An haifi Alhaji Mudi Spikin a ran 1 ga watan Oktoba 1930, a unguwar Darma da ke birnin Kano. Yayi karatun qur'ani a hannun Malam Umaru Badamagare. Bai taba zuwa makarantar boko ba, amma duk da haka, ya zauna jarrabawa GCE Ordinary level, ta hanyar yin rijista da wata kwaleji a Ingila, acikin 1960. Ya sami illimin zamani ne a hannun abokansa na gwagwarmayar siyasa irinsu; Malam Sa'adu Zungur, Malam Aminu Kano, da kuma Alhaji Yusuf Maitama Sule. Yana cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar kwato yancin talaka wato NEPU a 1950. Ya fara rubuta wakokinsa tun a 1948, ya fara da wakarsa ta "Rasha Abokan Tafiya", da kuma wani raddi da yayiwa malaminsa, wato malam Sa'adu Zungur maitaken "Arewa Jamhuriya Kawai".
A ya jama'a ina tashin
Ku dan ku rage yawan bacci
Ayau na zo gareku da sha
Wara don kara inganci
Mu wo himma mu tashi tsaye
Mu gyara kasa ta san yanci
Mu kawo shawara mai kyau
Mu tashi mu yaki jahilci
Rashin illimi ya sanya yau
Kasar nan ke yawan baci
Fa sai mun tsaya gyara
Na sosai babu jahilci
Sannan zamu san matsayi
Mu tsere wa wulakanci
Idan ba tattali a kasa
Hakika dole ta baci
Idan an zubda hakkin yan
Adam domin wulakanci
Idan masana kwarai an zub
Da su domin rashin yanci
Idan sharia ta zam ciniki
Ana nunnuna bambanci
Idan kuma masu aiki sun
Zamo duk babu inganci
Idan aiki ya zamto ba
Ayi, sai an ciwo hanci
Idan hairi a baki ake
Fada sharri cikin zuci
Idan da akwai yawan hassada
Da bata mutum da iskanci
Idan da akwai yawanta saki
Na aure don wulakanci
Idan ba tanadi wai duk
Wata sai anyi angwanci
Idan aure ya zam a kasa
Ana yi ne da jahilci
Idan kayan biki aka mai
Da su tamkar na dillanci
Idan ga jahilai a kasa
Na kin canji da shashanci
Idan da zama na banza, ba
Sana'a ai ta kakaci
A sa fatala gaban goshi
Da hula wai tsageranci
Ana ta musu ana karta
Ana zance na wawanci
Idan kuma ga yawan zargi
Na banza ga rashin yanci
Idan wani dan'uwa wai yayi
Samu ayi munafunci
Idan sharri ya zo a iza
Nufi dai ayi wulakanci
Idan da akwai yawan camfi
Da bori masu shashanci
Idan da akwai yawan tsegun
Guman banza na jahilci
Idan a kasa ya zam an go
Yi bayan masu lalaci
Idan mai gaskiya ya zamo
A kullum zai ga kaskanci
Idan gata ya sanya wadan
Su yin shirme da shashanci
Idan aka maida wadansu kamar
Ace bayi rashin yanci
Idan yan kasuwa suka zam
Sana'a aita hainici
Idan ga karuwai a kasa
A kullum ai ta fasicci
Idan da giya an ta
Ru kullm nuna iskanci
Idan ba tausayi a kasa
Mutane na ta makirci
Idan kuma har amana tai
Kadan sai nuna ha'inci
Idan har maluma suka bar
Sani i zuwa fagen baci
Idan bidia ta zam an gir
Gina kuma babu sassauci
Idan yaya suna sabon
Mahaifa har da kaskanci
Idan a kasa akwai wannan
Hakika dole ta baci
Fa sai in anyi aiki za
Hiri ba nuna lalaci
Sa'annan zamu san haske
Mu tserewa wulakanci
Abinda na farfadan nanYan
'Uwa da akwai muhimmanci
Fa duk gyaran wadannan na
Garemu cikin batun yanci
Mu daina abinda bashi da kyau
Mu daina biyewa jahilci.
3 comments:
thanks 4 creating dis blogger. in fact i very much enjoyed all poems posted so far. pls keep dis gud wk.
cud u pls post Aliyu Aqilu's Aikin hajji ya wuce wasa and wakar karuwa? I'll much appreciate if these two get posted.
malami
Good fill someone in on and this post helped me alot in my college assignement. Say thank you you for your information.
abdullahad usman manu darma anhaife a 1978 a unguwar darma gida mai lamba 132 na fara karatun firamare a 1985 makarantar masallachi special primary school dake shahuci na gama 1991 na shiga secondry a 1991 zuwa 1997 goverment secondry gwale nayi diploma a f.c.e a halin a yanzu ina aiki kano state water board.
Post a Comment