
Post a Comment