Tuesday, March 27, 2007

Wakar Keke; Ta [Dr] Aliyu Namangi

Muna shukura ga Rabbal alamina
Da alherin da yai mana ba kadan ba

Muna murna da mulkin ingilishi
Zuwan da sukai kasarmu ba tai tsiya ba

Zama zamaninsu ne aka zo da Faifa
kudi ba masu nauyaya aljihu ba

Dada zarafinsu ne aka zo da jirgi
Kaje Makka ba da tashin Hankali ba

Sa'annan gasu Babur, ga su Mota
Da farko da can bamu san da su ba

Izan tafiya ta faru ka nemi mota
Izan jirgi ba kui daidai da shi ba

Izan kuwa babu Jirgi babu mota
Ka je da kafarka ba keken tsiya ba

Banni da Basukar Ho! Dan jidali
shakiyyi ba abin Babba ya hau ba

A Dan-Mahawayi nih Hau sai ya barni
Tudun-Yakaji ban kawo gari ba

Ya bar ni da jin jiki da zama a turba
Da dai ko juma'a ba a je dani ba

Kudi tirmis! Na bashi Sule-da-Sisi
keke bai mani rangwame ko dari ba

Na ce masa "Basukur rika sawwakewa"
Yace "Malam hala ba ka sanni ne ba"

"Ina da tsiya biyar farkonsu fanca
Na kau buga bindiga ba mai wuta ba"

In babbake zuciya, in tafi da sawu
Cikin daji kamar ba'a je dani ba

Muna tafiya kuma na fizge kaina
Mu fada kwazazzabo ni ban kula ba

Ina da ciki ana ce mai Kurumbo
Karambanin hawa baka saya ba

Hanjina kaca mai kama riga
In fizgo mai hawa ni ban kula ba

Tsiya na can mu je kan kadarko
Madaidaici in ce ba zamu hau ba

In hau bisa kafadar bari in zauna
Kamar mahayin dadai bai hauni shi ba

Su kai kadda da Sale akan kadarko
Sai yace "Haba Sale bazan yadda kai ba"

Dadai suka wantsala hakan kan ya kwace
Ashe ba Sale ne a cikin ruwa ba?

Ya bishi ya bangaje ya buge yana ce
"Azo a gani idan ban yada kai ba"

Malam Sale saida ya tube riga
Yasa kaga Sale har bai sha ruwa ba

ya tashi ya hau tudu keke ya bi shi
Da rigar Sale keke bai sako ba

Su malam Sanda duk suka tar ma keke
Da ban magana yace ba zai saka ba

Ya ma rantse da jirgi har da mota
Ba zashi sako ba in ba'a sa wuka ba

Malam Sanda wai sun shirya da Keke
Wai yana kaunarsa ba domin tsiya ba

Yace "Haba malami kamarka
Bazan iya yadda babban malami ba"

Izan dai zaka hauni ka tara riga
Da wando ba ka hau ni hawan isa ba

Ya tashi hawa bai tattara ba
Ya fizgo malamin ba a jinjima ba

Ya yasai nan da nan a tsakar gidansa
Cikin matansa tun ba a kai dabe ba

Yace "Bari nai kure yashe ka malam
Dama ban kai ka bakin kasuwa ba

Bana son na yada mutum na kirki
Izan ba inda za ai dariya ba

Da motsa kararrawarka da kama burki
Ba zasu hana ni in jefar da kai ba

Yace masa "Bana kara hawanka keke"
Yace masa "ko adankiya ban kula ba"

Hawan da rashin hawan a gareni dai ne
Ban ga abinda zai cutar dani ba

Kamar tafiya ta sauri ko ta fizge
Baka je inda kaso nan da nan ba

Izan kazo ka hau ni ka bani iska
Na sha, ba inda ba zan je dakai ba

Ashe ba mai hawa keke ya more
Izan ba wanda ya iya zanzaro ba.

11 comments:

Abdulaziz Abdulaziz said...

Mal. Fatuhu, wannan wak'a dai na ga an yi maganarta a cikin gabatarwar littafin "Wak'ar Furan gero da tsarabar Madina" na Mal. Aliyu Namangi amm ba ni da ita zan kuwa so na sami littafin wato, "Wak'ar zamani"

Anonymous said...

Tare da Sallama, Lallai Malam Fatuhu wannan ba karamar hobbasa ba kayi wajen yunkurin adana mana wadannan wakoki da suke neman bacewa. In Allah a yarda zamu yi kokari daidai gwargwado domin raya wannan zaure. Ina da wasu ire-iren wadannan in Allah ya yarda zan aiko maka in hali yayi. Allah ya saka da alhairi.
GABA DAI..GABA DAI 'YAN AREWA !!!

MAGAJI GALADIMA

Anonymous said...

Ill know that U write a day???
I hope U are going to traslete all I cry I cry I know only this Kogin Rahama
Hanya kaha bi so sai
Kamar bayan macij ne
Wata rana na gani
Wani baban macij
Yana bi hanya a ba yan ka
Kogin Rahama
Mutumun famfo mai girma
Suna rara waka,kururuwa kuma
Suna aiki da launin waka
Famfo yana tura ru wa
Don jirgin kasa a tasha
Kogin Rahama
Itatu wa suna sharuwan ka
Suna da koren girma
Lokacin da ruwa ya tashi
Kayan banza
Da yawa da
Wadansu ita tuwa
Suna hau ruwa
Su ta fi da nisa
Kogin Rahama
Wani tsofo mai lambu
Yanna kai runsan ka
A gomarsa
Amfanin gona zai yi
Al barka so sai
Mun gode,da yawa
Don za mu ci
Mu ji dadi
Kogin Rahama

Unknown said...

Assalam,naji dadin samun wannan waka,domin inada kaset dinta amma wakar ta yanke.Allah ya taimaka.

Sadiq Maccido said...

assalamu alaikum, sunana sadiq maccido na rubutone daga malaysia. naji dadin ganin wayannan wakokin sosai na dade ina neman wakokin Dr Aliyu namangi. amma don Allah ka sa mana mp3 nashi koma saurara muyi down loading kuma thank.

Emzy Imam said...

Malam ka kyauta. Keep it up. MAHMOUD

musa umar said...

godiya muke da wannan gudummuwar

Aminu M.B Umar said...

Suna na Aminu M.B Umar. Na yi matukar farin ciki da wannan gudunmuwa a fannin Adabin Zamani.

bafillace said...

Fatuhul Ilmu, Ya kamata ka ci gaba da yauqaqa wannan blog.

Saddiq said...

Salaam INA Neman wakar imfiraji rubucacciya

Unknown said...

Slm. Allah yakara basira amma ina tambaya kan wani baiti kamar haka "gashi ka cutar da kanka sonkudi ya saka shirka da dubu milliya gareka randa kanmutu sai akaika......... "
Ina tambaya inane zansa wadannan baituka.????