Tuesday, April 17, 2007

TABARKOKO; Daga Sarkin Zazzau Aliyu Dansidi

Wannan dai itace wakar Tabarkoko, wadda sarkin Zazzau Aliyu Dansidi ya wallafa. Wakar dai gugar zana ce, ko kuma ince shagube da bai nuna wanda yake yiwa ba. Amma ana zaton ko yayi tane domin yiwa fadawansa shagube, game da yadda suke tafiyar da rayuwarsu.

Aboka zo nan mu bata
ka dubi dan dai ga wata
wada daban da batta
Haske na rana da wata
Ba zasu zam daidai ba

He dubi dai tsettsewa
Ya samu kifi a wuya
shina zaton babu kaya
Inta kafe mai ga wuya
ba zasu debe mai ba


He dubi dai irame
Can tai gida a rame
Can dauri kau ta rame
kyaushe mijin Irame
gallonsu ba zaki ba

Abin ga dai gama na
kare shi tono magana
zai iske kura a hana
ba dun akwai wata magana
da bai fito rannan ba

Ai ga fage ga doki
Noman fako ba taki
ai maganan ta sake
da dan kare da na doki
ba zasu zam daidai ba

Mu namu ga ta da taki
babu biri ba zaki
barde dubu mai doki
da zamanin kai taki
da bamu samu nai ba

Saura garin ya waye
duk kokuwan tai kaye
Damu ga yan tawaye
da masu da da maye
zamansu bai zam dai ba

Karya take zabira
bata zama gurara
Iska daban da sarara
matar maza da bera
kudinsu bai zam dai ba

Na ganshi duk ya kwabe
Yayi tabo ya tabe
yayi bago ya rabe
Neman jini ga babe
Ba za'a samu nai ba

Zo ka taba dai ka jiya
Yau muke koko jiya?
Haure ka ciwo ijiya
in yayi sai ayi jinya
ba za'a debewa ba

Ko ka iso, ko ka tsaya
Taunan aya ko ka iya?
Amale cimansa kaya
Jaki, da sa, ko akuya
Ba zasu taunawa ba

Kaya ga Rakumi shike
Takarkari sai taiki
Saimo akanwa taki
Tsaiko akanwa daki
bukka ba ta dauka ba.

Makaryata, mahassada
basu iya komi da guda
na yanzu ba ko da na da
tara su dai duk ka gwada
ba su zamo daidai ba

Babba da jaka ya zaka
Yana bidan kifi tsaka
gulbin da dorina tsaka
Gefen kadanni ya saka
kafansa ba zai kai ba

Yada guda ka dau guda
Duk ka fasa su ba guda
hanya mararraba guda
gaba-gaba akan guda
cikinsu bai ba daya ba

Ga kutu ga Tabarkoko
Ga dole-dole tai hako
ni naga tana ga fako
kai mai bago shiga sako
Wurin ba'a zo mai ba

Kwaddo ina kadangare
Naji kafarsa ta kare
ya bar diyanshi gangare
in yayi nan sai a tare
ni ban gano zai kai ba

Ko kaga mai digirgire
wuya awa gadar zare
Takuna zance hantsare
da zamanin bakin zare
da basu sa riga ba

Ga tsada mai dan tashi
kullum ta dau albashi
ba ta ci bata hana bashi
ran da safiya tai fashi
ba za'a koka mai ba

Ga wani tantalwashi
na biyunsu mai kan bashi
na ukkunsu bashi da nashi
Da dai ana tuna bashi
da basu sa riga ba

Nazundu mai zaka fada
kullum ka gana da rada
roko awa dan makada
a baka bashi a dada
ba zashi fasawa ba

Ga wani wai shi ya iya
yaje ya jawo igiya
ta nannade mai a wuya
yana kira da waiwaya
ba za'a debe mai ba

Shin me ya samu shamuwa
na ga tana ta dimuwa
naga ruwan da kainuwa
ba dun kasan da kaguwa
da bata sauka anan ba

Da kunkuru da bushiyta
halinsu dai noke wuya
ga zamani na waiwaya
da zamanin mazan jiya
ni naga da basu kai ba

Debi yawa, sam ma kadan
yanzu yawa ta zam kadan
a hankali kadan-kadan
Gidan yawa kan yi kadan
Abinga ba banza ba

Nai muku waka ta batu
ku zo ku nemi yan batu
awa su lugegen batu
tara fasihai na batu
ba zasu ganewa ba

Mai wagga waka ta batu
Ali Amiru wan Shatu
Shine abokin Warqatu
Dadai da sirri na batu
Da bashi boyewa ba

Allahu shi yai mu duka
Baki fari yai su duka
Shudi da Korensu duka
Da Ja da Rawaya duka
Shi dai kayi ba wani ba

Zama fa shi dai ya iya
Shi yo mutum shi tafiya
Wadansu ko shi yi su tsaya
Shi yai itace da kaya
Nufinsa ne ba wani ba

Shi yai dawa da karkara
Shi yai dawa da karkara
Shi yai kwai, yai zakara
Yai zabuwa, yai fakara
Shi ad damu ba wani ba

Bautanmu dai hasana'u
Zam haufu, duk dada rija'u
Ku lura ko asma'u
Nisa'u masu gina'u
Sha'aninsu ba karko ba

Asma'u an sanki da dai
Halinki ki ne ko can dadai
Shirinki kullum na kwadai
Maso biyu,bashi da dai
Batun ga ba karyaba

Ywaita rokon Jalla
Ka wakkale ga Allah
Ka zam kula da Salla
A baka ni'ima walla
Anan da can ba waiba

Muyi zikiri da salati
Mu karkare afati
Gobe mu san najjati
Ga shugaban hajati
Muhammadu bawani ba










6 comments:

Unknown said...

Assalamu alaikum,
da fatan kuna lafiya yaya akaji da aiki?To ni dai mai shaawar shiga wannan shafi ne na hausa movies,to amma an gani na ya kamata wanna shafi ya zama ana rubuta shi da hashen hausa.
Da lilina kuwa shine,tunda wannan shafi sunansa hausa movies.com to ya kamata arinka wallafata da hausa,sabo da alal misali anan in da nake a china akwai sinawa da yawa da suke koyon harse hausa a Jamioi daban dabam a nan kasar suna yawan yi mini tambaya,akan wai mai zai hana wannan shafi ba zai rinka wallafa labarun finafinan hausa cikin harshen hausa ba?sabo da cigaban harshe hausa a Duniya?
To ina fata Malam Fatuhu zai duba wanna shawarar tawa da idon basira.
Allah kuma ya kara taimakon ku akan wanna kokari da kuke yi da kuma kara daukaka wa harshen Hausa a duniya baki daya.
Daga LUBABATU BS ILELAH BEIJING CHINA.

Unknown said...

salamu alaikum,
Allah ya bada saa ya kuma kara karfafa guyiwa na karfafa harshen hausa. babban abin da ya sani rubuta wakokin hausa shine nishadi da nakanyi kokuwa bacin rai in ya same ni wanda hakan yasa na rubuta da yawa daga cikin wakokina kamar Gugar Zana Da Muriki Addini, da kuma matar dujal. to amma daga baya dana je khartoum naga yanda abubauwa suke musamman abin da ya shafi yarurrukan afirka sai na samu kwarin gwiwa fiye da baya na rubuta wakar mukaranci kwampita da ta'aziya sheik Abulfathi. don haka zan iya bada wasu wakokin don a taimaka wajen cigaban hausa da kuma yiwa samari kaimi wajen rubutun kamar yadda kakana Aliyu Dan sidi sarkin zazzau yayi. Allah yasa mu dace. zaka iya samuna ta email: ajidadi2@yahoo.com

Anonymous said...

very useful read. I would love to follow you on twitter.

Anonymous said...

Hi just wanted to give you a quick heads up and let you
know a few of the pictures aren't loading properly. I'm not sure why but I think its a linking issue.
I've tried it in two different web browsers and both show the same outcome.

My page: appliance repair tampa cost

Anonymous said...

I have read so many content on the topic of the
blogger lovers however this paragraph is really
a nice piece of writing, keep it up.

Review my blog - appliance repair Brandon

AHmeT said...

Enter your comment...