Sunday, May 13, 2007

Wakar Gyaran Kano; Daga Dr Aliyu Aqilu 1975

Wannan waka an rubuta ta ne a 1975, ya kuma yi tane domin wani hangen nesa da yaga Kantomman Kano na weannan lokaci yayi, wato Dr Uba Adamu. A hirar da nayi da Dr Uba Adamu, a gidansa cikin watan April, ya bayyana mini cewa " Cikin 1974 ne suka yi tunanin, kawo gyara a tsarin zamantakewar birnin Kano. A saboda haka suka kawo wani tsari, wanda hakan ya haifar da gina manyan tituna a Birnin Kano, da yin Kwalbatoci, da kuma wajejen zuba shara. A wannan lokacin ne akayi Manyan titunan da ake amfani dasu har yanzu a birnin Kano. Aka kuma yi musu Kwalbatoci a gefunansu, da kuma wajejen zuba shara". A saboda jin dadin wannan aiki ne, ya sanya Dr Aliyu Aqilu ya yi wannan waka. Ga dai wakar


Zan je ziyarar shugaba
Dattijo Kantoma Uba.

Bazan shiru na kawai ta ba
In ba da na ce Rabbu ba.

Sarki guda daya wahidi
Bazan takaita kiransa ba.

Bayan fadar Allah da gai da
Manzo Muhammadu Mujtaba.

Me zai biyo bayan su ne
Na abin nufi da yake gaba.

Haka ne akwai wani dan batu
Da ba zan ki tunkarar sa ba.

Ga dai bayani dan kadan
A takaice ba dungunsa ba.

Niyar ziyara ce dani
Zancenta yau zan bayyana.

Mai tambaya ya so yaji
Domin ya amfana gaba.

Manufar ziyarar wacce nai
Maganarta tun farko gaba.

Ya zuwa ina wai zani kai
Mai tambaya bai aibu ba.

Zan bayyana masa ne ya ji
Bazan yi kwauro gun sa ba.

Zan dau ziyara ne ni kai
Ta kano gari ba kauye ba.

Wajen masoyina abin
kamna sahihin Shugaba.

Shine Muhammadu Adamu
Kantoma mai lakabi Uba.

Dattijo din nan adali
Mai tausayin jama'a Uba.

Bangon tama ki faduwa
Sha kabra garnakaki Uba.

Matsayinka din nan kai can
Canta da shi malam Uba.

Illimi zalaka ke gare
ka da kwarjini na kwarai Uba.

Ga hattara ga hankali
Kantoma ga hangen gaba.

Illimin makamar zamani
Da sanin sharia tun gaba.

Ka san su ka kuma dandake
Ba yau kawai ka tsire suba.

Birnin Kano da wajenta duk
Ta samu babban cigaba.

A wajen nizafa in ka du
Ba kauyuka ba a bar suba.

Balle cikin birnin fa
Ba wai bane ba inke ba.

Kwatami cakal yau babu shi
Shara butsa bamu ganta ba.

Sarari a hanya ya dadu
Albarkacin himmar Uba.

Duk tarkace an kauda su
Daga ko ina ba a bar shi ba.

Sababi da wane mun ka sami
wannan gimgimemen cigaba.

Mun samu kakkaifan mutum
Mai kokari ba kasa ba.

Gwarzon maza namijin tsaye
Inuwa ba a bisne ki ba.

Kantoma Muhammadu Adamu
Dattijo mai lakabi Uba.

Bompai da Rimin Dada sun
Maka godiya malam Uba.

Sabon gari da Tudun wada
Sun gode mai daraja Uba.

Tarauni su da Giginyu sun
Yi yabo ga mai daraja Uba.

Gandu Sharada da Dorayi
Da Salanta., Calawa gaba.

Jama’ar da ke Fanshekara
Duk sun yi san barka Uba.

Waika da Jajira, Gobira
Wa, sun yi godiya malam Uba.

Kurna, Fagged da Gwagwarwa
sun maka godiya malam Uba.

Na sauka Fanisau mutan
Gama sun game da yabon Uba.

Ungogo, Kunya suna fadar
Madalla-madalla Uba.

Wannan Sadauki adali
Dattijo bai yashe mu ba.

Kub! Dai yawa kuwa lara bugu
Daya ta mace bata tashi ba.

Ya watsa rundunar
Sauro a yau bamu ji shi ba.

Bana nufin guda da dai
Ban daura niyyar yinta ba.

Amma dalili ya saka, ni
Na yi ta ban shiryeta ba.

Domin saboda farin ciki
Dadin zamanmu da kai Uba.

Zai sa ni Kwalla yar kadan
Watakil bakwa zarge niba.

Sirri na kokon zuciya
Fuska bata rasa jin sa ba.

Yururui! A yau na randama
Kodai da ban sabeta.

Amma akwai Magana daban
Da ba zan iya ban yi taba.

Domin ta nai mini kaikayi
Na zo ka sosa wajen Uba.

Najasa da ke yi barkatai
Haka nan butsa! An zuzzuba.

Ba kariya ko yar kadan
Daga baya har ya zuwa gaba.

Ka ga sangamemen saurayi
Bama su yara kanana ba.

Ya yaye al’aura a fi
Li bada jin kunyarsa ba.

Wannan abin bisa gaskiya
Ban samu jin dadinsa ba.

Domin akwai ill agama
Baki ba za su yabe mu ba

Harma sukan zarge mu ne
Ba wai bane, ba inke ba.

Ni naji sanda suke fade
Kuma na gwada na jarraba.

Kasan ni kan fita ne waje
Zancenga ban kage shi ba.

Wannan ta ja mini damuwa
Na tafo ka maganta Uba.

Ai ya kamata ka tsawata
Kuma kar a kara nan gaba.

Nasan ka baka rurumi
Kuma baka lalaci Uba.

Me maida kai kake mai kula
Ga abinda duk ka saka gaba.

Tsuguna da tashi ba’a yin ta
A ofishin malam Uba.

Baka shiri da munafuki
Cece-kuce baka ji shi ba.

Kowa shigo da maganganu
Mara sa shiri a gaban Uba.

Kudarsa zai kuwa dandana
Dadin karon bai ji shi ba.

Su kwaramniya da rigingimu
Da hayaniya an zuzzuba.

Duk dai a karata dole ne
Ayi gaskiya a gaban Uba.

Domin kurum shi kayi shi ji
Kowa abinda ya rattaba.

Suna daban yau zan fada
A gareka yau malam Uba.

Kere kana fasa kan maki
Bin gaskiya baka san shi ba.

In kun tuna nace da ku
Guda bana rika yin ta ba.

Amma fa har haka dan ku ji
Dadi bazai inganta ba.

In banda an ware shi an
Yafa shi an more shi ba.

Kash! Nan wajen zan dakata
In sa alama sai gaba.

Ni ne Aqilu Aliyu na
Gaisheka mai daraja Uba.

Kantoma huta lafiya
Sai lokaci wani nan gaba.

In Rabbana ya kaddara
Mana saduwa ban mata ba.

Bana yawaita maganganu
Sai addu’a zan kattaba.

Ya Rabbi ya Sarki Gwani
Allah ka ja zamanin Uba.

Amin saboda abin biya
Da yabo Muhammadu Mujtaba.

Tamat bi AunilLahi mun
Bidi taimako nasa tun gaba.>

4 comments:

Anonymous said...

An Original recording of a Lady GaGa Hit was Unsealed this morning with no traces of where it came from.
Some say that it was leaked from GaGa's Record Label's headquarters.

More info at http://ladygagaunreleased.blogspot.com

Free Download of the single at http://tinyurl.com/gagaunreleased

Anonymous said...

Hi Fatuhu
I was learning some language today...can you please help by telling me the meaning of the following words which I found on your blog:
san
shan
dada ga

thank you

Anonymous said...

Allah ya jikan fasihi Alh.Akilu Aliyu.
How i wish i could get his audio work.
God bless you,Mallam Fatuhu for keeping alive our heritage.

My name is Aliyu J,Kiru

Mohammmed Medhat said...

شركة النجوم مكافحة حشرات رش مبيدات نقل اثاث تسليك مجاري تنظيفشركة مكافحة الفئران بجدة


شركة رش مبيدات بجدة

شركة مكافحة حشرات بالطائف