Saturday, May 12, 2007

Wakar da ake Sanin Halin mata da ita; Muhammad Dangani Katsina

Wannan waka dai ta shahara a kafafen watsa labarai na Kano da Kaduna,domin akan watsa ta a shirye-shirye da dama.Ga dai wakar.

Bismillahir Rahmanir Rahim
Wasallallahu ala Nabiyul Karim

To bismiLlah Allah Sarki
Mai abu mai komai mai kyauta

Bani zalaka, bani fasaha
Inyi bayani na, a fahimta

Zanyi bayani halin mata
Zani rubuta, don a karanta

Kasan mata sun kasu ukku
Zo kusa in na fada ka rubuta

Akwai mata mai tsoron Allah
Bata nufin kowa da mugunta

Akwai wata ga barna ga gyara
Gata da saukin kai ga cuta

Sai ta ukunsu gadangama kenan
Bata nufin gyara sai cuta

Bata nufin hairi ga mijinta
Baga kiyoshi,ba ga makwabta

Bata nufin gyara sai barna
Sai duk safe ta cuci mijinta

Ya tafi office kokuma kanti
Bata kara zama dakinta

In mai noma ne ko zage
Ya tafi gona, zaure za ta

Tana nema taga masu wucewa
Wai ita dai suga kyan fuskarta

In taga sunki shiga harkarta
Sai kaji tace zata makwabta

Kaji irin halayen mata
Munana,manyan, makwadaita

In mace bata da kunya barta
Kama da miya,in ba gishirinta

In mace bata raga maka barta
Daina nufinta kabar sha'awarta

In mace ta zama bata ragama
Ko ka sota, kana kuma kinta

In mace, shashanci ya gameta
Ba mai kara ganin kirkinta

Bata nufin Allah da Ma'aiki
Sai bidi'a ita ke ka gunta

Taji ana Biko tai mika
Sai kaji tace Biko zata

Ba dangin iya babu na Baba
Ko kace ta bari, can zata

Wannan mace,ba mace ce ba
Dai na nufinta kabar sha'awarta

Natsuwa itace mace,ko yar wace
In kaga ba natsuwa,ka bajeta

Kasan mata sun iya karya
Sun iya yadda suke shirgata

Ba duk mace ke son addini ba
Nufinsu a basu kudi, su bukata

Matar da ta zam bata san Allah ba
Ba ta kara zama dakinta

Sai ta fito a tashar Takatale
Sai tai batsa gaban kanwarta

In kace mata, wance ki lura
Baka hana ni bugun cinyata

Babu ruwanta da kunya faufau
Ga Ashar, ko ciwake yana kunyarta

Sanarwata itace ga mazaje
Kar a yawaita kwadai, a takaita

Aure ba abu ne ba na wasa
Bar neman kyau, nemi nagarta

Ni nasan mace, komi kyaunta
Indai babu hali da nagarta

Kana sha'awarta, kana kuma sonta
Badan Allah ba kana kyale ta

Don haka, tun farko ka tsaya tsaf!
Kai nazari da irin halinta

In mace ta zama, shagiri girbau
Ko ka aureta, baka iyata.

Kun ji mazaje, kar ku kiya man
Ku lura da duk farkon maganata

Akwai mata na nan su shidda
Zo kusa inna fada ka jimilta

Akwai dibgau! Mai dibge mijinta
Ba ta jira ga fada shi taya ta

Danbago, mai zurfin tumbi
Ba ta takowa sai ta cikinta

Sai shirwa ita dai tayi fige
Kan ta shigo daki sai ta sata

Ratata, sarkin magana ce
Tun daga nesa, kana jin kanta

In maganar mace tayi yawa, kaji
Tun daga nesa, kana jin kanta

Wannan mata, tayi hasara
Sai a nada mata sarki wauta

Sai Malali, ita dai tayi kwance
Ta ki ta tashi, ta nemi na kanta

Ba ta kadi, kuma bata sanaá
Sai na mijinta, ya bata, ta sata

Sai ta cikon shida, mai mulkin kai
Ba mai sa ta, bare shi hana ta

Aure ne, ni nis sa kaina
In ka matsa mani, in tafiyata

To shida ta cika ban kara ba
Akwai saura, amma na takaita

Akwai saura, amma na kaita
Ka shaida akwai mata masu kazanta

In mace ta zam bata da tsafta
wannan kam, ta cuci mijinta

Yin tsafta, ta jiki da tufafi
Shine ke hana yadon cuta

Wadda ta zam, bata wanke tufa ba
Shike shaida, anga kazanta

Zani tuna muku in kun manta
Kashedi, da mata masu kazanta

Sun gaza wanke tufa da tukwane
Sun ki kula da abinci su kyauta

Ta gaza share cikin dakinta
Balle na mijinta, bale fuskatta

Kun ji isharata ku kiyaye
Ku lura da duk farkon maganata

Akwai barna ga mazaje
Zamu fada musu, don su raga ta

Wadansu maza dauka da ajewa
Sun dauko mace, sai su aje ta

Ba laifin tsaye, babu na zaune
Sai kaga basu zuwa dakinta

Ran aikinta ba zai fara'a ba
Ko magana tai, bashi kulawa

Duk namijin da ya dau kwanan wata
In ya hana mata, don bai son ta

Yaki bsatun Allah da maáiki
ya kashe kansa, saboda mugunta

Mata gunku amanar Allah ce
Don Allah maza ku rike ta

In mace tai maka laifi daure
Sai ka tuna, ai kai ka aje ta

Su mata halinsu mugunta
Sai dai-dai ke, basu da keta

Macce, mijinta ko sarki ne
bata yaba masa, sai in bata

Macce mijinta ko malam ne
Bata yabonsa tace da nagarta

Tana iya cewa miji mataulaci
Koda yayi kudin Dantata

Su ka bugu su riga kai kara
Ba ai magana ba su je su tsirata

In mace ta shirya maka karya
Ko boka kam, bashi iyata

Macce tana shiryawa mijinta
Karya, don ya bari tayi cuta

Tâce mashi zata gidan kanwarta
Ko kuma zata ta gaida uwaye

Ta fita, ta samu ta sulale
Ta shiga yawo santa-santa

Ba ta gidan iya, bata na Baba
Kaji nufinta ta sheke ayarta

Don haka mata, ba'a iya musu
In kaji sun magana ka aje ta

Kowace mata na da halinta
Wadansu da kyau, wasu ko da mugunta

Wata in suka fara fada da mijinta
Sai ta rike shi, tace ya kasheta

In kuma yaki ta kama tufarsa
Ace ta sake shi, tace ya kasheta

Ko kuma yanzu ka bani takarda
In kuma ka ban in ketata

In kuma kace anshi takardar
Sai kaji tace, bani riketa

Ita dai sababi ta ka so ta aza mai
Indai yace bashi sakinta

In ka hada ta da Allah sannan
Tafi matsa maka don tsiwarta

Kai kuma gaka kana jin kunya
Ga shari'a ka zage ka kasheta

Don haka sai kowa yayi sannu
Ya nemi hali mai kyau da nagarta

Ba'a sayan mota don kyanta
Sai kaya, da gudu, da nagarta

To haka ne mace, komi kyaunta.
Indai babu hali da nagarta

Kamar mota take komi kyaunta
Indai ba tafiya, bari sonta

Kyan ladabin mace tai wa mijinta
In taki ya mishi, ta kashe kanta

Kui ladabi mata ku kiyaye
aure ba'a gama shi da bauta

In mace tai ladabi ta kiyaye
Allah sarki, shi ka biyanta

Ku mata ku jiya, ku kiyaye
In kuma kun ki, kui mahukunta

Ran mutuwa, da gamo, da kasawa
Sai a tuna maka, in ka mance

In mace tabi mijinta da gaske
Tayi hakuri ta tsaya dakinta

Bata ganin wani banda mijinta
Allah zai mata, babbar kyauta

Miji babban abune bi mjinki
Dai na ganin waccan da mijinta

Bishi, ki so shi, ki bar raina shi
Ko shine sarkin matalauta

Don ki sani Allah ya aza mai
Shi aza masi, shi zai kyauta

Shi abu duk aikin Allah ne
Allah shike bada wadata

Ya kasa bayi fanni-fanni
Shi yai ma'azurta, yai matalauta

In niyyarki gudun matalauta
Sai ya so sannan ki wadata

Shi Allah ba ai masa wayo
Yanda yaso, haka za shi hukunta

Ki hakuri ki tsaya ga mijinki
In ya wadatu, sai ki wadata

Ya Allahu muna rokonka,
ya Allah ka bamu wadata

Ka bamu abinci ckin suturarmú
Allah kadda ka nufe mu da sata

Duk makiyanmu aza mu akansu
Duk sharrin da su kai da mugunta

Ka daukaka addini bisa komai
Ya Allahu bidia ka kashe ta

Kai tsira ga Muhammadu Ahmadu
Don dakin makka, don siffatai

Sahabi nabiyu, da ahlil baiti
Ahlil abaí kaza makusanta

7 comments:

Anonymous said...
This comment has been removed by a blog administrator.
viagra online said...

the blog is very interesting, very professional and very well written, thanks!

Anonymous said...

Sebagai Newbie, saya selalu mencari online untuk artikel yang bisa membantu saya. Terima kasih Wow! Terima kasih! Saya selalu ingin menulis dalam sesuatu situs saya seperti itu. Dapatkah saya mengambil bagian dari posting Anda ke blog saya?.

Anonymous said...

Total Control sepotong Marketing Review-Besar detail yang Anda telah diterima? Di artikel situs. Berharap aku bisa mendapatkan lebih banyak hal di situs web Anda sendiri. Aku akan tiba lagi..

Unknown said...

Gaskiya wannan waka tayi ko zan sami wadda aka rera a faifai?

kassimdandago said...

Za a samu mp3 din wannan wakar kuwa?

Anonymous said...

Don Allah a ina zan samu audio