Sarkin Zazzau Alu dan Sidi, shine sarkin Zazzau na farko da turawa suka fara nadawa, bayan sun ci kasar Zazzau. Ya mulki kasar Zazzau, tun daga 1903 zuwa 1922. Ya samu matsala da turawa, domin banbancin ra'ayi, wanda hakan ya sanya suka cire shi. Fasihin marubucin wakoki ne, kuma zamu kawo muku wakokinsa da dama. Da yake cikakken Batijjane ne, wato mabiyin darikar Tijjaniya, shi yasa muka fara da wakarsa ta Shehi Ahmadu Tijjani.
Na sha ruwan bege dada ni bani ji
Da gani ba, sai na zo gurin Tijjani
In na fito can zani nan in dawayo
Ni zani birnin Fas wurin Tijjani
kai mai zuwa Fas dakata mani zani nan
In yo ziyarar Ahmadu Tijjani
Shehunmu Ahmadu anka ba al-Fatihi
Budi Lima ughliqa sai Tijjani
shi anka ba al-Khatimi ga lima Sabaqa
Kuma Nasirul Haqqinmu sai Tijjani
Bil haqqi wal hadi kasan shi anka ba
Wa ila siratul mustaqim Tijjani
Wabi alihi ya Rabbi haqqa li Qadarihi
Miqdarihi ya al'Azim Tijjani
Sabkakkiya take inda Rabbil Izzati
Ita anka saukowa Wali Tijjani
Domin wadanda su kai shahada ran Badar
Don Makka duk da Madina don Tijjani
Ya Rabbi don Taurata har Injilu duk
Da Zabura har Furqanu don Tijjani
Domin safa don Marwa don Hajaral lazi
Sunansa Arfa, Rabbu don Tijjani
Domin Badiha Rabbu domin Zamzamu
Da Mukamar Ibrahimu don Tijjani
don hajaral Aswadu wanda kaba alkawal
Ran tambaya kalubale Tijjani
No comments:
Post a Comment