Monday, March 26, 2007

Yabon Allah; Daga Wazirin Gwandu Umaru Nasarawa

Malam Umaru Nasarawa dai ba boyayye bane, domin a zamaninsa kowa yasan irin gudunmawar da ya bayar wajen raya adabin Hausa ta fannin wakoki. Ya rubuta wakoki da dama, wanda insha Allah zamu kawo su. Amma ga wanda bai san shi ba, to shine mahaifin tsohon gwamnan jihar Kaduna a zamanin soja, wato; Abubakar Dangiwa Umar. Wannan wakar dai sunanta Yabon Allah. Ga kuma yadda take.

Yabo gun Jalla daidai na
Garan kuma wajibina na
Na jin kai nai da yan nuna
Garan ya amshi roko na

Tutur! Na zam shukura
Ga sarkin nan da naiyi kira
Da sunayensa naiyi bara
Zuwa ga biyan bukatuna

Da farko duk abinda ni kai
Da fari dai salati ni kai
Ga Annabi duk abinda ni kai
Da shi nika fara wake na

Sahabbai nai da Alu duka
Gama sun taimake shi duka
Ina ko daulaminsu duka
Da aikina da horo na

Abokina taho ka jiya
Ina rokonka kar ka kiya
Ka samu guri guda ka tsaya
Idan ka amshi roko na

Tsaya gun Jalla dai ka fake
Da imaninka kar ka fake
Ka bishi ka togi inda shike
Mu dogara nan masoyi na

Biyar Allahu ta wajaba
Sana'a ta mafi riba
Tutur! Batu na bai da tambaba
Tsaya in baka shaiduna

Ruwa bana sun ka kai ga wuya
Har na rasa inda zani tsaya
Balle juyi, balle tafiya
Ganin am fara zunde na

Rawata an suke ta duka
Gama an dungushe ni haka
Ganin ta kai ni ag ga haka
Dada nir raina wayo na

Dada sai nik kirai Ahadun
Guda, wannan da as-Samadun
Da nim matsu ni nufai da gudun
Gama shi am maceci na

Da nat tasamma inda shike
Cikin huruminsa ni iske
Aminci nan gare shi shike
Dada nid debe tsoro na

Da dai nig gane Sarkina
Da ba a bida garai shi hana
Ga kofofinsa niz zauna
Dada ni buda baki na

Dana roka da ya bani
Dani dauko ga Qur'ani
Ashe ma anyi min izini
In tai in kara koke na

Da najji hakanga nish shirya
Bido Zababbiya ka jiya
Cikinta kana ganin hanya
Da zam bi ta zam mahorina

Taho sa hankali ka kula
Kabar gajiya, kabar shagala
Tutur! mu tsare yabon Allah
Cikin zarafin zamowa na

La'in mun zo ga Qur'ani
Bisa horonka don ka sani
Ina tsaya ran dare da wuni
Ina shukuri da Bege na

Tabara yabonka jalli na
Gareni abin tsimina na
Sahihin maganina na
Da shi nika warke rauni na

Da lotto duk yabonka ni kai
Dana matsu duk kiranka ni kai
Bida bisa agajinka ni kai
Ka warwatse aduwai na

Kana nan inda nis sanka
Tutur! Ka amsa sunanka
Mujibun kow kireka haka
Kana ji baka yin kwana

Da kyau nas soka nab bika
Da kowa baiyi ma shirka
Ilahul Arshi baicinka
Wane ka biyan bukatu na

Ina wani banda kai Rabbu
Da ba a bida shice babu
Ina wani mai kade aibu
Gareni shi karbi rokona

Ku kawo wanda kun ka sani
Da komi za ayi shi sani
Da an roke shi bashi hani
Fada mini shi, ka ban suna

Kace Allahu sarki na
Wani nai dug gazajje na
Abi nai duk kadan dai na
Ina shika jure roko na

Bida ga waninka mik kai ni
Dadai duk wanda yas sanni
Cikin ni'imarka yag ganni
Kana da kula da raino na

Ka cetan kar a kaushe ni
Ga duk hanyar da shaidani
Rajimi kar shi rudeni
Shi hau kan yan dibaru na

Ta'ala kai da ka hora
Mu zan koko mu zan ta bara
Gareka mu zam bidan Nasara
Dashi ni kayo umurni na

Ta'ala Jallah mai iko
Ina nan dai ina dako
Ina ta kiranka kullum ko
Ina kuma kara kwazo na

Da farin na kiraye ka
Da sauri nig ga jinkanka
Ina gode ma baiwarka
Dashi ni ka rera wake na

Ta'ala bani fasa bara
Tutur! Ni ke duk cikin zakara
Ginarka gareka ga sutura
Wadarka, ka kore bakakina

Bukatu na matso ni su kai
Dana matsu ko kiranka ni kai
Tutur! Sonka bani ni kai
Ina nika kama bakina

Bukatu gasu sun gilma
Ilahi gani na soma
Kiran nan wanda nif fara
Da farko nigga dace na

Da farin gafara zambu
Nike roko wurin Rabbu
Da aikina nayin aibu
Da son raina da wayo na

Ka hori ga zuciya ta tsaya
Bida ga waninka duk ta kiya
Balle inyo haraminya
Garai in banna baki na

Isheni ga duk abinda nik kai
Biya min duk bukin da ni kai
Gama kasan nufar da ni kai
Ya Rabbi ka amshi rokona

23 comments:

Anonymous said...

Babu shakka, Wazirin Gwandu ya taka babbar rawa, wajen tunatar da jama'a ingancin dogara ga Allah (SWT).
Allah ya gafarta masa.Amin.

Anonymous said...

Wazirin Gwandu mutum ne haziki, wanda ya taimaka wajen bunkasa harshen Hausa, da kuma ilmantar da mutane muhimmancin dogaro ga Allah(SWT).
Allah Ya jikansa. Amin.

Alhajin Tatta, Yar'Akija,Sokoto.

Anonymous said...

[url=http://firgonbares.net/][img]http://firgonbares.net/img-add/euro2.jpg[/img][/url]
[b]buy photoshop 7, [url=http://firgonbares.net/]osx address book into filemaker pro 9[/url]
[url=http://firgonbares.net/][/url] power policies windows xp registry adobe photoshop cs3 information
places to buy software [url=http://firgonbares.net/]buying student software[/url] buy igo software
[url=http://firgonbares.net/]free autocad blocks[/url] discount software for educators
[url=http://firgonbares.net/]discount software ms[/url] buy and sell software
educational software reading [url=http://firgonbares.net/]office 2003 vista[/b]

Anonymous said...

Wazirin Gwandu,ya bayarda gagarumar gudunmawa a fagen fadakar da jama'a muhimmancin tauhidi.
Allah ya saka masa da alheri. Amin.
Alhaji Ibrahim Umar Yaro Gandu,Sokoto.
Secretary, SAHIHIYA PUBLICATIONS COMPANY,SOKOTO STATE.

Anonymous said...

Assalamu Alaikum! Ina zamu samu wakokinshi don muyi downloading

Anonymous said...

Wassalam alaikum, zaka iya samun wakokin sa gidajen sadarwa misali kamar rima rediyo sokoto ko kuma ka binciki inda masu tura wakokin zamani suke domin a can ma zaka iya samu Allah shisa adace babu shakka wannan wakar tana tattare da cikakken tauhidi zuhudu

Unknown said...

A kara rubuta wasu....mungode

Unknown said...

A kara rubuta wasu....mungode

Unknown said...

Enter your comment... Wannan yabon yana nuna mana tsentsayar tauhindi da kadaita allah shi kadae...
Allah yagafar ta masa..
Soko data buhari sokoto tudun wada....

Unknown said...

Happy to hear good things about my granfather

Unknown said...


"
At the point when all activities and slimming down stage gets fizzled, Keto Primal works splendidly to give the coveted results by giving a thin and sharp body appearance since it is a characteristic craving boosting fat buster. The supplement additionally limits the nourishment desires or enthusiastic eating of people where they would encounter less appetite feel and that would offer them to stay in controlled calorie admission.

The supplement attempts to influence a person to go fit as a fiddle and carry on with a sound and a la mode way of life. The weight reduction process that begins after the admission of the pills go normally, and you may encounter the results inside 2-3 weeks of time. The expansion of every common concentrate here attempts to support the stomach related framework and furthermore clean the colon framework to stay free from hurtful poison squander. It supports the digestion level and gives a lift to vitality and stamina level where you would have the capacity to exercise more without getting worn out and stay dormant way of life. Visit for more informations:
Keto Primal
Health Care 350"

Unknown said...

"I like this post,And I guess that they having fun to read this post,they shall take a good site to make a information,thanks for sharing it to me.
Read more here:
kim kardashian sex tape
porn sex video hd
mia khalifa sex video
sunny leone sexy movie"

ABCD said...

Losing weight became easier since I started using Pro Keto X
that is fast acting appetite supperant and leads to burn stubborn
belly fat without causing any side effects to the health but it
is not designed to use for minors, thank you for this magical creation
Keto Pro X

Pankaj Kocchar said...

Why worry with the weight loss factors when there is one of the best weight loss supplement
available in the market that is named as teal farms keto and works to remove bad cholesterol
and boost the metabolic rate of the bodyto deliver controlled weight gain and burn unwanted
calories naturally http://www.nutratrials.com/teal-farms-keto-diet/

ToneSlim111 said...

Healrun is a health news blog we provide the latest news about health, Drugs and latest Diseases and conditions. We update our users with health tips and health products reviews. If you want to know any information about health or health product (Side Effects & Benefits) Feel Free To ask HealRun Support Team.

Retro Lean Garcinia said...

Supplements For Fitness make sure there are no known interactions between the medicines you are already taking and those you are taking without a prescription.Just remember that everything you buy and invest in your body should

fgtgtr said...

Pilpedia is supplying 100 percent original and accurate information at each moment of time around our site and merchandise, and the intent is to improve the usage of good and pure health supplement. For More Info please visit Pilpedia online store.

Sharon Wood said...

Avast Customer Support
Mcafee Customer Service
Norton Antivirus Phone Number

Dale Morris said...

Norton Customer Service Number
McAfee customer service phone number
Malwarebytes support
hp printer support windows 10
canon printer support usa

Erin Moses said...

canon support number
Avast Phone Number
Microsoft Edge Support
mozilla firefox support
apple contact number
norton support australia
hp printer support
brother support australia
Contact number for McAfee antivirusr
outlook contact number australia

Shark Tank Diet said...

It's not illegal. There's stunningly little likelihood for you to be blindsided by this. Have you ever bought a Fat Loss? I hadn't disputed that I could not have had more to mention as this touches on Fast Weight Loss. Keto Power Boost This means that that you'll have a larger flexibility along with your Fat Loss. This was a discount value. You may expect that the sunshine's on but no one's home.

http://www.sharktankdiets.com/keto-power-boost/

http://www.sharktankdiets.com/

Nutra Health Pro said...

As a depend of path, you in all likelihood can and could get a wellness that waste a taste for a wellness. i have attended several seminars pertaining to wellness.

What you really need is apparent proof.
https://www.nutrahealthpro.com

https://www.facebook.com/nutrahealthpro

https://twitter.com/nutrahealthpro

Anonymous said...

Do you have the complete audio? pls