Tuesday, March 27, 2007

Wakar Zambon Kazama; Aliyu Namangi Zaria

Ya Allahu Rabbana taimakemu
Mu gargadi yan'uwa ga auren kazama

Auren tsohuwa hasara ga yaro
Gwammaci tsohuwa ga auren kazama

In baka san tane ba kau tambaye ni
In Allah ya yarda kasan kazama

Mummunan halin kazama na fari
Bata fece majina sai da dama

Mai son cin tuwonta sai yaci gashi
Susan hagu na tofi da dama

Hanci majina, idanunta kwantsa
Dattsa ya dadawa bakinta girma

Sai kaga tai gajal da suma da dauda
Ga bauli a kwance, tashinta fama

Bamai son kitso ba, ta kasa aski
Taba ya dafe hakoran kazama

Gude ba kokari ba ga kasa girki
Ga hadama a zuci koshinki fama

Ran girki ba a koshi da jibi
Shi naman miji ki cinye a tsama

In taga ka fito kamar zaka zaure
Sai sababi ya tashi don bata girma

Ka ji "Bar neman fita ina tsame nama
Yau dai kai rabon a zage ka kai ma"

Tunda ka sai kitse ya narke a girki
In aka zo rabo, rabawansa fama.

Wanda ka bashi kankane sai ya raina
Kowa so yake ya karba da dama

Ran nan ma ka sai kashi, na ki zagi
Gun kwarin gidanka mai yada girma

In ta ce dani kazama in rama
Wanda ya san Kumatu yasan kazama

In tace ina da ci ne in rama
"Domin ga Tasallah koshinta fama"

Kwana goma jere, haifanta goma
Ba taran miji ga haifan kazama

Ita ko Bante ta ketara sai ta haifu
In ka san kudi su kare a suna

Ya Allah dadawa matanmu tsabta
Kada Allah ka bamu mata kazama

Tunda mijin kazamiya zai ji kunya
Can Aljanna babu mata kazama.

9 comments:

Abdalla said...

Excellent effort! Allah Ya saka da alhairi

Abdulaziz Ahmad Abdulaziz Fagge said...

Sallam,
Gaskiya Mal. Fatuhu na ji dad'in ganin wannan wak'a, domin ni a da ban san cewa Mal. Aliyu Namangi bane yayi wannan wak'a, na dai san ta a bakin al'majirai. Allah ya saka.

Anonymous said...

gaskiya wannan namijin qoqarinyayi, don zai taimakawa dalibai masu nazarin harshen Hausa ako ina afadin duniya. DA ISHAMAK AL-KANAWI MADOBI

Phoebe Talata said...

Dr. Akwai yanda zamu sami fasarar ta turanci? Na taba ganinta. watau "song of the slattern, by Aliyu Namangi". Na gode

Anonymous said...

flbcv [url=http://www.beatsbydresolosales.com]cheap beats by dre[/url] lufzxjpo http://www.beatsbydresolosales.commeonjdthz izvrir [url=http://www.beatsbydrdrestudiosales.com]cheap beats by dre[/url] ltoioxlqhttp://www.beatsbydrdrestudiosales.com qfypfsroj zttwfx [url=http://www.drdrebeatsheadphonesonline.com]cheap beats by dre[/url] hnywvdim http://www.drdrebeatsheadphonesonline.com wlfzgpreg uryinv [url=http://www.drdrebeatsheadphonesforcheapsale.com]dr dre beats[/url] ijjgykva http://www.drdrebeatsheadphonesforcheapsale.com tavlhhvlf maoqex [url=http://www.drdrebeatsheadphones-cheap.com]beats by dre[/url] kcvcuoky http://www.drdrebeatsheadphones-cheap.com plggervxp txkoid [url=http://www.drdrebeatsproheadphonessale.com]cheap beats by dre[/url] oziwycwh http://www.drdrebeatsproheadphonessale.com yywfpqrco a

Rachel said...

Awesome!

Cherry Adom said...


Tory Burch handbags are advised by way of a acclaimed artist termed Tory.When we are talking about the trends, we consistently apperceive that it comes and goes with the time. However, archetypal artist Chanel replica handbags will be the admirable appurtenances that can abide the analysis of the time. Thus, a chichi beautiful bag will accumulate a continued abiding attraction. For instance, the beforehand appearance on "the bigger, the better" still is the appealing hot a part of women who buy aerial handbags. He uses their abundant aptitude of adroitness and way by creating and aswell designing such claws for women for the women of about every age and styles. These cover accessible in a amount of assorted styles, shapes, colors and materials. The accoutrements are amid in abstracts such as Hermes Replica Handbags leather, bolt and textile, blubbery wool, jeans and others, that could be in fashion.

Nasir Umar said...

Don Allah kaci gaba da wannan kokarin naturo rubutattun wakokin hausa domin amfsninsu a addinince ba wai a al'adance ba kawai

Nasir Umar said...

Don Allah kaci gaba da wannan kokarin naturo rubutattun wakokin hausa domin amfsninsu a addinince ba wai a al'adance ba kawai