Barka da zuwa Turakar Sha'irai (Hausa Poets Blogspot). An bude wannan Turakar ranar 23 ga Maris 2007 domin yad'a rubutattun wak'ok'in mawak'an Hausa (amma Sha'iran Najeriya, domin ba mu da masaniya game da sha'iran Jamhuriyar Nijar). Muna bukatar ta'aliki da gyara a kan abubuwan da aka gani a wannan Turakar. Allah Ya ba mu sa'a, Amin.
Saturday, December 8, 2012
wakar Begen Muhammadu Daga Malam Nasiru Kabara
wannan waka ce da marigayi Malam Nasiru Kabara ya rubutu, domin nuna tsantsar kaunarsa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wassallam.
Wakar Begen Muhammad ta Malam Nasiru Kabara
Bismillahir Rahmanir al Rahim
Wa sallalLahu ala nabiyul karim
1. Begen Muhammadu ya cika mani zuciya
acikinta ba sauran muhalli ko daya.
2. Wallahi garwashin bidar sado da shi
ya kona sassan zuciya wayyoniya
3. Naso ka Daha kamar ido ga makauniya
naso inje ni gareka koda sau daya
4. Naso ziyara gani bani da fiffike
kaka nake na gano masoyin zuciya
5. Na so ka son mai wabiya da ta so diya
ko ko maridhi yadda yaso lafiya.
6. Ko san abincin nan ga wanda ya yunwata
ko ko ruwa ga maji kishi zai sha wuya.
7. Mukhtari ka tafi ban gane ka a duniya
kona rabauta inga ko gun kwanciya
8. Acikin mafarki in na samu sai ince
“Allahu Akbar uh uhum wayyo niyya”
9. Begenka ya konan kasha har jijiya
Naman jikina ya zangwanye bai daya
10. Ya kona hanta har da hanjaijai duka
Ya bar hawayen zuciya da idaniya
11. Kaunarka ta kone bukatar zuciya
Duk babu sauran ma bukatar duniya
12. Inma akwai sauran bukatar zuciya
sai ko ganinka da yamma ko ko safiya
13. Ta yada zancen duniya tatsuniya
ta dauki amri wanda ya zam gaskiya.
15. Ta yada zancen zo mu ji ta dake fadi
ta kalmashe gizo ta hana masa kokiya
16. Duk zuciyar da ta so ka Daha da gaskiya
wallahi ta arzurta ba sauran tsiya
17. Tai sutura, ta tufata aluni bam-da-bam
labudda tai shaani irin na hawainiya
18. Wata safiya yayi murmushi wata safiya
Riga fara, wata ran ya sanyo shudiya.
19. Wata ran da alkyabba fara, wata ran kuwa
ya fashe da kuka nai kamar dan saniya .
20. Kaka ni kai da gani cikin nan duniya
wa zani kara gunsa ni wayyo niya
21. Ko nayi kara babu mai ji ko ya zam
kukan amale nake, ace ko jiniya
22. Mukhtaru ka faku ga gani nasa yai wuya
balle ince masa Daha ni na sha wuya
23. Shine abin kara gareshi gani nasa
ya zam kamar koyin farar hankakiya
24. Dan san ganinsa yana da yar farkar wuya
na dauki jure so ina ta dawainiya
25. In babu wanda nake da shi zai taimaka
na sauke kayan zo taya min dauriya
26. Ni dai ganin Makka a bukatar zuciya
inje ni can in samu saukin zuciya
27. Inje mahaifatai in san guri inje
insha ruwan zamzam inai wata gewaya
28. Inje Safa, inje ni Marwa in dawaya
inje musallai, in ziyarci mazan jiya
29. Sannan in dawo in dawafin salama
bayan makaman nan da Daha ya tsaitsaya
30. In wo hajjina kamila in masgaya
ni dai nufina gun mazajan gaskiya
31. Koda ina yan rarrafe in ja jiki
inje Madina garin Habibi Anbiya
32. Inje ni raudhar nan ta Daha in sunkuya
in gaisuwa, in dada da safe in dawaya
33. Ya Rabbi domin Anbiya’I da Auliya
Domin sahabban wanda ya cika duniya
34. Ka bani iko nai ziyarar Anbiya’a
dan Kudubu, dan Gausu, domin anbiya
35. A Ka saukake hanyar zuwanmu Idaibatu
Dan Mujtabai, dan Ni’ima domin Ma’iya
36.Kai agajinka A Rabbu dubi idaniya
Domin Tijjani al Khudubu mai Tijjaniya
37. Dan gimbiya tasa na kira ka A Rabbana
Ka jikan masoyan Daha, rana da safiya
38. Ganar dani Mukhtari Daha Alaniya
Domin ya kore min shuunin Duniya
39. Dauke hijabi Rabbana in gane shi fai
nan duniya ya rabbi ko a manamiya
40. Rahmarka ta gama kowanne balle niya
da na dauka karata ilaika Ilahiya
41. Ya Rabbi nai kara gareka fa kai daya
bayanka waye zaya amsa du’a’I’ya.
42. Ka yi wo salati ga Daha kai Taslimiya
a gareshi ya Rabbil wara, ya Bariya
43. Duk sanda mai bege yace ‘kul’ safiya
sallu ala Mukhtaru koda sau daya
44. Aufan zuwa Tashdiri fi takmilihi
Begen Muhammadu ya cika min zuciya
Subscribe to:
Posts (Atom)